DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Indai ba comment toh ba zan cigaba ba domin comment d’inku shi yake k’ara mana k’warin gwiwa dan haka muje zuwa my fan’s????
Comment
nd
Share
Sis Nerja’art✍????
????????????????
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
????????????????
(BASE ON TRUE LIFE STORY)
Written By ~ Sis Nerja’art
DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL
INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….✔
Sak’on gaisuwata agareki tahannun dama sharifiya sidi nagode da k’aunarki agareni????
Wannan page din nakine my k’anwa janaf ke tadabance acikin zuciyata????
Page 2⃣3⃣
Lubna tunda tafita tabar sapna a d’akin bata dawoba, sapna kwanciya tayi saman 3 seater din har tsawon 1 hour lubna bata dawoba, ganin har magrib ta gabato yasa sapna tatashi tad’auki jakkarta tafito, ko da tazo parlour tsoro ne yakamata ganin yadda yadda nutanen ciki suketa rayuwarsu da mamakinta take kallon lubna ta yi d’ai-d’aya bisa wani k’ato suna ta shan sholisha, bata ankaraba ta shagala da kallonsu kawai sai ji tayi an rungumota a tsorace sapna ta kalli wanda yarungumota wani nark’ek’en k’atone cikin 6acin rai sapna tad’aga hannu tawankesa da mari tare da janye jikinta, marin da sapna tayi masa ya shigesa da sauri yadafe kuncinsa nan duk hankalin mutanen wajen suka dawo wajensu, dasauri lubna tataso tana tangyad’i kamar zata fad’i nan tawanka ma sapna mari cikin 6acin rai sapna tad’ago kai takalleta cikin d’aga murya lubna tace Sapna har kinkai matsayin da zaki d’aga hannu kimari customer d’ina daga zuwanki yau? Hawaye ne suka fara zuba daga idon sapna tace Aunty lubna shi fane yata6ani, harararta lubna tayi tace dan ya ta6aki shine zaki maresa? Toh wannan yaxama nafarko kuma nak’arshe babu ruwanki da customer d’ina, itadai sapna hawaye kawai takeyi, gani tayi lubna ta rik”e mutumin tana basa hak’uri shi kuma ya yi tsaye kamar gunki, ganin baida niyar yin hak’urin yasa takalli sapna awulak”ance tace kibashi hak’uri, sapna shuru tayi takyaleta, cikin 6acin rai tace nacemiki kibasa hak’uri, Cikin 6acin rai sapna tace Allah yabaka hak’uri dasauri taficce daga d’akin tana goge hawayen fuskarta, ko da tafita daga gidan mai adaidaita tasamu tafad’a masa inda zai kaita, lokacin da ya isa da ita anguwarsu har anfara kiran sallah nan tasallamesa sannan tashiga gida da sallamarta saida tabiya d’akin ummah lokacin ummah tana shirin tayar da sallah cikin sakin fuska ummah tace a’ah sapna har kindawo? Murmurshi sapna tayi tace eh wlh ummah.
Toh ina lubna ko har ta wuce,?
Sapna tace eh tana safkeni tawuce gida, ummah bari inshiga ciki kiya sallarki,
Ummah tace toh shikenan mamana.
Sapna ko da tashiga d’akin wanka tashiga tayo bayan tafito shiryawa tayi cikin kayan bacci sannan tahau gadonta takwanta tare da jawo wayarta tahau chart batafi 5 minutes da fara chart d’inba sai ga kira yashigo wayarta ganin bak’uwar number ce yasa tak’i picking har ta tsinke sannan taci gaba da chart d’in kawai sai ganin number tayi anyo mata magana tana dubawa saigani tayi ance ke har kin isa kibar gidan nan ba da izini na ba?
Sapna tunda taga msg din tagane mai mgn dan haka tashare tacigaba da chart d’inta,
Chan sai ga wani calling d’in ya shigo, saida takusan tsinkewa sannan tayi picking dakyar tayi sallama, daga can 6angaren lubna Cikin fad’a tace ke kin isa kitafi ba da izini na ba? Sapna da tunda tad’aga wayar shirin rashin mutunci tayi jin muryar lubna da tayi yasa takasa cikin kwantar da murya Sapna tace Aunty lubna na ga magrib ta yi saisa natafo ammah kiyi hakuri insha Allahu ba zan k’araba,
Lubna cikin jin dad’i tace toh shikenan baby, ammah fa kin d’aga min hankali,
Shuru Sapna tayi batace komai ba.
