BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

murmushi haydar yayi yace baby da ace da yadda zanyi da na maido cikin jikina nima banason wahalar da kike sha,

Sapna murmushi tayi tace nasan haka my hubby saisa nake k’ara sonka acikin raina a kullum ina k’ara gode ma Allah da yabani miji irinka mai tausayi ga iyalinsa

shafo fuskarta haydar yayi yace baby ai kula da ke dolene tunda ni Allah ya azama nauyin hakan fatana Allah yabani ikon cigaba da kula da ke har k’arshen rayuwata,

Sapna kissing d’in bakinsa tayi tace Ameen my hubby, zaka kaini wajen mami ko?
haydar murmushi yayi yace as u wish dear.

wayarsa ce da tad’auki ruri takatse musu hirarsu, d’auko wayan yayi ganin daddy ne yasa yatashi zaune nan suka hau gaisawa

sapna ganin yana waya yasa tamik’e zata bar wajen haydar dasauri yarik’o hannunta, sapna fari tayi masa da ido tace hubby bari ind’an shiga ciki kafin kagama,

sakin hannunta haydar yayi yabita da kallo yana waya.

Bayan ya gama wayar mik’ewa yayi da shirin yabi sapna a bedroom, sallama yaji ana kwad’awa a main parlour amsawa yayi yanufi chan,

wata matace a tsaye take sallaman kallon sani yake ma matar itama kallonsa take tana hawaye,

ganin bai ganetaba yasa tace haydar baka gane niba? nice khadija,

haydar cike da mamaki yake kallonta duk ta rame ta yi bak’i chan kuma sai yad’aure yace mi yakawoki gidana?

khadija hawaye tafara yi tare da tsugunnawa tace haydar dan Allah kayafe min nasan ban kyauta makaba.

haydar tsawa yadaka mata yace tashi kifitar min daga gida tun kan ranki ya6aci kar kimance ke dakanki kikace duk wata alak’a da take tsakaninmu kin yanketa
duk ranar da naga kin tako gidana inmiki duk rashin mutuncin da naga dama
ko kin mance da cin mutuncin da kikayi min keda iyayenki?

khadija fashewa tayi da sabon kuka tace haydar dan Allah kayafe min ko zan samu sauk’in hak’inka da yake bibiyata.

Sapna da tafito neman haydar hayaniyar da tajine a main parlour yasa tanufi chan tana cewa hubby hayaniyar me nake ji.

ido tahad’a da macen da take tsugunne tana ba haydar hak’uri, daga ita har matar sun razana kallon kallo sukeyi, Sapna nunata tayi da hannu tace deedeee deejah! !!!!
itama khadija zumbur tayi tamik’e tsaye tace Sapna,
haydar zuba musu ido yayi yana kallonsu……..

Comment
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

Alk’alamina ba zai ta6a tsayawaba batare da namik’o sak’on gaisuwata agarekuba masoya aduk inda kuka kasance Sis Nerja’art tana yinku over????????

Wannan page d’in nabaku shi a kyauta kuyi yadda kukeso da shi

Page 4⃣1⃣

     _*END*_

????????????????????????????

Deejah a firgice tace mikikeyi a nan gidan? kar dai kice min kece matar haydar,

Sapna binta kawai take da kallo chan sai tace meyakawoki gidana?

haydar kallonsu kawai yakeyi chan sai yace daman kun san juna?
Sapna hawaye suna zuba daga idonta tace yaya haydar wannan itace deejah da nabaka labari,

haydar da mamaki yake kallon Sapna yace deejarki? Sapna gyad’a masa kai tayi alamun eh.

haydar kallon deejah yayi cike da tsanarta yace wannan itace khadija,

a firgice Sapna take kallonsa tace yaya haydar matarka da kata6a aure?
haydar dakyar ya iya cewa eh sannan yazauna saman kujera tare da dafe kansa yana jin tsanar khadija yana k’aruwa acikin ransa.

deejah kuka kawai takeyi tace nashiga ukku yanzu Sapna kece kika auri haydar d’ina wanda nafi so a rayuwata?

