BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

K’ara gyara kwanciyarta tayi tace eh wlh mummy

Lallai daughter ko dai a bige kike ne.

Hmm A’a mummy baccin kawai yazo.

Lubna ba dan ta gaji da hirar da itaba dan ba yadda zatayi yasa sukayi sallama.

Aje wayar sapna tayi sannan tajawo kwalbar giyar da take cikin bag d’inta tunda tad’aga kai tafara kwan-kwad’a bata aje ba sai da tasha kusan rabin kwalbar.

Ahankali taga ta fara ganin komai ya koma mata bibiyu dakyar ta kulle kwalbar takoma takwanta ba a dad’eba bacci 6arawo yasaceta

yawan comment yawan typing

Muje Zuwa
????????????????

 _*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA...*_

              ????????????????


_(TRUE LIFE STORY)_

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

kuyi hak’uri da canza sunan novel da nayi daga BA LAIFINA BANE zuwa DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA…

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

BASED ON 2RUE LIFE

Page 3⃣➖4⃣

Alarm d’in wayantane yatadata daga baccin da take dakyar tabud’e idonta takashe jin ana kiran sallah yasa tatashi tanufi toilet tayo alwallah,

Raka’atanil fijir tayi tazauna tana lazimi har aka kabbara sallah sannan itama tatashi tayi,

Bayan ta gama sallah karatun alkur’ani tazauna tayi har saida gari yafara haske sannan tayi addu’a tatashi tahaye gadonta takoma bacci.

Wajen k’arfe goma tafarka brush tayi tad’auro alwallah tazo tayi sallar walha.

Bayan ta gama tafito tanufi d’akin ummah dasallama tashiga bedroom d’in ummah tanufa taga har time d’in bata tashi bacci ba fitowa tayi tagyara gidan tahad’a masu breakfast.

‘Dakinta takoma tayi wanka tashirya cikin had’ad’d’en less sky blue,
Gashin kanta tagyara tatufk’eshi a baya, ko da bawata kwalliyar kirki tayiba ammah tayi kyau sosai,

Kitchen tashiga tad’auko breakfast d’in da tahad’a masu tanufi d’akin ummah.

Sallama tayi tashiga ta aje sannan tanufi bedroom d’in ummah,

Ummah zaune take tana shiryawa bayan ta fito daga wanka,
Murmushi tayi tace ummana ina kwana?
Kallon d’iyartata tayi cikin so da k’auna tace lafiya lau sapna, dafatan kintashi lafiya.

Lfy lau ummana, ummah ga breakfast d’in chan parlour,
Toh sannu sapna, yauwa ummah

Dan Allah ummah ina so zanje chan gidan lubna tana nemana zan rakata anguwane.

Murmushi ummah tayi tace bakomai sai kin dawo ammah kizauna kifara breakfast na san bakici komai ba.

Toh ummah bari inje inyi sai intafi.

Ummah tana mamakin yadda bata iya hana sapna zuwa ko’ina ko da ace kwana zatayi ba ta iya hanata kuma ba ta iya tambayarta daga ina kike indai ba ita sapna tafad’a mataba saidai wani lokacin tayi ta jin abun yana d’an damunta a ranta.

Ita kanta sapna tun tana mamakin rashin hanata da ummah batayi har tazo tadaina.

Agurguje tayi breakfast takoma d’akinta tad’auko veil da handbag white colour takalmanta ma white colour ne.

Wayarta tad’auka tanufi d’akin ummanta tace ummah zan tafi sai na dawo.

Murmushi ummah tayi tace adawo lafiya my daughter.

Tana fitowa batasha wahalaba wajen samun abun hawa tace akaita burget…

Ko da suka isa ita tayi gwada hanya har sukazo gidan tabiya mai adaidaita kud’insa sannan tabud’e gate d’in gidan tashiga.

Gidane babbah babu laifi da anshigo da anshigo main parlour ne mai girma wanda aka k’awata da manyan kujeru masu kyau da tsada, sai plasma tafkekiya a jikin bangon.

Bedroom hud’une a cikinsa sai kitchen,
Kowane bedroom da kalar kayan da ke cikinsa.

Da sallama tashigo ta yi sa’a bakowa cikin parlour ta6e baki tayi tace ynz haka suna wajen sharholiyarsu.

