BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Comment
nd
Share

Sis Nerja’art✍??
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Page 2⃣1⃣➖2⃣2⃣

Sapna tana isa gida d’akin ummah tafara shiga da sallamarta lokacin ummah tana zaune tana yankan farce, kallonta ummah tayi tana murmushi tace a’a mamana har kin dawo? Saman kujera Sapna tafad’a tazauna tace wlh ummah na dawo mummynsu ma tana gaisheki ga ma kayan bikki da suka bada, ummah tace masha Allah anko gode Allah yabasu zaman lafiya, Sapna tace Ameen sannan tatashi tad’auki jakarta tace ummah bari inshiga d’aki Ind’an watsa ruwa kafin akira magrib, ummah tace toh shikenan mamana.

Lubna ko da tafita motarta tashiga bata zarce ko’inaba sai gidan malaminta da Sallamarta tashiga cikin jin dad’i matansa suka tarbeta nan sukace aikam kinyi sa’a yanzunnan malam yashigo lubna tace Allah sarki matarsa d’aya tatashi tace bari inje infad’a masa zuwanki, ko da tashiga tasanar da shi cikin jin dad’i malam yace ace tashigo, ko da lubna tashiga malam cikin jin dad’i yakar6eta tare da nuna mata waje tazauna, malam yace me yake tafe dake ranki yadad’e?, lubna gyara zama tayi sannan tace malam wani aikine yake tafe da ni idan kacika min shi zan baka kud’i masu tsoka, cikin jin dad’i yace kifad’a aikinki nikuma incika miki shi,

Cikin jindad’i Lubna tace wata yarinyace nakeso kayi min aiki akanta inaso kasa tasoni kuma duk umurnin da zan bata ba zata k’etaresaba, kai ba ma ita kantaba hatta mahaifiyarta bazata ja da maganataba saboda naji ance mahaifinta ya rasu kaga aikin zai zo mana da sauk’i Dan haka inaso tazo a hannuna sai yarda nayi da ita.

Tunda tafara maganar malamin zane yake a k’asa yana sharewa sai chan yace minene sunanta tace sapna, saida yarubutu sunanta kusan sau ukku yana sharewa sannan daga k’arshe yad’ago kai yakalleta yace hajiya aikinki zaiyi wuya gaskiya saboda yarinyarnan akwai tsari a jikinta itada mahaifiyarta suna da k’arfin addu’a,

Cikin tashin hankali lubna tace yanzu malam ya kake gani za’ayi yanzu kataimakamin ko nawane wlh zan iya biya Indai zakayi min aikin nan, dariya malamin yayi yace ai babu abinda zai gagareni zanyi iyakar k’ok’arina in sunsan wata basusan wataba, yanzu yadda za’ayi kije gida zan yi bincike bayan sati d’aya kitafo min da gashin kanta ko ya yake saboda dashi zanyi aikin, mahaifiyarta ko kibarni da ita nasan yadda zanyi da ita saboda aikinta mai sauk’ine na yarinyar shine mai wahala ammah zaki bada dubu goma wanda za ayi sadaka da shi, cikin jin dad’i lubna tace godia nake malam ai nasan aikinka kamar yankan wuk’ane dan haka zan iya biyan ko nawane, dubu goma lubna tajawo ta aje gaban malam sannan ta d’auko dubu biyar ta aje tace wannan kuma nakane kasha ruwa kafin aiki yacika, malam washe baki yayi yace nagode sosai hajiya, tashi lubna tayi tafito matan malam dubu biyu tabasu sunata murna da godia sannan taje tashiga motarta tanufi gida lokacin dare ya yi, tun a mota takira deejah tafad’a mata yadda sukayi da malam tare da cewa tataimaka mata wajen ganin ta samo gashin kan sapna, cikin jin dad’i deejah tace gaskiya naji dad’i sosai da jin labarin nab nikuma insha Allahu zan samo miki gashin kanta cike da jin dad’i sukayi sallama.

Bayan sati d’aya Sapna da Deejah zaune suke a class kowace rik’e take da book d’inta tana karatu inda sauran ‘yan class d’in wasu suna surutu wasu suna note, deejah kallon sapna tayi tace besty wani kitsone da akayi miki Wanda kika kwance yaburgeni sosai gaskiya matar ta iya kitso, murmushi sapna tayi tace aikam dai bamuda nisa da ita anguwarmu d’aya idan kinaso kizo zan rakaki, deejah tace aiko dai zan
Zo ammah sai lokacin da zakiyi kitso sai inzo muyo tare, harararta Sapna tayi tace ko ma da ace ba kitson zanyiba bakikai matsayin da zan aje hidimata inrakakiba? Dariya deejah tayi tace na san nafi k’arfin hakan a wajenki ammah ni nafiso muyi tare, murmushi sapna tayi tace toh shikenan next week sai kishigo muje, cikin jin dad’i deejah tace yauwa besty gaskiya naji dad’i sosai na gode, ko da deejah takoma gida kiran lubna tayi tafad’a mata yadda sukayi da sapna nan lubna tayita murna da godia,

