BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

More comments more typing✍????

Comment
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Masha Allah my k’anwa janaf ina tayaki murnar kammala novel d’inki mai taken MA’AIKACIN KAMFANI abinda kika fad’a daidai Allah yabada ladar, kurakuren da ke ciki Allah yayafe miki,
Kin wa’azantar sannan kin nishad’antar damu am so happy dear????
More grace to your golding elbow
Keep d fire ???????????? burning dear, Urs Aunty Sis Nerja’art????

Page 2⃣5⃣

Tun daga nesa da yahangota saida gabansa yafad’i domin ya gane itace yarinyar da yake nema tsawon shekara d’aya da tawuce, tabbas fuskarta ba zata ta6a 6oyuwa awajensa ba, cikin sauri yayi parking d’in motarsa a gabatanta, kallonsa sapna tayi cikin tashin hankali saida gabanta yafad’i, shima haydar kallonta yake yana mamakin gidan da yaga tafito da yanayin shigar da take jikinta, Hawayene yaga suna zuba daga idanun sapna tace dan Allah bawan Allah kataimaka min wlh tun d’azun nake nan tsaye ban samu abun hawaba, haydar mamakine ya ida kashesa da yaji yanayin muryarta tabbas ko ba a fad’a ba ya san a buge take, kamar yaja motorsa yayi tafiyarsa yaji ammah kuma sai yakasa cike da takaici yace tashigo, cikin jin dad’i sapna tabud’e motar tashiga, saida tafad’a masa anguwarsu sannan yak’ara tabbatar da itace, tunda suka kama hanya haydar yana lura da ita tana ta goge hawayen fuskarta, wayarta tad’auko tak’ara kiran ummah, cikin kuka tace ummana ganinan zuwa sai muje asibiti meyasa baki fad’amin baki da lafiya ba? Daga chan 6angaren ummah murmurshin k’arfin hali tayi tace sapna kikwantar da hankalinki, sapna cikin kuka tace ummah kekad’ai kika ragemin akan wane dalili hankalina zai kwanta, ummah tsinke wayar tayi saboda wani irin ciwo da taji k’irjinta yana yi,

Sapna ida rud’ewa tayi nan tak’ara sautin kukanta, haydar gudu yake da motar kamar zai tashi sama domin har cikin zuciyarsa yakejin kukan da sapna take,

Ko da suka isa anguwar ita tayi ta masa kwatance har k’ofar gidansu, tun kafin ya ida parking tafito dagudu tashiga gidan, ganin haka yasa haydar yafito daga motarsa yajingina jikinta cike da takaicin halin da yasamu sapna,

Sapna tana shiga d’akin ummah tataddata kwance dafe da k’irji dasauri tanufi inda take taduk’a tana kuka tace sannu ummana please kitaso muje asibiti, ummah dakyar tabud’e baki tace d’auko min hijab d’ina, dagudu sapna taje tad’auko mata hijab d’in tataimaka mata tasanya, sannan ummah tamik’e dakyar tana nishi, sapna tana rik’e da ita suna tafiya ahankali har suka fito gidan, da mamakinta taga haydar bai tafiba, haydar da yake jingine da motarsa ganinsu yasa yayi sauri yabud’e bayan motar sapna tashigar da ummah sannan tadawo tarufe musu gida tabud’e bayan motar tashiga kusa da ummah tana rungume da ita, haydar yaba motar huta cike da tausayin matar cikin minti takwas ya isa Aminu kano Teaching Hospital, tun kan ya ida isa yakira waya, agaban emergency ward yayi parking, cikin sauri wasu nurse sukazo suka kama ummah cikin wani room na musamman wanda sai ma’aikata ko family d’insu suke using da shi, sapna mamakine yakamata ganin inda aka shiga da ummah dan tasan ak’allah sai an cajesu sama da 200k, tana nan tsaye daga waje sai ganin mutumin tayi sanye da lab cute tare da wani sunzo sun shige d’akin ko ba a fad’a ba tasan doctor ne, jingine kanta tayi jikin bango tana jin wani iri a ranta fatanta ummanta tatashi domin itace rufin asirinta, tana nan tsaye tsawon awa d’aya saiga doctor d’in da abokinsa sun fito, cikin sauri sapna tanufi inda suke hankalinta atashe tace doctor ya jikin ummana? Kallo d’aya haydar yayi mata yad’auke kai, dr Ahmad ne yace kikwantar da hankalinki ummanki ta samu sauk’i yanzu haka bacci take, zaki iya shiga ammah kar kitasheta, cikin jin dad’i sapna tagoge hawayen fuskarta tace nagode dr Allah yasaka muku da alkhairi, Dr Ahmad murmurshi yayi yace kigode ma Allah baby,
Cikin jin dad’i Sapna tashige d’akin, tafiya suke Dr Ahmad kallon Dr haydar yayi da fuskarsa take d’aure yace friend ina kasamo wad’annan bayin Allahn? Banza haydar yayi yakyalesa, ganin haka yasa Dr Ahmad yaja bakinsa yayi shuru domin yasan halin abokin nasa.

