BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

sapna cikin ranta tace wannan mugun zai fad’amin, can kuma sai tace ayya ina ji ya mancene, dariya hafsat tayi tace baidai yi niyar fad’a miki bane ai nasan halin yayana sai ahankali, murmushi sapna tayi tace toh ya kika barosu dafatan duk suna lfy?
hafsat tace lafiya lou, ya bak’unta?
sapna tace gashinan muna ta fama, gaba d’ayansu sukasa dariya daganan suka hau yin hira, sapna tana ta wasa da afrah,

kallon agogo hafsat tayi ganin 12pm tayi yasa tamik’e tace matar bro bari intafi inje infara shirya kayanmu kinsan gobe zan tafi,

sapna marairaicewa tayi tace kai mummyn Afrah tun yanzu? hafsat murmushi tayi tace ai zani dawo idan nagama, sapna tace to dan Allah kidawo, hafsat tace insha Allahu zan dawo,

har bakin k’ofa sapna tarakata sannan tamik’a mata afrah sukayi sallama, bayan ta dawo kitchen tawuce tad’aura girki, wajen 1:30 tagama nan tagyara ko’ina sannan tashiga wanka,

bayan ta fito shiryawa tayi cikin material brown colour d’inkin riga da skirt ne sun kar6eta sosai,

bayan ta yi Sallah zuwa tayi tacire wayar daga charge cike da jin dad’i takoma saman gado tazauna takunna wayar da mamakinta taga har da sim aciki, cike da jin dad’i takira ummah

ummah tana d’auka ko sallama batayiba tace ummana nayi missing d’inki, ummah tana jin muryar sapna murmushi tayi tace mamana ko sallama ba’abari ayi? itama sapna murmushi tayi tace yi hak’uri ummah d’okine kawai nake, ina wuni?
ummah tace lafiya lou ya mijin naki dafatan duk kuna lfy?
sapna tace lafiya lou muke ummana, kema dafatan kina lfy? wlh ummah jinake kamar indawo incigaba da zama da ke nayi missing d’inki dayawa.
murmushi ummah tayi tace sapna kenan ai hak’uri zakiyi ahaka zaki saba gidan miji ai shine mutuncin mace ba wai gidan iyayentaba.
dan haka kikula kiji tsoron Allah kirik’e mijinki hannu bibbiyu domin indai kika bari haydar yaku6ucemiki bawai fata nake mikiba bana tunanin zaki sami miji kamarsa,
sapna shuru tayi sai kuma can tace toh ummah insha Allahu
ummah cike da jin dad’i tace yauwa sapna Allah yaimiki albarka,
Sapna tace Ameen ummana, daga nan suka hau yin hira saida sukayi kusan minti talatin sannan sukayi sallama, sapna cike da jin dad’i tabi wayar da kallo tana murmushin jin dad’i,

bata ankaraba sai ganin haydar tayi ya shigo d’akin binsa tayi da kallo cike da mamaki domin bataji dawowarsaba saidai taga ya shigo,

haydar kallo d’aya yayi mata yad’auke kai, ganin haka yasa sapna ciki-ciki muryarta can k’asan mak’oshi tace sannu da zuwa,
haydar kamar ba zai amsaba saida aka kusan minti d’aya sannan yace yauwa.
takaicine yacika sapna cikin ranta tace mutum sai jin kan tsiya saikace mace, ganin yana shirin cire kayane yasa tatashi tafita daga d’akin tadawo parlour tazauna.

bayan kamar minti biyar sai ga haydar ya fito, sapna kallonsa tayi ya yi mata kyau sosai ganin yana sanye da k’ananun kaya sai k’amshi ke tashi cikin ranta tace gaskiya guy d’innan ya had’u,

batasan ma tashagala da kallonsaba saida yace baby wannan kallon fa nayi miki kyau ne? kinga d’an had’ad’d’en saurayi ki k’yasa.

dasauri sapna tad’auke fuskarta daga kallonsa tare da murgud’a baki, tace Allah yasauk’e insoka. murmushi haydar yayi yace baby muje kizuba min abinci inci sauri nake infita jirana akeyi.

sapna saida gabanta yafad’i jin ya ce zai fita, cikin ranta tace ai nasan daman wajen wata zayaje, shuru tayi takyalesa,
haydar yace ko bakiji bane,
sapna kamar zatayi kuka takallesa tace ai ita wacce zakaje wajenta d’in sai tazo tabaka kaci, tashi tayi tashige bedroom tabarsa nan tsaye

murmushin jin dad’i haydar yayi yace sapna kenan sarkin kishi, dining yaje yazuba abincin yaci agurguje sannan yatashi tashiga bedroom yasamu sapna a zaune saman gado tazuba ma gefe d’aya ido,

haydar key d’in motarsa yad’auka sannan yace baby zan tafi kibada sak’on gaisuwa afad’a ma ‘yar uwarki, nan sapna ta ida k’ulewa jitake kamar takamosa tacigaba da dukansa,
haydar ganin ya hayak’ata yasa yawuce yana cewa toh nidai natafi kar tajini shuru tayi fushi da ni.

sapna tana jin tashin motorsa nan takife kanta saman gado tacigaba da rusa kuka.


