BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Haka rayuwar sapna tacigaba a duk lokacin da zataji ta fad’a wani yanayi tablet din take sha idan yak’are kuma sai tasiyo wani saida yazamana duk inda zataje toh yana cikin jakkarta, lubna abun har mamaki yake bata tana jinjina ma dauriyar sapna ammah har alokacin tana nan da mugun k’udirinta akan sapna.

BAYAN SATI ‘DAYA
Tun wajen 11am tagama shirinta Cikin gown white nd black colour tayi rolling da black d’in veil tajawo handbag d’inta, lokacin wayarta tafara ringing tana ganin lubna ce tayi saurin yin picking tace mummy gani nan zuwa yanzu, cikin sauri tazura takalmanta, bak’in space tasaka a fuskarta, d’akin ummah talek’a taga bata ciki dan haka tafito tanufi kitchen a chan tasameta ita da yarinyar da take zuwa tana tayasu aiki, kallonta ummah tayi tace mamana wannan kyau haka? Ammah dai acire glass d’in, Dariya sapna tayi tacire sannan tace ummah zan wuce Aunty lubna tana chan tana jirana, Ummah tace toh shikenan adawo lafiya. Sapna tana fita tamaida glass d’inta sannan tasamu abun hawa tahau.

Sapna ko da ta isa gidan lubna tun a parlour tafara cin karo da su teemah sun k’ure volume k’id’a na ta tashi suna ganinta suka hau shewa kowa yana yaba kyaun da tayi, teemah tace saidai abu d’aya yahanaki ki ida wayewa, murmushi Sapna tayi sannan tashige d’akin lubna, lokacin da tashiga lubna tafito daga wanka, tsayawa tayi kallon Sapna, kallo d’aya sapna tayi mata takauda kai cikin siririyar muryarta tace mummy lubna ina wuni? Murmushi lubna tayi tace lafiya lou baby gaskiya kinyi kyau sosai ammah kyau kicanza kayan nan kinga wannan birthday d’in k’awar tawa da zamuje na manyan mutane ne k’ara kisa riga da wando, ta6e baki sapna tayi agadarence tace ba na buk’atar hakan, wucewa tayi tabud’e freezer tad”auko ruwa tabud’e jakkarta tad’auko tabs tasha sannan takoma saman kujera tazauna, lubna bata tanka mataba domin tasan wani lokacin idan miskilancin sapna yatashi daga inda tayi magana ba ta canzawa, lubna shiryawa tayi cikin English wears shirt nd skirt sun kamata sosai abu ga mai k’iba, kitsonta tabazo a gadon bayanta, jin ankira sallah yasa sapna tatashi daman da alwallarta takuskuro bakinta tad’auko hijab tasaka, lubna binta take da kallo cike da mamaki tace sapna ya haka? Murmushi tayi tace sallah zanyi sai muje, tsoki lubna taja sannan tacigaba da shirinta, ita kuma sapna takabbara sallarta,

Saida tagama sallarta sannan tatashi tacire hijab d’in, rolling d’in tamaida tak’ara gyara fuskarta sannan suka fito, a motar lubna suna fita.

