DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Ko da suka shiga kayane birjit a ciki kallon sapna tayi da taketa kalle-kalle tace kiza6i kayan da kikeso nan domin sonake kema kiwaye kifaso gari baby, shuru sapna tayi batace komai ba ganin haka yasa lubna tarik’o hannunta suka je wajen wasu English wears masu kyau riga da wando tad’aukar mata kala goma sai shirt nd skirt shima kala takwas sai takalma kala goma sai gown kala takwas, ko da sukaje wajen biyan kud’in ta yi mamakin kud’in da lubna takashe, mota suka dawo daga nan suka wuce shagon cosmetic tasiya mata kayan makeup sosai daganan lubna tawuce dasu gidanta itadai sapna iyakarta ido.
Ko da suka isa gidan direct d’akin lubna suka yada zango itadai sapna duk a tsorace take kallonta lubna tayi tace baby bari inkawo miki abinci nasan kinsha yunwa,
Fried rice ce takawo mata wacce tasha had’i sannan tabud’e freezer tad’auko lemu tafakaici idon sapna tazuba wasu k’wayoyi tagirgiza saida taga yakoma kalan lemun sai takulle murfin sannan takawo ma sapna tana murmushi tace baby kici abincin mana keda kika kwaso yunwa, batare da musuba sapna tad’auki abincin dakyar taci kad’an sannan ta aje tasha ruwa, ganin batada niyar shan lemun yasa lubna tace baby kisha lemun mana ko inzo inzuba miki? , girgiza kai sapna tayi tace nak’oshi ne Aunty lubna, tasowa lubna tayi tadawo kusa da ita tazauna sannan tajawo lemun tatsiyaya mata a cup tamik’a mata tace ki amsa kisha sapna kisaki jikinki da ni banason wannan d’ar-d’ar din da kike min kinji ko?
Gyad’a kai sapna tayi alamun eh, murmushi lubna tayi tace yauwa baby toh kar6a kisha, sapna k’in kar6a tayi ta bud’e baki zatayi magana sai gani tayi lubna ta girgiza mata kai alamun kar tace wani abu, ganin haka yasa sapna takar6a domin batason jayayya da lubna, ahankali tad’aga cup d’in tafara sha bata d’agoba saida tashanyesa duka, nan tafara hamma tare da lumshe ido kallon lubna tayi bibiyu dakyar tabud’e baki tace Aunty lubna me kika bani? Dan Allah kar ki cutar da rayuwa. … bata ida fad’a ba nan tafad’a saman lubna bacci yayi awon gaba da ita, cikin jin dad’i lubna tayi dariya tace sapna kenan kin fara zuwa hannu nasan nan gaba ba zaki hanani kankiba, ina tayaki murnar shiga sabuwar rayuwa,
wayarta tajawo takira deejah bugu biyu tad’auka dariya lubna tasa tace deejah k’awarkifa ta fara Zuwa hannu tunda har ta sha k’waya, cike da farin ciki deejah tace ya akayi tasha? Dariya lubna tayi tace yau dasafe nakoma ma malamina yabani wani magani nahad’a da k’waya nazuba mata dan haka itama yanzu zata bi layi,
Cikin jin dad’i deejah tace gaskiya Aunty lubna kingama min komai wlh ina sonki kin iya aiki, dariya lubna tayi tace ai kad’an ma kika gani daga cikin aikina , dariya sukasa gaba d’ayansu sannan sukayi sallama suka kashe wayar.
Lubna gyara ma sapna kwanciyarta tayi sannan tatashi taficce daga d’akin
Sapna bata farkaba sai wajen k’arfe biyar a daddafe tamik’e har lokacin k’wayar bata Ida sakintaba kallon lubna tayi da take kwance da wata saman gado rungume da juna dasauri Sapna tad’auke kai daga kallonsu tatashi tajawo jakkarta tasaka hijab d’inta tace Aunty lubna zan wuce gida saboda ummah tana chan tana jirana, kallonta lubna tayi tace kizauna sai zuwa anjima sai inmaidake batare da Sapna ta ce komaiba takoma tazauna tajawo wayarta tafara dannawa domin batada burin k’ara kallonsu saboda tana k’yamar rayuwar da sukeyi,
Lubna ce tatashi taje tabud’e freezer d’inta tad’auko kwalbar giya tamik’a ma Sapna tace gashi kirage kad’aici, Sapna kallon kwalbar take ammah ta k’i kar6a, ganin haka yasa hankalin lubna yatashi domin tana gani ko maganin bai fara tasiri a wajen Sapna ba, chan sai kuma taga Sapna ta mik’a hannu ta kar6a tabud’e murfin tafara sha, ganin hakan yasa lubna tafara murna tajuya takalli k’awarta da take kwance saman gadon suka sakar ma juna murmushi, Sapna bata aje kwalbarba saida tasha kusan rabinsa sannan ta aje dakyar, ganin haka yasa lubna tazauna gefenta a hankali takai hannu tashafi fuskarta tace baby bari incire miki hijab d’innan kisha iska, janye hannunta Sapna tayi cikin muryar maye tace kidaina ta6ani banaso, nan Sapna tafara lumshe ido takure jikinta tayi waje d’aya nan bacci yayi awon gaba da ita, ganin haka yasa lubna tatashi takoma tacigaba da harkarta.
