DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Bayan wata biyu akasha bikkin deejah duk yadda lubna taso sapna taje ammah tak’i ta yi magiyar har ta gaji ak’arshema sapna da taga lubna na shirin takura mata yasa tad’auke k’afarta daga gidan bata dawoba sai bayan bikkin deejah, a wajensu takejin yadda suke yaba tsarin gidan deejah da mijin da ta aura.
Ahaka sapna tacigaba da tafiyar da rayuwarta duk wani party da club tana raka lubna ammah har alokacin ta kasa bata had’in kai, samarin lubna sau dayawa suna kawo mata farmaki sapna kulle ido take tayi masu rashin mutunci, lubna tun tana masifar ganin sapna bata kulata yasa tafara lallashinta a yanzu tsawon shekara d’aya kenan,
Wannan kenan.
CI GABAN LABARI
Dr Haydar yau ma kamar kullum yana tashi daga aikinsa direct chan kusa da islamiyar da yasaba zuwa yaje yayi parking d’in motarsa a masallaci yashiga yayi sallah, sannan yafito yakoma gefen motarsa yatsaya har saida ‘yan islamiyya suka fara wucewa suna shiga yana binsu da ido ahaka suka gama wucewa sai wajen k’arfe biyar sannan yahak’ura yashiga motarsa cike da takaici, yakife kansa a saman sitiyarin d’in motar cikin d’aga murya yace shikenan na fitar da rai da ke tabbas nasan ba zan ta6a samun ki ba, gani d’aya nayi miki kika shiga rayuwata kitaimaka insake sakaki a idona please, d’ago idanuwansa yayi da suka yi ja sannan yatada motarsa yanufi gida cike da takaicin rashin ganinta da baiyiba tsawon shekara d’aya kenan, tsaki yaja yace dole infitar dake a raina domin sonki yana azabtar da ni, zuciyarshi ce tabashi cewa k’ilama aljanace, murmurshi yayi yace ko aljanace ina sonki baby saboda na yaba da halayyarki, ahaka ya isa gida cike da tunani a ransa.
Yana isa part d’insa yafara shiga saida yayi wanka yashirya sannan yafito yanufi wajen maminsa dasallamarsa yashiga lokacin mami tana zaune saman kujera tana kallon news, cike da fara’a ta amsa ma d’an nata, haydar zuwa yayi yazauna k’asa gefen k’afafuwanta sannan yad’aura kansa asaman cinyarta murmurshi mami tayi tare da shafa kansa tace my son sannu da hanya ya naga ka yamutse ko duk aikin ne? Murmurshi haydar yayi cike da k’aunar mahaifiyar tasa yace mamina wlh gajiya ce kuma na yi missing d’in abincinki, murmurshi mami tayi tace saisa nakeson kayi aure my son kaima kahuta, lumshe ido haydar yayi baice komaiba, ganin haka yasa mami tayi murmurshi domin tasan d’an nata indai zatai masa maganar aure bayaso dan haka tacigaba da cewa zama ba aure ai bai yuwuwa my son, ahankali yad’ago kai yakalleta fuskarsa d’auke da damuwa yace mami ina tsoron matan yanzu kiduba kaga khadija fa aurenmu baifi wata shidda ba ammah ya mutu, mami murmurshi tayi tace kar kadamu my son ai ba duka mata bane suka taru suka zama d’aya kacire wannan tunanin daga ranka inma kana ganin ba zaka iyaba toh ni kabani dama inza6a maka mata cikin ‘ya’yan friends d’ina ko danginmu, dasauri haydar yagirgiza kansa yace a’a mami zan za6a dakaina kidai cigaba da tayani addu’a, mami tace toh shikenan my son tashi kaje kaci lunch d’inka mun ma yi waya da dadynka ya ce next week zai dawo cikin jin dad’i haydar yace kai gaskiya na ji dad’i mami, daman na yi missing d’in daddy, dariya mami tayi tace kafin yadawo kuma kajuya min baya,shima haydar dariya yayi yace aike ta dabance my mami, tace na k’i dad’in bakin naka oya wuce kaje kayi lunch, tashi haydar yayi yanufi dining area yazuba abincinsa yafara ci.
