BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Ahaka har suka shiga final year d’insu ammah babu wani canji daga wajen deejah, deejah da tazauna labarin Saurayinta takeba sapna kuma kullum sai suyi waya sama da sau ukku a school, sapna har mamakin hakan take domin ita gani take bata iya tsayawa tadinga fad’a ma saurayi kalaman da taji deejah tana fad’a saboda gani take sai yarainata ko da yake sapna batasan menene so ba saboda Sapna har lokacin batada wani saurayi da taji tana so.

Bayan wata biyu sapna sun maida hankali karatu suke babu kama hannun yaro saboda final exam d’in da zasu fara hatta ita kanta deejah Yanzu ta maida hankali wajen karatunta ta rage shashanci,

Yau kasancewar Asabar ce Sapna ce take tafiya cikin nutsuwa da hijab d’inta har k’asa sun tashi daga islamiyya zata koma gida, daidai k’ofar gidansu ta tadda deejah tsaye jikin wata mota da waya a hannunta da alama number d’in Sapna take dubowa, dasauri Sapna tazo tatarbeta cikin murna da mamakinta macece tayi driving d’in mota d’in dukkansu babu mai shigar kirki a jikinsa nan sapna ta gaisheta domin bata kawo komai a rantaba, Kallonta Deejah tayi tana dariya ta rainin wayau tace ‘yan mata ana ta zuwa islamiyya, dariya sapna tayi tace muna fa tazuwa kushigo daga ciki, deejah duba agogon hannunta tayi tace a’a sauri muke nakawo miki card d’in bikkin Aunty khausar ne, cikin jin dad’i sapna tace wow yaushene bikkin?
Deejah tace next week ne,
harararta sapna tayi tace shine ko a school baki fad’aminba sai yanzu?
Deejah taye ashe ban fad’amikiba, sorry wlh na shafa’ane I thought na fad’amiki,
Sapna kallon wacce take cikin motar tayi tace wannan itace Aunty khausar d’in,?
Girgiza kai Deejah tayi tace wannan mummyna ce Amfah,
Itadai sapna bata gane komi Deejah take nufiba dan haka tace kushigo ciki kunga sai kugaisa da ummana,
Deejah yewa tayi a’a sapna ai munyi dare,
Harararta Sapna tayi tace indai baki shigoba wlh ba zanzo bikkinba kar ma kibani IV d’in,
Deejah kallon ta cikin motar tayi tace Baby bari inshiga ba zan dad’eba,
Murmushi ta cikin motar tayi tace ohk dear, please kiyi sauri,
Ko da suka shiga a tsakar gida suka iske ummah nan Deejah tagaisheta ta amsa cikin fara’a da sakin fuska, ummah tace Sapna kishiga da ita d’aki mana,
Deejah tace a’a ummah sauri muke dare keyi daman I.V ne nabikkin yayata.
Ummah tace Allah sarki yaushene bikkin?
Next week ne ummah.
Toh Masha Allah, Allah yakaimu Allah yasa alkhairi,
Deejah da sapna atare sukace Ameen sannan tad’auko I.V d’in tamik’a ma Sapna tace bari inwuce kinga jirana ake, nan tayi sallama da ummah,
sapna har wajen mota tarakata saida taga tafiyarsu sannan tashigo gida, tana shigowa har ta wuce zata shiga d’akinta nan ummah takirata,
Amsawa tayi sannan tajuyo tadawo inda ummah take,
Kallonta ummah tayi tace Sapna nidai hankalina bai kwanta da wannan yarinyarba kiduba fa kiga irin shigar da tayi,
Murmushi sapna tayi tace ummah kikwantar da hankalinki yadda kike tunani ba haka Deejah takeba kawai dai ita kalar gayun ne nata,
Cikin damuwa ummah tace sapna gayu ne haka? Da ace haka ake gayu ai da mutane dayawa sun hak’ura da gayun, ni dai a kullum ba zan gaji da fad’a mikiba kiguji k’awayen banza, kiji tsoron ubangijinki,
Sapna tace to ummah nagode, Allah yasa mudace,
numfashi ummah taja tace Ameen ya rabb,
Jin ana kiran sallah yasa sukayi alwallah a d’akin ummah sapna tayi sallah, bayan sun gama sapna k’arin tilawar alk’ur’ani tayi ma ummah har saida aka kira sallar isha’i sannan suka tashi sukayi sallah isha’i sannan sapna taje kitchen tad’auko musu abinci sukaci bayan sun gama suka d’an ta6a hira sai wajen k’arfe tara sannan sapna tayi ma ummah sallama takoma d’akinta, wanka tayi tashirya cikin kayan bacci sannan tajawo littafinta tafara karatu sai wajen 11 sannan ta aje takwanta bacci.