Lub jin da tayi Sapna batada niyar yin magana yasa tace Sapna kiyi hak’uri abinda yafaru d’azun, dan Allah kidaina wulak’anta mutane wlh wannan Alhajin da kike gani akwai kaya da ace kinbasa had’in kai da har kyautar mota sai yayi miki,
Takaici yacika Sapna takasa cewa Komai.
Lubna tace gobe kishirya zanzo muje anguwa, Sapna dakyar tabud’e baki tace akwai school fa gobe,
Lubna tace toh shikenan zanzo school ind’aukeki,
Sapna tace to Allah yakaimu, cikin k’osawa da maganar tace Aunty lubna bacci zanyi yanzu.
Numfashi lubna taja tace toh shikenan nidai ba dan na gaji da hirar da ke ba, dafatan dai yanzu andaina fushin da ni.
Sapna cikin k’osawa tace uhm.
Murmushin jin dad’i lubna tayi tace ohk gud nyt baby hv a swt dream,
Sapna dasauri tatsinke wayar saboda firar ta gundureta, kwanciya tayi nan bacci yayi awon gaba da it.
Wanshe kare tunda safe Sapna tatashi tagyara ko’ina tahad’a musu breakfast sannan tayi wanka tashirya cikin less d’inta black nd red colour ta yi kyau sosai ko da ba wata kwalliya tayiba hijab red tasa daidai gwiwa a gurguje tayi breakfast sannan takama hanyar school,
Ko da ta isa mamakine yakamata ganin deejah ta rigata zuwa, har ta zauna mamakine bayyane a fuskarta, dariya deejah tayi tace kina mamakin zuwana dawuri ko Sapna? Itama Sapna dariyar tayi tace ai dole inyi mamaki abun ne naki naga kamar a mafarki, ke daman inaso intambayeki wa yanuna ma Aunty lubna gidanmu,
Cikin mamaki deejah tace gidanku kuma? Toh ya akayi tasani?
Harararta Sapna tayi tace toh ‘yar duniya ai nasan kece, kike wani nema ki wayancemin,
Daidai lokacin lecturer yashigo nan suka maida hankalinsu ga abinda yake koya musu,
Wajen 11 yafita daga class d’in nan su Sapna suma suka fito suka nufi resturent d’in dake cikin skul d’in sannan sukaje Wajen da suka saba zama suka zauna kowa yad’auko takeaway d’insa yaci, bayan sun gama deejah bud’e jakkarta tayi tajanyo robar lemu lacasera tafara sha, kallonta Sapna take fuskanta d’auke da mamaki tace deejah daman har yanzu baki daina shaba? Murmushi deejah tayi tace toh ya zanyi wlh na saba ban iya k’in sha, addu’a zaki cigaba da yimin, cikin jin haushi Sapna tace Allah dai yakyauta, kallonta deejah take tayi dariyar rainin wayau tace kowa ma dai yabari yaga k’arshensa, banza Sapna tayi takyaleta batare da ta k’ara ce mata komaiba, sai Wajen 12 sannan suka koma class, bayan sun fito daga class sauri sapna take tatafi kafin lubna tazo, mamakine yacikata tun daga nesa tahango motar lubna, tsaye tayi takasa cigaba da tafiyar, ganin haka yasa deejah tarik’o mata hannu suka k’arasa wajen motar, zaune take a mazaunin driver fuskarta d’auke da bak’in space atamface jikinta kallabin atamfar kawai tad’aura tabazo kitsonta da yasha attach, deejah ce tace lah Aunty lubna ashe kinzo,? Murmurshi lubna tayi tare da kallon sapna tace eh nazo tafiya da babyna, deejah dariya tayi tace toh shikenan bari nima intafi ga driver d’ina chan yana jirana, kallon sapna tayi da take tsaye ta kasa motsin kirki murmushi deejah tayi tace besty sai Allah ya kaimu,
Banza sapna tayi mata batace komaiba, deejah bata damu da hakanba takalli lubna tace Aunty lubna zan wuce sai na shigo,
Lubna tace ohk sai kin shigon ina nan ina sa ido nasan halinki ganin amfa batanan yasa bakya ma son lek’omu,
Dariya deejah tayi tace ina nan tafe ai sai kun ganni,
Daganan sukayi sallama tawuce, lubna kallon sapna tayi tace kishigo mana, batare da musuba sapna tashigo lubna taba motar wuta direct wani had’ad’en BQ taje nan tayi parking tace ma sapna tafito sushiga,