Bayan ya gama d’akinsa yakoma yafad’a saman gado tunanin yarinyar ne yak’ara fad’o masa a rai nan yalumshe idoonsa tun kafin ya auri khadija ya san yakeson yarinyar, tafiya yake a cikin motarsa anutse yake driving suna waya da khadija cike da nishad’i nan recharge card d’insa yak’are cike da takaici yaja tsoki sannan yatsaya yayi parking a wata anguwa abakin wani shago neman recharge card nan yaga yarinyar tana tafiya a nutse sanye take da doguwar hijab lokacin ta taso daga islamiyya zataje gida binta yake da kallo lokacin da yatsaya kar6ar card d’in tuni har ta 6ulle baisan inda tashiga ba, nan yatsaya dube-dube ammah baiganetaba sai ma sauran ‘yan islamiyyar da suke wucewa, haka yahak’ura yashiga motarsa cike da takaici ko ma kiran wayar khadija fasawa yayi ahaka yayi tafiyarsa da tunanin zai k’ara ganinta, abu wasa-wasa ganinta yaimasa wuya har islamiyyar ya je yai ma nalaman kwatancenta ammah basu gane wacce yake nufiba duk wadda aka kira yace ba ita bace, haka yacigaba da zuwa kusa da islamiyyar yayi parking d’in motarsa yafito sai yaga shigar kowa ammah ita bai k’ara sanyata a idonsa ba, girgizasa da yaji anyine yasa yayi firgit yadawo daga kogon tunanin da yafad’a yabud’e idonsa ganin Dr Ahmad ne yasa yatashi zaune, dariya dr Ahmad yayi yace ya dai abokina tun d’azun nashigo na ga ka durmiya cikin tunani ko munyi sabuwar kamu ne ba a fad’a minba, hararasa haydar yayi yace kana tunanin a yanzu zan k’ara aure? Ni fa tsoron mata nake kaduba fa kaga khadija wlh tun daga kanta na sare daga lamarin mata, Ahmad zama yayi kusa da abokin nasa cike da tausayi yace kadaina cewa haka haydar ba duka mata suka taru suka zama d’ayaba kana ganin matata tunda mukayi aure yau kusan shekara biyu kenan babu wata matsala atare da hasinah, ya kamata kaima kacire wannan tunanin kazo kayi aure, numfashi Haydar yaja yace inma zanyi aure toh wannan yarinyar da nabaka labari kawai zan iya aura, dariya Ahmad yayi yace kace dai aljanarka, harararsa haydar yayi sannan yatashi yakunna musu wasan ball suka fara kallo.
Sapna sai gab da magrib sannan ummah tazo tatasheta tace ya ciwon kai d’in ? Cike da tausayin ummanta tace ya yi sauk’i ummah, ummah tace Allah yak’ara Sauk’i kitashi zaune domin magrib ta gabato, Sapna tace toh ummah, ko da ummah tafita Sapna binta tayi da kallo cike da tausayin mahaifiyartata domin ta san a duk ranar da ummah tagano tana shaye-shaye toh bazasu kwashe dakyau ba, tashi tayi tashiga toilet tad’auro Alwallah bayan ta yi sallar magrib zama tayi saman darduma tana tilawa har aka kira isha’i sannan tatashi tagabatar da sallah, d’akin ummah taje sukaci abinci sannan suka hau hira, sai da taga ummah ta fara gyangyad’i sannan tayi mata sallama takoma d’akinta, wanka tashiga tayi bayan ta yi shirin bacci tabud’e wardrobe d’inta tad’auko kwalba biyu ta tutulin da syrup tazuba k’wayoyi a ciki sannan tad’aga kai tashanye duka, ginin d’akin ne taga yana juya mata dakyar tatashi tana tangyad’i tanufi saman gadonta tahau takwanta.
Tun da ummah tazo tatashe tayi sallar asuba adaddafe sannan takoma bacci ko azkhar bata tsaya yi ba sai wajen 10am tafarka gyara d’akinta tayi sannan tashiga wanka bayan ta fito tashirya cikin atamfa riga da skirt yellow colour d’inki ya kar6eta sosai, fitowa tayi gidan fes tagansa yarinyar da take zuwa tana musu aiki ta gyara ko’ina, wucewa tayi tanufi d’akin ummah dasallamarta tashiga lokacin ummah tana zaune tana breakfast, cikin fara’a ta amsa mata kusa da ummah taje tazauna tagaisheta ummah ta amsa tare da tambayarta ciwon kan, murmurshi sapna tayi tace ai ya daina ciwo ummah, ummah dakanta tahad’a mata breakfast d’in tatura mata gabanta nan sapna tad’auka tafara yi.
Bayan sun gama sapna kwashe kayan tayi takai kitchen nan tatarda yarinyar da take musu aiki tana gyaran kayan miya, sapna dakanta tayi musu girki tana ganawa d’akinta tashiga tayi wanka sannan tad’auro alwallah bayan ta fito shiryawa tayi sannan tagabatar da sallar azuhur tana zaune tana lazimi sai ga kiran lubna ya shigo wayarta cikin sauri tayi picking tace hello mummy
Daga d’ayan 6angaren lubna ta ce sapna wai kina ina har yanzu baki shigoba?
Murmurshi sapna tayi tace wlh mummy na tsaya yi ma ummah girkine ammah gani nan zuwa yanzu,
Lubna cikin jin dad’i tace ohk kiyi sauri kizo yanzu please daughter, kashe wayar sapna tayi tacigaba da lazuminta.