Bakin wani k’aton gida sukayi horn maigadi yazo yabud’e musu suka shiga tun daga nan sukaji kid’a na tashi, a parking space lubna tayi parking din motarta sannan suka fito, chan filin da ake birthday party d’in suka nufa, wajen ya yi kyau sosai cike yake da mata da maza duk ‘yan barikine a wajen tun da suka nufo wajen nan mazan suka fara kawo musu farmaki sapna da idonta yake dad’e da glass kallonta kawai zakayi kagane fuskarta a d’aure take, duk namijin da yayo wajenta tun kan ya iso take tsaidasa da hannunta kan dole suke barinta saidai sukoma wajen lubna, bafday gurl d’in suka hango cikin riga da wando sun d’ameta ta yi kyau sosai da kaganta kaga cikakkiyar ‘yar duniya, wajenta lubna taja sapna suka nufa tana hangosu dagudu tazo suka rungume juna ita da lubna cike da murna lubna tace fidoh kinganki kamar bakeba wannan irin kyau haka? Dariya wadda aka kira da fidoh tayi tace dear tun d’azun ina ta jiranki shuru sai yanzu zakizo? Kallon sapna tayi tace wow dear wannan babyn fa? Dariya lubna tayi, fidoh sai Kallon sapna take da tabi tahad’e face tace dear ki aramin ita please, lubna Kallon sapna tayi tace sapna baki gaisheta, sapna agadarence tace sannu fa ina wuni? Yanayin hakan da tayi sai tak’ara birge fidoh, cikin sakin fuska ta amsa sannan takalli lubna tace wlh babyn nan taki ta yi ba k’arya, dariya lubna tayi tace kizo muje acigaba da shagali nifa kinsan wajen disco nan nafi afki kuma da alama akwai manyan Alhazai, dariya fidoh tayi tace akwaisu fa k’awata sai kin darza, cikin jin dad’i lubna tace yauwa k’awata saisa nakeson ki saboda bakya k’aramar harka, nan suka sa dariya tare da ta6awa, lubna Kallon sapna tayi tace muje, yamutsa fuska sapna tayi tace no kuje kawai Aunty lubna ni zan zauna a chan saman waccan chair d’in, lubna ta san halin sapna sarai dan haka tace ohk baby kikula da kanki, sapna batace komaiba tanufi wajen plastic chair d’in tazauna tana raba ido, kayan shaye-shaye ne kala-kala tagani aje duk maiso sai yayi magana a basa, hannun tad’aga ma mai kawowar alamun yakawo mata, daidai lokacin wani had’ad’an guy yazo kusa da ita yazauna yace sannu ko baby,
Sapna ko inda yake bata kallaba tacigaba da dannar wayarta daidai lokacin aka kawo mata, kwalbar giya tad’auka shima mutumin ganin ta d’auka yasa shima yad’auka yace baby please idan ba zaki damuba inaso kibani had’in kai ind’an huta da ke, Sapna d’ago kai tayi tawatsa masa mugun kallo sannan tabud’e murfin giyanta tafara sha, murmurshi mutumin yayi sannan yace gaskiya baby kina burgeni dayawa ya kamata kitaso mu d’an shiga filin chan, ita dai sapna bata tankasaba kallon su lubna take cike da takaici yadda suka shiga tsakiyar maza suna ta6asu son ransu, ganin inda take kallo yasa guy d’in yayi murmurshi yace baby kizo muma mushiga, ni da zaki bani dama da munje gidana wlh zan baki kud’i masu tsoka,
Sapna ahankali tacire glass d’in da yake manne a fuskarta cikin 6acin rai tace kai kana tunanin ka kai matsayin da zan kulaka? Kaduba kaga fa na yi kama da class d’inka?
Murmurshi guy d’in yayi yace wlh baby kina burgeni kifad’i yadda kikeso zan baki, hannu yakai zai rik’o hannun sapna dasauri sapna tajanye hannunta cikin 6acin rai tace indai kakuskura kata6ani wlh sai ka gane kurenka, Sapna cigaba tayi da shan giyarta duba tym tayi taga 4:30pm har lokacin lubna bata da niyar zuwa sutafi gida, Kiran ummah ne yashigo wayarta cikin sauri tad’auki wayar Yanayin yadda taji ummah tana magana ne yatabbatar mata da batada lafiya a firgice tace ummah baki lafiya ne me yasameki? Shuru taji ummah ta yi saidai nishi da take sama-sama, cikin tashin hankali sapna ta aje kwalbar tatashi tsaye tafara tafiya cikin tangyad’i kamar zata fad’i dasauri guy d’in yatashi tare da rungumota jikinsa cikin 6acin rai sapna tad’ago hannu tad’aukesa da mari tare da kwace jikinta tace kak’ara gigin ta6ani sai ka gane kuskurenka, cikin tafiyarta kamar zata fad’i tadinga ratsa mutane tana buge wasu, wasu mazan suna ruk’ota tana turesu ahaka ta isa inda lubna take, rawa take hankalinta kwance, rik”ota sapna tayi ta baya, cikin 6acin rai lubna tajuyo domin taga wanene yake neman tsaidata daga rawar da take, ganin sapna ne yasa lubna tad’aure fuska, sapna tana lumshe ido tace please mummy lubna kizo kikaini gida ummana bata da lafiya, batare da lubna ta damuba tace ni babu inda zanje batare da antashi wannan partynba kitafi kawai, k”wallace tafara zuba daga idanun sapna, ganin haka yasa lubna tacigaba da rawarta, juyawa sapna tayi tana tafiya kamar zata fad’i mazan da ke wajen suna ta rik’ota alamun tazo suyi rawa itakuma tana turesu duk maganar da suke mata batasan ma me suke cewaba ahaka har tazo gate tafita, tsaye tayi wajen ta yi kusan minti goma tana jiran abun hawa ammah bata samuba k’wallah kawai take hankalinta atashe, daidai lokacin wata dank’areriyar mota tazo wucewa, tun daga nesa da yahangota saida gabansa yafad’i domin yagane wannan itace yarinyar da yake nema tsawon shekara d’aya da Ta wuce tabbas fuskarta ba zata ta6a 6oyuwa a wajensaba………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button