BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Abincin da take dafawa takwashe cikin kula sannan tagyara ko’ina, bayan ta gama d’akinta takoma tayi wanka tare da d’auro alwallah saida tayi sallah sannan tashirya cikin material gown blue nd red colour sai tayi rolling da k’aramin veil red colour, handbag dinta tad’auka tazura talamanta su ma dai red ne,

‘Dakin ummah tashiga da sallamarta alokacin ummah tana saman darduma tana tasbihi kallon d’iyartata tayi tana murmurshi sapna ma murmurshi tayi sannan tace ummah munyi waya da Aunty lubna ta ce infad’a miki tana gaisheki da jiki, ummah tace ina amsawa ai jiki ya warware, sapna kwantar da murya tayi tace ummah zanje wajen Aunty lubna tana nemana, ummah tace toh Allah yakiyaye kigaisheta, sapna tace toh zataji.

Lokacin da sapna ta isa gidan a parlour ta tadda su sumy da kwartayensu suna ta sharholiyarsu, ko kallon inda suke batayiba tashiga d’akin lubna, da mamakinta ta tadda lubna kwance saman cinyar Alhaji Naira suna ta soyewarsu, ganinta yasa Alh Naira yawashe baki, sapna d’aure fuska tayi batare da ta matsaba tayi tsaye bakin k’ofar, murmurshi lubna tayi tace kishigo mana baby, sapna tsayuwarta tayi kamar ba da ita take magana ba, ganin hahaka yasa lubna tatashi daga jikin Alh Naira tace Alh katafi kawai yanzu, cikin rashin jin dad’i Alh yace toh sai yaushe zaki nemeni? Murmurshi lubna tayi tace da anjima sai kadawo, cikin jin dad’i yace ammah nan zan kwana ko? Lubna tace eh. Kallon sapna yayi da har lokacin take tsaye sannan yamaida kallonsa wajen Lubna yace sweetheart har yanzu dai kink’i samar min fada wajen sapna wlh ina buk’atarta sosai ko da sau d’ayane ataimaka min zan biya kudi masu tsoka, murmurshi lubna tayi tace dear kak’ara bani lokaci, maida kallonta tayi a wajen sapna da take tsaye tana ta dannar wayarta kamar batama san abinda suke cewaba sannan lubna tace Sapnar ce ta cika Jan aji komai nata tsada garesa kafin asamu, jinjina kai Alhaji yayi yace tabbas naga alamar hakan daga gareta nidai ataimaka min ashawo min kanta domin daga gani za a huta atare da ita, dariya lubna tayi tace shikenan Alhaji kar kadamu, cikin jin dad’i yad’auko kud’i masu yawa ya aje ma lubna yace ga wannan kita6a kafin indawo, cikin jin dad’i lubna tad’auki kud’in tace Allah yasaka da alkhairi Alhajin Allah, saisa duk cikin customers d’ina nafi sonka saboda kafi sakin hannu, dariyar jin dad’i Alhaji yayi yasaka rigarsa yace baby sai na shigo anjima, cikin jin dad’i lubna tace Allah yakawo min kai lafiya, Alhaji cikin jin dad’i yazo wucewa zai fita sapna cikin d’aure fuska tawuce domin tabasa hanya, dasauri Alhaji Naira yarik’o hannunta, juyowa tayi tawurga masa muguwar harara dasauri Alhaji Naira yasakar mata hannu domin wani lokacin tana musu k’warjini hatta ita kanta lubna tana ganin kwarjininta kawai dakewa takeyi, Alhaji Naira fita yayi daga d’akin ganin haka yasa sapna tawuce taje saman kujera tazauna, lubna safkowa tayi daga saman gadon tadawo kujerar da sapna take itama tazauna, kallo d’aya sapna tayi mata tad’auke kai tare da cewa mummy lubna ina wuni? Murmurshi lubna tayi tace lafiya lou baby ya jikin ummah? Sapna tace dasauk’i.
Lubna tace shine baki fad’amin ba ai da naje na ganota.
Murmushi sapna tayi tace kiyi hak’uri mummy lokacin hankalina ba a kwance yakeba ammah yanzu ai ta warke,
Lubna tace Allah yak’ara sauk’i, kina buk’atar wani abu ne?
Ta6e baki sapna tayi tace bana buk’atar komai,
Dariya lubna tayi irin tasu ta ‘yan duniya tace har giya abokiyar hirar taki? Domin naga kamar kinfi son shanta.
Shuru sapna tayi batace komai ba
ganin haka yasa lubna tatashi taje tabud’e freezer tad’auko kwalbar giya mai sanyi takawo ma sapna,
Kar6a sapna tayi ta aje sannan tatashi taje ta kuskuro bakinta tazo tagabatar da sallar la’asar bayan ta gama kwalbar giyar tajawo tafara sha cike da nishad’i sai da tasha tayi tatul sannan ta aje kwalbar, tashi tayi tad’auki kwalbar tana tangyad’i tanufi parlour, su sumy har lokacin suna zaune, saman kujerar da bakowa sapna taje tazauna kowa kallonta yake, cikin muryar maye tace sai kallona kuke ko ku ma zakusha ne? Daidai lokacin lubna tafito daga d’akin kallon sapna tayi tace sapna lafiyarki kuwa? Dariya sapna tayi tace Aunty lubna ko zakisha kema? Cikin mamaki lubna tace miye haka kike sapna?
Dariya sapna tayi tace ina cikin farin ciki yau ku ma kuna farin ciki ko?
Zuwa lubna tayi tarik’ota tace kina cikin hankalinki kuwa?
Murmushi sapna tayi sannan takife kanta saman hannun kujera nan bacci yayi awon gaba da ita,
Ganin haka yasa lubna tayi murmushi tagyara mata kwanciyarta.