Sai bayan magrib sannan Sapna tafarka lokacin giyan ta d’an saketa dasauri tad’auki jakkarta ganin lubna ba ta d’akin yasa tafito a parlour ta taddasu su ukku zaune suna fira ganinta yasa duk suka maida hankalinsu agareta, Lubna ce tace baby kin farka? Sapna d’aga mata kai tayi alamun eh sannan tace Aunty lubna gida zanje dare ya yi, lubna tace ohk muje inmaida ki,
Lubna har gida takai Sapna sannan takar6i jakkarta tasaka mata 30k tare da kwalbar giya tamaida takulle, Sapna kar6ar jakkar tayi tashige gida, dasallamarta tashiga daga cikin d’aki tajiyo ummah ta amsa mata dan haka direct d’akin ummah tashiga ummah tace sannu mamana kin dawo? Murmushi Sapna tayi tace eh ummana ya gidan? Ummah tace Alhmdllh, ya wajen lubna, Sapna tace tana nan lafiya lou,
Ummah cikin damuwa tace Sapna kikasance mai jin tsoron ubangijinki kitsare kanki da mutuncinki a duk yanayin da kika samu kanki a kullum nasihar da nake miki kenan, Murmushi Sapna tayi tace toh ummah insha Allahu zan kiyaye nagode sosai, murmushi itama ummah tayi tace Allah yayi miki albarka, jeki kid’auki abincinki kici, Sapna tace toh ummah; mamakine yakamata ganin kamar jiya yau ma ummah bata tambayeta inda tajeba ganin haka itama tabar abun a ranta,
ko da tashiga d’akinta jakkarta ta aje sannan tacire kayan jikinta tashiga wanka bayan ta fito shiryawa tayi cikin kayan bacci kasancewar tana fashin sallah, sannan taje kitchen tad’auko abincinta gudun kar ummah tayi fad’a idan tace ta k’oshi, d’akin ummah takoma tazauna suna fira tad’anci abincin sai wajen 8:30 sannan tayi ma ummah sallama takoma d’akinta, jakkarta tajawo tad’auko wayarta ganin kwalbar giyan yasa tajawo takoma saman gadonta tazauna tabud’e tana sha tana chart saida tasha dayawa sannan tarufe murfin dakyar ta aje saman bedside nan tafara gani bibiyu tana lumshe ido nan ta6ingire wayarta na hannunta bacci yayi awon gaba da ita,
tunda takwanta bata farkaba sai wajen 7am, dasauri tayi wanka tana fitowa lokacin ummah har ta gama had”a mata breakfast cikin sauri tad’an sha sannan taficce daga gidan tanufi schl,
Tun daga ranar Sapna takoma ‘yar k’waya bata iya yin kwana d’aya batare da tasha wani abu da zai 6atar mata da hankaliba har a school yanzu waje suke samu su6oye itada deejah susha abunsu ahaka zasu dawo class suyita bacci, nan karatun Sapna yafara ja baya har lecturers d’insu saida sukai mamaki yadda ayanzu sapna tarage maida hankali duk son karatunta yanzu ba a kullum take zuwa class ba ga final exams d’insu remain 1 month sufara, lubna kullum sai ta biyo school d’in ta d’auki Sapna ta wuce da ita gidanta ammah har lokacin Sapna bata bari lubna ta samu biyan buk’ata daga garetaba, customer’s d’in lubna dadama sunnuna suna son Sapna ammah bata basu had’in kai saboda ita hakan bai gabanta, afili take nuna tana k’yamatarsu,
A lokacin sapna ta ida fahimtar wacece deejah saboda k’azamammiyar rayuwar da take yanzu ba ta shakkar sapna taganta, ta sha kwatanta mata tadaina lesbian ammah kullum amsar da take bata itace tasamu itama tadaina shaye-shaye kafin tafara yi ma wani wa’azi, saidai Sapna tayi shuru saboda batada amsar da zata bata.