BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Wanshe kare tun da wuri lubna tashirya taje gidan malaminta bayan sun gaisa nan tabud’e jakkarta tad’auko gashin sapna tace toh malam gashi nacika umurninka, dariya malam yayi yace lallai aikinki ya yi kyau, yanzu abinda yarage shine wannan gashin zan ba ma aljani idu domin yayi amfani da shi yashiga cikin kanta ammah alokacin da tashagala batayi addu’a ba sannan kekuma zan baki wani ruwa kiyi wanka dashi sai ga kwallin da zaki shafa yadda da kinje uwarta ba zata ta6a ja da maganarkiba kuma zan kulle bakinta yadda duk inda yarinyar zataje ba zata ta6a tambayarta ina zatajeba barema tahanata, cikin jin dad’i Lubna tace gaskiya malam nagode sosai, murmurshi malam yayi yace sai kuma ga wannan maganin kisan yadda kikayi kika zuba mata a cikin abincinta indai taci toh shikenan aljani idu zai cigaba da kasancewa saman gashinta kuma zata dinga bin duk umurnin da zaki bata ke zata ma iya barin maganar mahaifiyarta tabi taki ammah saidai akwai matsala d’aya, murnar da lubna take tafara komawa ciki tace wace irin matsalace malam? Gyara zamansa yayi yace matsalar kuwa itace ba zamu iya amfani da zuciyar yarinyar nan ba, ammah zamu samo miki soyayyarta ko kad’ance awajenta, kar kikuskura kitilasta ta tasoki dan idan hakan takasance toh zaki aikata babban kuskere, kedai kije kiyi yadda nace miki bayan sati d’aya sai kije gidan nasu, cikin jin dad’i lubna tace nagode sosai malam wlh ka taimaka min nawa zan biya, dariya malam yayi yace wannan aikin Aljani idu ne dan haka yanka kawai zaki bada kud’i ayi masa domin yasha jini, dubu hamsin lubna tazaro ta aje gaban malam tace gashinan asamu rago ayanka, sannan taciro 20,000 tace wannan kuma nakane malam, cikin jin dad’i malam yayi mata godia suka yi sallama kowa yana murna,

Bayan sati d’aya Sapna ce kwance saman gadonta duk sai taji kasala ta kamata gashi lokacin daman period take school ma kasa zuwa tayi a ranar, bayan sallar la’asar sapna kwance take tana chart kawai tajiyo ana sallama har ta bud’e baki zata amsa saitajiyo ummah ta amsa dan haka tashare tacigaba da chart d’inta domin batasan mai muryarba,

Lubna ko da tashigo gidan suna had’a ido da ummah saida gaban ummah yafad’i dakyar tabud’e baki tace sannu da zuwa kishigo aciki, Lubna d’akin ummah tashiga tazauna nan ummah ma tazauna, awulak’ance tagaishe da ummah sannan tace Sapna fa tana nan? jikin ummah yana rawa tace eh tana nan akira maki ita ko zaki shiga kiganta? Yamitsa fuska lubna tayi tace kikiramin ita dai, ummah cikin rawar jiki tatashi tashiga d’akin sapna, da mamaki sapna take kallon ummah, ummah ma kallonta take tace kizo kinyi bak’uwa, sapna tace bak’uwa kuma ummah? Wacece take nemana? Ummah tace ai sai kitaso kiganta, Sapna Tashi tayi tabi bayan ummah ko da suka shiga d’akin itama saida gabanta yafad’i da taga lubna ammah tadake tabbas ta ganeta itace suka had’u wajen bikkin yayar deejah tabbas tasan deejah ce zata gwada mata gidansu fuskar sapna d’auke da mamaki k’arara tagaisheta, cikin sakin fuska lubna ta amsa mata tace sapna kenan ashe ana ganinki? Murmurshi Sapna tayi tace eh, lubna kallon ummah tayi tace ni sunana lubna daman nazone ki aramin Sapna dan Allah domin taraka ni wata anguwa, ummah batare da fargaba ko tsoroba tace toh shikenan ai ba matsalabane kutafi kawai, lubna kallon sapna tayi tace jeki kid’auko mayafinki mutafi, batare da musuba sapna tatafi tad’auko tafito kallon ummah tayi taga babu alamar damuwa atare da ita tace ummah sai mundawo, Murmushi ummah tayi tace toh sapna Allah yakiyaye hanya,