Bayan sati d’aya
Tunda aka fara hidimar Sapna bataje ba saboda partyn da za’ayi kusan kala hud’une, yau kasancewar ranar ake yinin bikki yasa Sapna tashirya cikin ashoben da akayi pink colour ba wata kwalliya tayiba sosai, after dress tad’aura a saman kayan sannan tayi rolling da veil d’in rigar, ‘yar puse tad’auka taziri Takalmanta saida tabiya tad’akin ummah tace mata zata tatafi nan ummah tayi mata adawo lfy.

abun hawa tasamu tafad’i inda za a kaita ko da suka isa anguwarsu Deejah batasha wuyaba wajen gano gidansu saboda gidansu sananne ne a anguwar, kiran deejah tayi tafad’a mata gata a k’ofar gidansu, deejah da murnarta tazo tatareta tace ammah dai besty na yi fushi yanzu saboda Allah sai yau zaki lek’oni?
Mutmushi sapna tayi tace kiyi hak’uri hidimace ta6oyeni ammah yanzu ai gani nazo,
Harararta deejah tayi tace daman ai nasan haka zakice,
Deejah saida tafara kai sapna part d’in mummynta suka gaisa sannan tatafi da ita part d’insu,

Ko da suka shiga yanayin yadda taringa ganin wasu da suke zaune a d’akin yasa jikinta yayi sanyi, deejah wajen khausar takaita suka gaisa nan Sapna tayi mata Allah yasa alkhairi, ta yaba da kyaun da amaryar tayi, Waje deejah tanuna ma sapna tazauna a bakin gano, tunda sapna tazauna nan wadda take zaune kusa da ita tatsareta da ido, Sapna wayarta tajawo tahau chart cike da takaicin kallon da matar takeyi mata,
Daidai lokacin deejah tashigo da kaya nik’i-nik’i ta aje gaban sapna sannan tazauna kusa da ita.

Wadda take gefen sapna tace deejah wannan fa? Mutmushi deejah tayi tace Aunty lubna friend d’ina ce, .wadda aka kira da Aunty lubna tace Allah sarki gaskiya ta had’u dayawa,
Dariya deejah tayi tace sunanta Sapna,
Muryar matar tajiyo ta ce wow nyc name sunan naki ‘yan mata,
Sapna murnushi tayi a tsorace tace nagode, saboda yanayin yadda taga mutanen wajen majority d’insu duk ‘yan barikine,
Muryar amaryar tajiyo tana cewa ya dai Lubna ko kin k’yasa ne? Dariya Lubna tayi tace ba mamaki khausar ammah dai ina zuwa, tashi lubna tayi takalli Deejah tayi mata sign da idonta, deejah ganin hankalin sapna yana a kan waya yasa tatashi tace besty ina zuwa, Sapna tace toh,
A chan gefe guda deejah ta iske lubna tsaye tana jiranta,
Kallonta lubna tayi tace k’anwata gaskiya wannan k’awar taki ta burgeni kin dai gane abinda nake nufi,
Zaro ido deejah tayi tace Aunty lubna kirufa min asiri wlh wannan da kike gani ba ‘yar hannu bace bata wayeba, dariya Lubna tayi tace ni zan wayar da ita kinsan in inason abu toh wajibine in samesa kuma dolene tayi accepting dina dan daga ganinta zan more dayawa,
Dariya deejah tayi tace wlh na ji dad’i dan nima tun tuni na k’yasa da ita tsoro nake kar tarabu dani shiyasa nayi shuru ban furta mataba saboda rannan ma da nayi sanadiya takur6i giya wlh rabuwa tayi dani dakyar nasamu nalallasheta ta amince mukacigaba da k’awance saidai idan zakibi ta wata hanyar toh zan taimaka miki,
Dariyar jin dad’i lubna tayi tace kar kidamu tunda dai nace inaso toh dolene tayarda dani saboda ina alfahari da kaina ban ta6a neman wani abu ba narasaba kuma ba zan fara daga kantaba dan haka yanzu zanje wajen malamina domin yayi min aiki akanta koma dai ya mukayi dashi zakiji inyaso sai kitaimaka min, dariya deejah tayi irin ta ‘yan duniya tace nikuma zan taimaka miki domin nima insamu rabona,
Lubna tace bari ma kigani inje ind’auko jakkata yanzu zanje wajensa.
cikin jin dad’i deejah tace Aunty lubna aikinki yana kyau wlh.
lubna wucewa tayi tana tafiya tace kad’an ma kika gani daga cikin aikina, d’akin tashiga tad’auko jakkarta tunda tashiga suke kallonta,
Amaryar ce tace a’ah lubna sai ina kuma?
Murmushi lubna tayi tare da kallon sapna da hankalinta yana akan waya sannan tace aikine yataso min shine nakeso inje inyosa a yanzu,
‘Daya daga cikinsu ce tace ko dai ta samune k’awata?
Dariya lubna tayi irin ta ‘yan duniya tace ina fa tasamu kina ganin kayan ba zasuzo hannuba cikin sauk’i saisa nakeso inje inga yadda zani 6ulloma al’amarin,
Shewa sauran matan sukayi sukace angaisheki lubna sa’a daga gareki take.
Dariya lubna tayi tare da d’aukan key d’in motarta sannan tace duk abinda nasa a gaba sai na samesa saboda sa’a ta dan haka kuzuba ido kugani sai kun jini, kallon sapna tayi a karo na k’arshe sannan taficce daga d’akin itadai sapna bata gane komai ba daga maganar da suke, nan deejah tashigo suka zauna suka d’an ta6a fira saida daga magrib ta gabato sannan tayi musu sallama tatashi deejah tarakata tasamu abun hawa tatafi gida. …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button