DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Lubna tura sapna tayi tafad’a saman gado tabita hannu takai tanaso tarabata da rigarta, sapna tureta tashiga yi suka dinga kokawa lubna ta yi mamakin yadda takasa raba sapna da rigarta dan haka tace amfah tazo tarik’e mata ita, sapna duk ta fita hayyacinta tana daga kwance so tayi tatashi ammah ta kasa nan tafara kuka tace mummy kar kiyi min haka bana so, lubna da amfah sai dariya suke ganin suna neman yaga mata riga yasa tamik’a hannunta dakyar tad’auko kwalbar giyar da lubna ta aje, takwad’a ma lubna a kai, dasauri lubna ta saketa tare da kwala k’ara, sapna ture amfah tayi daga jikinta dasauri tamik’e tamatsa gefe tajawo wuk’ar da take saman bedside tanuna su da ita cikin kuka tace duk wadda ta matso wlh sai na kasheta, lubna tana dafe da kanta tawuce a zuciye zataje wajen sapna dasauri amfah tarik’ota tace kar kije, lubna shiga tayi fuzgewa tace kibarni inje wlh yau ko ni ko ita saidai mukashe juna, rik’eta amfah tayi sosai tace babu inda zakije lubna, ganin haka yasa lubna tajawo plate na glass da apple d’in yake ciki tawurga ma sapna, bai sameta a ko’inaba sai a saman goshinta, sapna k’ara tasaki tayi taga-taga baya kamar zata fad’i dasauri tacije tatsaya tasaki k’ara jin kanta tayi kamar ya fashe dasauri ta ta6a goshinta sai ga ciwo kafin kace mi sai ga jini yana tsiyaya a fuskarta, k’ara rik’e wuk’ar tayi da hannu d’aya, d’ayan hannun yana saman goshinta ta cize le6e, baya-baya takeyi har tazo wajen k’ofa, dasauri tajuya tacire jam lock d’in tana bud’e k’ofa sai ganin su teemah tayi dasauri tanuna su da wuk’atar tace duk wadda tamatso wlh sai na kasheta cikin k’araji tace kubani hanya! Dasauri duk suka matsa gefe a tsorace, Sapna da gudu tayi hanyar waje, lubna dasauri tafito tana cewa maigadi kar kabarta tafita kakulle k’ofar, kafin maigadi yamik’e daga zaunen da yake saidai ganinta yayi fuuuu ta wuce saida yatsorata daga yanayin yadda yaga tana gudun.
Sapna gudu take sosai batasan inda take jefa k’afartaba har saida tazo bakin titi,
Fahad tafiya yake a motarsa zai koma gida bayan ya biya anguwar su wani abokinsa ya safkesa kawai sai ganin mutum yayi saman titi cikin sauri yataka burki, da mamakinsa Sapna ce take tafiya taga-taga kamar zata fad’i kallonta kawai zakayi kad’auka mahaukaciyace k’afarta ba takalma gashinta duk a baje yake, fuskarta duk jini dasauri haydar yabud’e motarsa yafito yanufi inda take yace sapna lafiyarki? Sapna cikin kuka tafad’a jikinsa tace yaya haydar duba kaga yadda suka maidani, so suke sulalata min rayuwa, dan Allah kad’aukeni daga nan kasheni zasuyi, haydar janyeta yayi daga jikinsa cikin tashin hankali yace sapna suwaye zasu kasheki? Wa yaji miki ciwo? Sapna lumshe idanuwanta tafara yi, haydar tallabo fuskarta yayi yana kallonta cikin ido yace kifad’a min wa yayi miki haka? Dakyar sapna tace su lub na… baya tayi kamar zata fad’i dasauri haydar yatallabota tafad’o jikinsa, kallonsa sapna tayi sannan tamaida idonta takulle alamun bacci, haydar rikicewa yayi yad’auketa kamar jaririya yanufi motarsa da ita yabud’e yasakata baya yayi mata dressing d’in ciwon da yake a goshinta sannan yanad’e da bandage, sapna baccinta kawai take batasan ma me yakeyiba.