‘Dakin mummy lubna tanufa, bedroom d’in babbane sosai yana d’auke da royal bed sai wardrobe, dressing mirror, sai plasma da aka manna a bango, sai aka zuba kujeru su ma masu kyau sai freezer dake cikin d’akin, komai na d’akin lemon green colour ne.

Tura d’akin tayi da sallama tashiga batayi mamaki ba ganin mummy lubna kwance da wani k’ato saman gadon ta yi d’ai-d’aya a jikinsa.

Suna ganinta basu damu ba.

Ta6e baki tayi ba tare da ta tanka masu ba tanufi wajen bedside tad’auko kwayoyi tanufi fridge tabud’e tad’auko lemu tazuba k’wayoyin a ciki.

‘Dago kai mummy lubna tayi takalleta tace daughter kinsan fa zamu fita da kin bari sai munje chan sai kisha, idan kika bugu fa ya zanyi dake za ki 6ata min lokaci.

Ba tare da ta kalli inda sukeba tace sai kijirani intashi kokuma ki tafi kekad’ai ko kisamu wani yarakaki.

Bata jira amsar da zata bataba tadawo parlour tazauna girgiza lemun tayi sannan tabud’e tafara sha saida tasha mai isarta sannan ta aje.

Sumy ce daidai lokacin tashigo d’akin kallonta tayi tasakar mata murmushi tace baby sapna har kin iso kenan,

Dakyar sapna ta iya daga idonta takalleta saboda nauyi da sukayi mata bata tanka mataba tafara lumshe ido alamun zatayi bacci.

Sumy tana ganin haka tagane a buge take murna tafarayi a ranta tana tunanin burinta yau zai cika murmushi tayi tace sapna tashi muje d’aki kikwanta kinga zakifi jin dad’in baccin saman bed mik’a hannu tayi zata rik’ota,

‘Daga mata hannu sapna tayi dakyar tabud’e baki cikin muryarta wadda da anji ansan a buge take tace no Aunty Sumy kibarni kawai nan zan kwanta.

Haba sapna waike meyasa bakida yarda nifa ba cutarki zanyiba ammah sai kiyi ta guduna

Kibarni kawai nace Aunty Sumy nan nake ra’ayin kwanciya lumshe ido tafara yi alamun bacci ya fara d’aukarta dak’yar ta iya kwanciya saman kujerar saboda jikinta duk ya yi mata nauyi.

Bata dad’e da kwanciya ba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.

Lubna ce tafito daga d’akin domin taraka bak’onta kallon sapna tayi da taketa bacci hankalinta kwance,

Murmushi tayi tace sapna akwai rigima.

Bata tashetaba takoma d’akinta,
Wanka tayi tashirya cikin riga da skirt na atamfa sun matseta sosai.
Kwalliya tayi gwanin kyau daman gata kyakkyawa nan kyawun nata yak’ara fitowa.

Falon tadawo tanufi wajen sapna tana girgizata tace sapna kitashi hakanan please kinga har k’arfe biyu ta kusa.

Ahankali sapna ta bud’e idanuwanta tasafkesu akan fuskar lubna.

Murmushi lubna tayi tace please kitashi kishirya muje.

Tashi tayi jikinta duk ba k’wari tanufi bedroom d’in mummy lubna,

Wanka tashiga tayi tare da d’auro alwallah.

Lokacin da tafito tatadda mummy lubna har ta fito mata da kayan da zata saka daga cikin wardrobe.

Dressing mirror tanufa tashafa mai sannan tad’anyi makeup.

Kayan tanufa tad’auko zata sanya,
Batayi mamakin ganin k’ananun kaya tad’auko mataba.

Riga ce red mai ratsin black har gwiwa sai wando pencil bak’i tare da gyalen rolling.

Kayan tasanya sai tad’auko hijab tasa.

Lubna takalleta tace daughter miye kuma na sanya hijab.

Mummy lubna sallah fa zanyi kinga har k’arfe biyu ya yi kar lokacinta ya wuce.
Bata jira jin mai zataceba tashimfid’a darduma takabbara sallah. ……

yawan comments yawan typing✍????

Muje Zuwa

Real Sis Nerja’art
????????????????

 _*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA...*_

             ????????????????

   _(TRUE LIFE STORY)_

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA AND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button