Ko da suka fito lubna motarta tabud’e suka shiga, sapna jingine kanta tayi jikin motar tana jin kanta yana wani irin juya mata dan haka talumshe idonta, kallonta lubna tayi tana murmushi sannan tacigaba da tuk’inta, bata zarce ko’inaba sai gidanta horn tayi ma maigadi yazo yahangame mata gate tunda suka shigo harabar gidan sapna take bin wajen da kallo har lubna tayi parking sannan takalli sapna tace baby kifito mushiga ciki, Sapna batayi gardamaba tabud’e murfin motar tafita, rik’o hannunta lubna tayi suka shiga cikin gidan itadai sapna a tsorace take bata ida tsorataba saida suka shiga main parlour din gidan, matane da maza a zaune kowa da kayan maye a gabansa yana sha kid’a sai tashi yake suna shiga nan idanuwan mutanen suka dawo kansu dasauri wani babban mutum yataso yana tafiya yana tangyad’i daga gani ya sha ya-yi tatul hannunsa rik’e da kwalbar giya yana isowa rungume lubna yayi nan sukasa dariya sannan lubna takar6i kwalbar itama takur6a, kallon sapna yayi da take tsaye bayan lubna duk mamaki ya cikata, sakin lubna yayi yayo wajen sapna yana shirin rungumeta dasauri sapna taja baya tare da wurga masa harara, murmishi lubna tayi tajawo sapna gefenta sannan tace Alhaji naira wannan ba ‘yar hannu bace kabarta kawai, cikin muryar maye yace ammah kuma gaskiya baby ta yi min ki aramin ita, dariya lubna tayi tace haba Alhaji naira me kake ma sauri kabari abi komai a sannu yanzu dai bari inshiga daga ciki, ko da tazo wucewa matan da ke wajen suka zo wajensu lubna sukace sannu da dawowa first lady, dariyar jin dad’i lubna tayi tace yauwa nuna musu sapna tayi tace ga daughter d’ina nan dan haka kukular min da ita, gaba d’yansu sukake wow lubna ina kika samo wannan kyakkyawar yarinyar haka, teemah tace kar dai kice min sapna ce, dariya lubna tayi tace itace mana, cike da mamaki teema tace lubna ya akayi hakan takasance? Murmushi lubna tayi tace kin d’auka ni tawasa ce? Shewa sukasa sukace dagirman kujerarki babbar mace aikinkin yana kyau gaskiya.

Dariya lubna tayi sannan tajawo hannun sapna tabud’e d’akinta suka shiga, saman 3 seater d’in da take d’akin Lubna takaita tazauna, itadai sapna duk atsorace take, zama lubna tayi kusa da ita tana murmushi tace sapna kisaki jikinki mana naga sai wani takurewa kikeyi nan ma ai gidane, sapna murmushi kawai tayi batare da ta ce komai ba, ganin haka yasa lubna tatashi tace bari inkawo miki abun motsa baki, fita lubna tayi tanufi kitchen jalop d’in taliya tazubo tad’auko garin maganin tazuba ciki tamotse sannan tadawo d’akin gaban sapna ta aje sannan taje tabud’e freezer tad’auko ruwa da lemu sai kwalbar giya tazo ta aje gaban sapna tace kici abinci mana, girgiza kai sapna tayi tace na k’oshi, kallonta lubna tayi tace sapna kisaki jikinki ni fa ba cutar dake zanyiba yakamata kisaki jikinki da ni domin ni banzo da niyar cutar da rayuwarkiba sapna dan haka kici abinci, sapna ta bud’e baki zatayi magana kenan lubna tad’aga mata hannu tare da cewa bana son gardama dan haka kici kawai, sapna d’aukar abinci tayi duk yadda taso tayi bismillah ammah saitaji bakinta ya yi mata nauyi dakyar tad’ebo lomar farko takai bakinta saida taji kanta ya sara mata dasauri tadafe kanta takalli lubna ganin yadda tatsareta da ido yasa ahankali tacigaba da cin abincin saida taci kusan rabinsa sannan tature plate d’in tajawo ruwa tasha, Ganin bata ta6a giyarba yasa lubna tatashi tazo tatsiyaya mata a cup tamik’a mata jin warin giyar da tayi yasa tatuno da abinda deejah tabata tasha a school har ya6atar mata da hankali tabbas tasan shine dan haka tak’i kar6a, girgiza kai sapna tayi tace bana shan wannan please karki tirsasa ni insha abinda zai 6atar min da hankali domin ina k’yamar aikata hakan,
Cike da mamaki lubna take kallonta tace sapna kisha ko kad’an ne babu abinda zai faru dake saima dai wata irin rayuwa da zaki shiga wadda ba zakiso kiga kinfita daga cikintaba, murmushin takaici sapna tayi tace daman ashe akwai dad’i acikin sa6a ma Allah? Ni ba haka nakeba dan haka ba zan sha ba, kallonta lubna take fuskarta d’auke da mamaki tace sapna kinsan ko dawa kike magana kuwa? Hawayen bak’in cikine suka zubo daga idon sapna tace aunty lubna shin kinsan girman zunubin mutumin da yake shan kayan maye dan yafita daga cikin hankalinsa kuwa?
‘Daga mata hannu lubna tayi tace kar kiyimin wata nasiha ya isa haka nasan nan gaba dakanki zaki nema kisha, shuru sapna tayi batace komaiba ganin haka yasa lubna tad’aga cup din tashanye sannan tatashi dakyar tad’auki plates d’in tace ma sapna bari indawo, sapna dai kallon ikon Allah take har lubna taficce daga d’akin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button