Haydar fitowa yayi yakoma gaba yatada motar dagudu yaja motar, maganganun sapna ne suke masa yawo a cikin k’walwarsa saida yaje gaban wani shago yayi parking yashiga yasiya mata takalma da hijab ko da yadawo da mamakinsa har lokacin sapna bata farkaba dan haka yawuce resturent yayo musu takeaway sannan yatada motar yatafi saida yakusa zuwa anguwarsu sapna sannan yasamu waje yayi parking ta mirror yakalleta yaga har lokacin bacci take dan haka yad’auki takeaway d’insa yafara ci cike da takaicin halin da sapna tajefa kanta, dakyar yad’anci kad’an duk yunwar da yakeji saima yaji tatafi dan haka aje abincin yayi, yajuya yaga har lokacin bacci take kuma ya san shaye-shaye da tayine yasata bacci, tsaki yaja tare da kife kansa a steering yana tunanin yanayin da yaga sapna cikin ransa yace daman ban taimaka mataba watak’il ma wajen yawon bin mazanta akayi mata haka, tsaki yaja nan yaji tsanarta ta k’ara kamasa ahankali yace albarkacin mahaifiyarki kikaci dan haka zan jira kifarka sai inkaiki gida saboda kar hankalin ummanki yatashi.
Ummah bayan ta gama sallar la’asar sai ga mai wankinsu ya zo d’aukar wanki bayan sun gaisa tace aini nawa wankin bai taruba saidai na sapna ammah bari inkirata waya inji idan ta had’a nata, ummah tana kiran wayar sapna sai jin k’ararta tayi a d’akin sapna, tace oh ashe ma nan tabar wayartata bari dai indubo inga idan ta had’a inkuma bata had’aba toh saidai gobe kadawo, ummah tana shiga d’akin sapna direct wajen wardrobe d’inta tanufa domin ta san gefe d’aya taware tana sa kayan wankinta, tana bud’e wardrobe d’in dasauri taja baya cike da tashin hankali take kallon abunda tagani a ciki, murza idonta tashiga yi domin taga ko mafarkine take ammah ina azahirine kwallah ce tacika idon ummah ahankali takai hannu tad’auko kwalaben cike da mamaki tafara kokwanto me sapna take da kwalbar giya kar dai ace d’iyarta shaye-shaye take? Gaban ummah ne yashiga dukan ukku-ukku kwalaben tad’auko tafito daga d’akin, cikin tashin hankali takalli mai wankin tace yatafi kawai babu wanki, ummah zama tayi k’asa hankalinta a tashe tace na shiga ukku kar dai ace sapna shaye-shaye take dagaske, tunowa tayi da yanayin da take yawan ganin sapna hawayene suka fara zuba daga idanun ummah tace kaicona da wannan rayuwar, nan ummah tafara kuka.
Haydar firgit yayi yajuyo yakalli sapna saboda wata irin k’ara da tasaki, idanuwanta a rufe suke tana girgiza kai tana cewa meyasa kukeson lalata min rayuwa me nayi muku? Wlh sai na kasheku wuf tayi tatashi daga kwancen da take tashiga kiciniyar bud’e k’ofa, Haydar tsawa yadaka mata yace ke me kikeyine haka? Bakida hankali?
Sapna cikin kuka tace kabud’e min infita, Haydar tada motarsa yayi yanufi gidansu sapna yana isa tun kan ya ida yin parking tabud’e motar tafito dagudu tashiga gida turus tayi tatsaya lokacin da tahango ummah zaune a k’asa tana kuka, sapna bata lura da kwalbar giyan da suke gaban ummah ba dasauri tanufi inda take cikin tashin hankali tatsugunna tace ummana wa yata6amin ke? Wanene yasamin ke kuka?
Ummah d’ago kai tayi tawurga ma sapna wata muguwar harara har saida sapna tatsorata numfashinta yakusa d’aukewa……
Nima dai na tsorata dagudu nafece daga gidan????????♀
Comment
nd
Share
Sis Nerja’art✍????
????????????????
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
????????????????
(BASE ON TRUE LIFE STORY)
Written By ~ Sis Nerja’art
DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL
INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….✔
Wannan page d’in nabaki shi a kyauta kiyi yarda kikeso da shi sis Izzat????????
Page 2⃣8⃣
Tureta ummah tayi tamik’e tsaye, dasauri itama sapna tamik’e tana kallon ummanta cike da mamaki tace ummah lafiya? Tun kafin ta ida rufe baki ummah tad’auketa da mari saida tayi mata mari hud’u lafiyayyu cikin 6acin rai tace kifita kibarmin gida sapna na yafeki ashe daman kalar rayuwar da kike kenan? Daman Shaye-shaye kike ke ‘yar iska ce ban saniba? Toh wlh yau sai kinbar min gida.