Lubna tunda sukaje Abuja harka kawai suke da manyan Alhazai kud’i ta ko’ina suna shigo masu,

yauma Lubna ce da amfa zaune a cikin katafaren d’aki, gefensu apple ne suke ci, amfa takalli Lubna tace k’awata kinga yadda kika koma kuwa kin k’ara kyau da fresh, dariya lubna tayi irin tasu ta ‘yan duniya tace kedai bari k’awata ai mu wannan rayuwar gaba takaimu tunda jakkunanmu cike suke da kud’i, shewa sukayi gaba d’ayansu suka tafa,

amfah tace wai k’awata ya maganar tafiyanmu gida gobe? Ta6e baki lubna tayi tace tana nan daram, amfah tace dafatan dai Alhaji mai nasara ya san zaki tafi, lubna dariya tayi tace ai kinsan dole ma yasani yanzu hakama har ya sallameni, dariya amfah tayi tace nima kau kinsan saida nayagi abinda nayaga wajen Alhajina, lubna tace ai wlh k’ara muyi ta yagar rabonmu a wajensu ahaka muma mutara abinda muka tara, amfah ni wlh na k’agara gobe mukoma gida ko dan saboda inga sapna,

ta6e baki amfah tayi tace kedai har yanzu kina son wannan banzar yarinyar, 6ata fuska lubna tayi tace ya isa haka kar kik’ara cemata banza nifa kinsan akanta zan iya komai, ke ni ban ma san ta shiga raina hakaba saida nayi nisa da ita tsawon wad’annan watannin, dariya amfah tayi tace Allah yahuci zuciyarki ai ni na d’auka tuni kin cireta daga rai ko dan wannan abin da yashiga tsakaninmy da ita,

dogon numfashi lubna taja tace wlh na kwad’aita da yarinyarnan ko da ace zan iya rabuwa da ita toh dole sai na moreta son raina bari dai mukoma gida zaki ga aiki da cikawa, amfah tace ai nasan zaki aika indai kece, ammah ni innice na barta, lubna gyara zamanta tayi tafuskanci amfah sosai tace k’awata wai ya wajen deejah ni fa ko labarinta bana ji wayarta ma bata shiga idan nakirata,

amfah ma gyara zamanta tayi tace deejah tana nan ko shekaran jiya munyi waya kinsan ai aurenta ya mutu yanzu haka tana kd ta cigaba da karatunta ammah harkarta kawai take,

dariya lubna tayi tace ai nasan deejah ba zata iya zaman aureba yadda tasaba da harka ammah kuma na yi mamakin yadda duk take son mijinta har suka iya rabuwa,

amfah ta6e baki tayi tace ke abin takaicinma ashe tare take da humaira ban saniba tayaudareni sai gashi ita tayi sanadiyar mutuwar aurenta.

lubna afirgice tace yanzu humaira ce silar mutuwar auren deejah? toh garin yaya hakan tafaru?

amfah batare da damuwaba tace uhm kedai bari kawai, rabon dubunta ce zata cika rannan mijinta yakamasu daga nan yasaketa,

ko da takoma gidansu k’arya tayi ma iyayenta saida sukayi rikici sosai da mijjnta shi kuma yaji bai iya tona mata asiri bai fad’a ma iyayen halin da d’iyarsu take cikiba saboda a yarda yalura da sun yarda da d’iyarsu gani yake ko ya fad’a musu ba zasu yarda ba,

haka akaje aka kwaso mata kayanta tadawo gida, bayan ta gama idda ne suka turata kd domin taje tacigaba da karatunta daga nan tabud’e sabuwar harka.

cike da mamaki lubna tace ya akayi toh ni duk ban san abinda yafaru ba, murmurshi amfa tayi tace su ma su teemah duk basu saniba sai daga baya, nima fa kaina bata fad’a minba, ko da na ce zanje gidanta sai tayita min kame-kame a k’arshe dai a wajen humairah naji komai, sai daga baya natambayeta shine take warware min komai,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button