Haydar yau tun bayan sallar la’asar daga masallaci gidansu sapna yawuce kai tsaye yashiga gidan saboda yanzu ya zama kamar d’an gida tunda suka gaisa da ummah har suka fara fira ammah baiji ko motsin sapna ba, gashi ba ya jin zai iya tambayar ummah ita, har gab da magrib yaji ta shuru daurewa kawai yake suna fira da ammah chan dai da yaji ba kanta yadaure yace ummah wai ina sapna na ji banji motsintaba, Murmushi ummah tayi tace ai batanan ta je anguwa, Haydar saida gabansa yafad’i jin ance sapna bata nan , ummah tace ammah nasan yanzu zata dawo tunda magrib ta dawo, haka suka cigaba da hira da ummah duk bayan mintina sai haydar ya duba agogon hannunsa ahaka har aka kira sallah yayi alwallah yatafi masallaci Sapna bata dawoba.

A chan 6angaren Sapna sai gab da magrib sannan tafarka daga baccin da take lokacin parlourn ba kowa dakyar tatashi tanufi d’akin lubna lokacin lubna waya take, Sapna jakkarta tad’auka sannan tace mummy zan tafi gida naga magrib ta gabato, lubna tace toh daughter dan Allah gobe kishigo da wuri domin gobe akwai wani club da zamuje, Sapna tace toh mummy Allah yakaimu.

Har lokacin giyar bata ida sakintaba tafito tasamu abun hawa tanufi gida, lokacin da ta isa har angama sallar magrib,

dasallama tashiga gidan lokacin haydar da ummah suna zaune tsakar gida suna hira, saida gaban haydar yafad’i dayaganta tabbas ya san akwai abinda tasha saboda daga ganinta ba ta cikin hayyacinta, isowa tayi tagaishesa bai amsa mataba, bata damuba tace ummah sannu da gida, ummah tace sapna ya naganki haka kamar bakida lafiya, murmurshi sapna tayi tace ummah kaina ne yake ciwo, suna had’a ido da haydar yawurga mata wata mugawar harara tsanarta tagani zallah a idanun haydar, dasauri tad’auke kai daga kallonsa tace ummah bari inshiga inyi Sallah, ummah tace toh sapna daga nan sai kisha d’an paracetamol Allah yasauke, haydar takaicine yacikasa da tausayin ummah ganin matar mutuniyar kirki ammah d’iyarta bata biyo halintaba, ko ya zataji alokacin da tagano d’iyarta tana wannan mugun halin.
Tabbas yanzu ya Ida sarewa da halin lubna cikin ransa yace wata k’ila ma wajen wani k’aton taje, dasauri yajanye tunanin daga ransa…….

Comment
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button