Sapna tana shiga kusa da ummanta tatsaya tana kallonta cike da tausayin mahaifiyartata, ummah baccinta take hankalinta kwance, sapna toilet tashiga tad’auro alwallah sannan tadawo tad’auki hijab d’in ummah tasaka tatayar da sallar la’asar ko da tagama bata tashi daga saman darduma ba saboda magrib ta gabato, bayan ta yi sallar magrib zaune take saman darduma sai ji tayi anbud’e k’ofar anshigo dasauri tad’aga kai takalli mai shigowar, fuskarsa a d’aure yashigo tare da yin sallama ciki-ciki, sapna amsa masa tayi, kallonta shima yayi yace bata farkaba? Sapna tace eh har yanzu bata farka ba, wajen da ummah take kwance yaje ya aje ledar da take hannunsa sannan yasa mata drip, juyowa yayi yakalli sapna itama kallonsa take kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yajanye idonsa daga kallonta yace ya kamata kidinga kula da ita sosai sannan tarage tunani da sa damuwa a ranta saboda jininta gab yake da yahau, duk abinda kikasan zai tayar mata da hankali toh kigujesa, tunda yace ummah jininta ya kusan hawa sapna tafara kuka cikin kuka tace toh doctor mungode sosai Allah yasaka da alkhairi, haydar baice komai ba yanufi k’ofa zai fita saida yakai bakin k’ofa sannan yajuyo yakalleta yace idan ta farka ga telephone nan sai kikara nurses kishaida masu, cikin kuka sapna tagyad’a masa kai, haydar yafita yamaida k’ofar yarufe, sapna kife kanta tayi saman dardumar tacigaba da kuka ahankali cike da tausayin ummanta, Saida tayi mai isarta sannan taje takuskuro bakinta tazo tatayar da sallar isha’i bayan ta gama takoma kusa da ummanta tazauna cike da tausayinta.

Haydar bai dad’e da fita ba saida wani attender ya shigo hannunsa d’auke da leda babba, gaisawa sukayi da sapna sannan yace ga wannan inji ogah yace akawo miki, kar6a sapna tayi domin ta gane ko wanene ya aiko masu da shi, Godia tayi bayan ya fita bud’e ledar tayi taga takeaway ne guda biyu sai drinks da swan water, bud’e takeaway d’in tayi taga fried rice ce sai k’amshi yake tashi sai alokacin taji tana jin yunwa, nan tafara cin abincin saida taci tak’oshi sannan taje takuskure bakinta tadawo tazauna.

Sai wajen 8:30 sannan ummah tafarka dasauri sapna takira wayar tashaida ma nurse din, nan da nan nurses 2 suka shigo suka dubata saida suka tabbatar da ba abinda yake damunta sannan suka taimaka mata tatashi zaune suka bata abinci taci saida tak’oshi suka bata magani sannan sukabar d’akin suka kira Dr Haydar suka shaida masa sun cika umurninsa.

Haydar yana fita motarsa yashiga tanufi gidansu direct part d’insa yashiga saida yayi wanka yashirya sannan yagabatar da sallar isha’i, bayan ya gama fitowa yayi yatafi d’akin mami ganin tana sallah yasa yafito yanufi dining area yayi serving d’in kansa saida yak’oshi sannan yatashi yakoma bedroom d’in mami yataddata zaune tana addu’a shima gefenta yazauna suka shafa addu’an atare, mami juyowa tayi takallesa tana murmushi tace my son yau ka dad’e baka dawoba dafatan dai lafiya, Haydar shafa kansa yayi yace lafiya lou mami wlh wani aikine yarik’eni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button