Ranar asabar bayan sapna ta dawo daga islamiyyar safe cikin sauri tad’aura girki kafin 12 ta gama, wanka tashiga tayi tana cikin shiri tajiyo sallamar deejah amsa mata sapna tayi tace oyoyoo besty kishigo mana, deejah tana daga waje tace bari infara gaisawa da ummanah, dariya sapna tayi tace ai ummah batanan ta je anguwa, Deejah shigowa tayi d’akin takalli sapna da take gaban dressing mirror tace eyye ‘yanmata anata shiri, juyowa sapna tayi takalli deejah da tazuba mata ido, yanayin shigarta takalla kayan sun kamata sosai sai wani d’an siririn mayafi da tayafa wanda da shi k’ara babu, harararta sapna tayi tace waike meyasa bakison sa babban veil ko fa a school ina lura da ke? Ta6e baki deejah tayi tace toh sarkin sa ido kullum sai kin min wa’azin nan toh na gaji babu ruwanki da shigata kabarinki daban nawa daban dan haka kiyi shigarki inyi tawa kowa da kabarinsa alarammiya, murmushi Sapna tayi domin tasan deejah batason afad’a mata gaskiya, tace Allah yashiryeki Deejah, deejah tace Ameen y rabb nidai yisauri kishirya muje, Sapna batace komai ba tacigaba da shirinta bayan ta gama hijab d’inta tasaka iya gwiwa nan deejah tayi ta mata tsiya itadai Sapna shareta tayi ahaka takulle gidan suka tafi gidan kitson da yake bayan layinsu.

Deejah aka fara ma kitson bayan angama sannan aka fara ma Sapna tunda Sapna tabud’e kanta deejah tace masha Allah besty daman ni nakeda gashinki da ba zanyi kitsoba murmushi Sapna tayi tace haka dai kikace ammah ai damunki zai dinga yi, deejah tace ahaka dai nakeso, cikin dabara tasamu tafakaici idonsu tad’auki gashin da aka sharce ma sapna kai yafita, cikin jakkarta tasaka cike da farinciki domin tasan sun kusan cika burinsu, ahaka aka gama musu kitson sapna hana deejah tayi tabiya kud’in ita tabiya musu sannan suka dawo gidansu sapna sukayi sallah suka ci abinci sai wajen k’arfe biyar sannan deejah tayi waya domin azo ad’auketa, ko da akazo d’aukarta sapna har bakin motar tarakata da mamakinta sai taga irin samarin nan ne ‘yan iska nan jikinta yak’ara sanyi da lamarin deejah, deejah ko da talura da yarda sapna tayi domin ko da saurayin yayi mata magana bata kalli inda yakeba, ganin haka yasa deejah tace sapna wannan friend d’ina ne kugaisa, wani mugun kallo sapna tayi mata sannan tace sai anjimanki kigaishe min da mummy, murmushi deejah tayi domin tasan halin k’awartata tace toh shikenan zataji.

Ko da deejah tatafi bata zarce ko inaba sai gidan lubna, cike da murna lubna ta tarbeta nan deejah tabata gashin, cikin jin dad’i lubna ta rungumeta tace nagode k’anwata wlh kin gama min komai kifad’i abinda kikeso inbaki, dariya Deejah tayi tace Aunty lubna wannan friend d’in taku da kukazo bikkin Aunty khaausar da ita nakeso kicusa ni wajenta saboda ta burgeni wlh, dariya lubna tayi tace bakida hankali kina nufin zarah kike nufi? K’awar fa khausar ce, dariya deejah tayi tace toh ai nima Aunty khausar d’in tana bin nawa friends d’in, nidai kitaimaka min wlh tashiga zuciyata, lubna harararta tayi tace aikam sai na fad”a ma amfah idan tadawo watau dan kinga ta yi tafiya shine zakiyi mata haka ko? , dasauri deejah tarik’ota tace dan Allah karki fad”a mata nidai kitaimaka mani, lubna murmushi tayi tace ai dole intaimaka miki kar kidamu koma mi kenan zamuyi waya, har bakin mota Lubna taraka deejah kallon guy d’in da ke cikin motar tayi tace deejah wannan ne Haidar d’inki? Girgiza kai deejah tayi tace a’a haidar d’ina kamiline kuma yana da class dayawa shifa zan aura ai da tare dashi nake da ba zaki ganni da wannan shigarba saboda yana min kallon kamila mutunniyar kirki ammah baisan wacece niba, dariya lubna tayi tace k’anwata idan akwai naira wlh kishige kimori abunki kar kibari yagane, deejah tace dagudu ma Aunty lubna wlh ina sonsa da yawa guy d’in ya yahad’u sosai, daidai lokacin suka isa bakin motar guy d’in nan suka gaisa da lubna sannan sukayi bankwana, ko da deejah tashiga motar guy d’in kallonta yayi yace baby ina zamuje yanzu? Deejah murmushi tayi tare da kashe masa ido d’aya tace muje hotel d’in my dear ai yau muna tare har gobe dasafe saboda mummy night duty takeyi hospital, cikin jin dad’i yace yauwa baby wlh saisa nake k’ara sonki, deejah tace nima ina sonka dayawa babyna.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button