Sapna itama hawaye takeyi tace kingani ko deejah? kinga yadda Allah yanufa da ni, tabbas nayi da nasanin saninki a rayuwata domin ke virus ce, dasauri deejah tad’ago kai takalleta

Sapna tace eh deejah kece silar fad’awata a mummunar k’addara , kiduba kiga a lokacin da nakeso ingyara miki rayuwarki in cetoki daga halin da kika fad’a nikuma a lokacin kika gur6ata min rayuwa, dayake Allah ba azzalumin bayinsa bane kinga sai reshe yajuye da mujiya,
yanzu mijinki wanda kikaso shine yazamo mijina, kiduba kiga yadda kika koma a lokaci guda.

deejah cikin kuka tace tabbas Sapna maganarki gaskiya ce nice silar faruwan komai, LAIFINA NE
kaicona da ace ban bi son zuciyaba da duk hakan bata kasance da ni ba, lokacin da naso in6ata miki rayuwa ashe tawa rayuwar nake 6atawa, tabbas nasan na zalunci kaina domin hak’in kune yake bibiyata, na kashe aurena a lokacin da nake ganin waccan rayuwar itace zata fiye min, gani nake mijina ba zai ta6a gamsar dani ba kamar yadda zan gamsu da ‘yar uwata mace, ashe duk tunanina ba hakan bane lallai na yarda lesbian bala’ine duk macen da tafara kafin ta iya bari sai anhad’a da rok’on Allah, domin k’arshen mai aikatawa ba zaiyi kyauba,

kallon sapna take da idanuwanta da suka k’ank’ance saboda kuka tace sapna a lokacin da nazalunceki sai gashi nima nahad’u da k’awar da tayi sanadiyar fad’awata bala’i
hmm dole inkira hakan da bala’i saboda itace tahad’ani da saurayi ganin son inci dukiyarsa sai gashi nakwaso H.I.V.

deejah rushewa tayi da wani sabon kukan tana girgiza kai tace yanzu duba kiga yadda nakoma yau da lafiya gobe babu lafiya, yanzu duk wani nakusa dani ya gujeni, hatta su kansu iyayena sunyi baya da ni sun tsaneni, kawai suna zaune da ni ne dan ba yadda zasuyi, alhali sune silar fad’awana wannan mummunar rayuwar, basu ta6a zama sukaji menene matsalarmuba sudai kawai burinsu suga munyi karatun boko,
sai muyi kwana biyu batare da mun sakasu a idonmu ba duk inda zamuje basu damuwa, basu sa ido domin suga yadda muke tafiyar da rayuwarmu,
ina tausayin duk mutumin da yasamu iyaye irin nawa domin basu dace da sukacen iyaye ba, ammah duk da haka nasan nima da laifina a ciki saboda DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA SHI RUWA KAN DOKA
nayi nadamar abinda na aikata saidai kuma lokacin nadamar ya riga da ya k’uremin domin banyi amfani da damataba a lokacin da nake da damar tawa tatafi,

kallon sapna take da take kuka tace sapna dan Allah kiyafemin ko zan d’an samu d’an sauk’i domin bansan yadda lahirata zata kasance,

sapna cikin kuka tace deejah kije kawai na yafe miki ammah ba dan halinkiba sai dan nasan Allah yana son mutane masu yafiya, muma masu laifine kuma muna neman yafiyar ubangijinmu, saidai ba zan k’ara yarda injawoki a jikinaba saboda kin riga kinmin tabon da bazai ta6a gogewa a cikin zuciyataba, deejah baki dace daniba domin ba halinmu d’ayaba K’ADDARA CE kawai tahad’ani da ke kuma nakoyi darasi akanki, saboda GANI GA WANE ya ishi wane tsoron Allah

Deejah cike da jin dad’i tace nagode sosai sapna Allah yasaka da alkhairi wlh ke macece kuma kece kawai kika dace da haydar ba ni ba. sapna dai kuka kawai takeyi

deejah wajen da haydar yake zaune ya dafe kansa tanufa tatsugunna k’asa tace haydar dan Allah kayafe min wlh sharrin shaid’anne da na abokai, haydar d’ago kai yayi yakalleta tare da wurga mata harara yace zancen banza sai mutum ya gama cin karensa babu babbaka idan duniya ta juya masa baya sai daga baya yadawo yace yayi tubar mazuru,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button