DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Sai kekuma a matsayinki na mahaifiyarta kuskuren da kikayi shine baki damu da yanayin rayuwar da d’iyarki take cikiba kina mata kallon ke kin bata tarbiya maikyau saidai abinda baki saniba shine kina nan kina gini wasu suna chan suna ruguje miki domin a yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba saboda su ‘ya’ya sai Allah ya tambayemu game da kiwonsu da yabamu, abokan banza sune suke silar 6ata yaranmu saisa anaso mudinga sa ido akan ‘ya’yanmu ko yaya mukaga wani abu ya fara canzawa daga yanayin tarbiyar da muka basu sai muyi sauri mumaidosu akan hanya dan haka wannan ya kamata yazama k’alu bale agaremu
sai maganar nagani kuma idan naje gida akwai magungunan da zan had’a muku wanda zaku dinga amfani da su domin kusamu kunisanta daga sharrin wad’ancan mugayen mutanen, musamman ma ke sapna da aikinsu yafi tasiri a kanki, sai kinkai zuciyarki nesa kin nisantar da kanki daga wannan mummunar rayuwar da aka jefaki a ciki, kicigaba da istigfari kina neman kusanci ga Allah, domin Allah baya kama bawansa da laifin da ya aikata ba a saneba,
Insha Allahu zuwa gobe zan ba haydar yakawo muku, Allah yasa mudace
Sapna da ummah kuka kawai suke hatta shi kansa haydar jikinsa ya yi sanyi, Cikin kuka ummah tace mungode sosai malam Allah yasaka da alkhairi tabbas yanzu na gano kuskuren da nayi wajen rashin sa ido akan yanayin yadda sapna take tafiyar da rayuwarta kekuma sapna wannan yazama ishara a gareki domin DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA SHI RUWA KAN DOKA kinga ke mai abokiya kina neman gyara mata rayuwa sai gashi ta ruguza miki taki ta yi miki tabon da bazai ta6a 6acewa ba,
Sapna cikin kuka tace ummah kiyafe min insha Allahu ba zan k’araba domin ankoya min darasi a yanzu nasan mecece rayuwa insha Allahu zan kai zuciyata nesa wajen ganin na nisanta daga wannan halin addu’anku kawai nake buk’ata ummana, shafa kanta ummah tayi tace a kullum kina a cikin addu’ana saidai zan cigaba insha Allahu, Allah yakare mun ke.
Malam yace toh masha Allah, Allah yasa mudace yanzu dai bari intafi infara tanadar muku maganin, su ummah godia sukayi ma malam sosai suna kuka sannan haydar yaje yaraka malam tare da yi masa godia.
Ko da yadawo har lokacin ummah da sapna kuka suke, zama yayi gefen ummah cike da tausayinta ta yace ummah dan Allah kidaina kuka kugodema Allah da gaskiya ta bayyana sai dai acigaba da addu’a Allah yakiyaye gaba, ummah cikin kuka tace haydar nagode sosai Allah yasaka da alkhairi wlh ka cancanci a yaba maka domin ka cetomu a lokacin da muka fad’a cikin bak’in duhu Allah yasaka da alkhairi Allah yabada lada,
Haydar murmushi yayi yace bakomai ummah ai ke mahaifiyace a gareni duk abinda na aikata agareki kin cancanci hakan, sapna ma godia tayi masa sannan tatashi dakyar tana fara takawa dasauri tadafe kanta tare da furta wash, haydar a rud’e yakalleta yace me yasameki sapna?
Cize le6enta tayi tace bakomai kaina ne yake ciwo.
Haydar cikin tashin hankali yace sannu ko akama miki?
Murmushi tayi tace a’a zan iya, har tashige d’akinta haydar yana kallonta, chan kuma ko mai yatuno takaici yakamasa kallon ummah yayi da takafesa da ido sai kuma yaji kunya ta kamasa yasosa kai sannan yace ummah bari intafi gida, ummah tace toh haydar Allah yakiyaye hanya mungode sosai, har ya juya zai tafi sai kuma yajuyo yace ammah ummah kurufe gidan saboda wad’annan mutanen, ummah tace toh ai yanzu ma so nake intura sapna chan gidan kawunta tazauna chan, haydar yace ai ba sai ta je ko’inaba zan sa wad’anda zasu kula da ku dan har na yi reporting anbani police wad’anda zasu zauna k’ofar gidan nan, cikin jin dad’i ummah tace toh
mungode sosai Allah yasaka da alkhairi
Sapna ko da tashiga d’akinta saida tayi wanka sannan tad’auro alwallah tayi sallar la’asar ta dad’e saman darduma tana addu’a na neman tsarin Allah daga sharrin su lubna.
Haydar ko da yakama hanya dakyar yamaida kansa gida saboda abubuwan da suka farune suka dinga yi masa yawo a k’walwa, ko da ya isa d’akin maminsa yashiga suka d’an ta6a hira sannan yatashi yayo alwallah yatafi masallaci domin yayi sallar magrib;
Bayan ya dawo ji yayi hankalinsa bai kwanta da zamansa ba dan haka motarsa yashiga yanufi gidan ummah…..
Comment
nd
Share
Sis Nerja’art✍????
????????????????
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
????????????????
(BASE ON TRUE LIFE STORY)
Written By ~ Sis Nerja’art
DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL
INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….✔
Page 2⃣9⃣
Lubna tunda sapna tafita ta so tabita ammah su teemah suka hanata cikin jin haushi takoma d’akinta, amfah binta tayi tace kikwantar da hankalinki indai sapna ce kamar kin sameta domin kinsan bazata iya kufce ma tarkonmu ba ko kinmance da aikin da malam yayi miki kanta?
Lubna cike da takaici tagirgiza kai tace bana tunani a yanzu asirin zai cigaba da tasiri saboda malam ya fad’amin idan har nasaki na tursasata tayi dole toh zata iya dawowa cikin hankalinta,
Amfah tace ammah ai batayiba gaskiya a yanzu bana tunanin ta dawo hayyacinta yanzu yadda za’ayi kisaki ranki kidanne damuwarki muje mubata hak’uri idan ta yarda ta dawo toh komai zamu iya yi ni zanma kaiki wajen malamina shima ba bayaba wajen cika aiki.
Lubna saboda jin dad’i neman damuwarta tayi tarasa tace gaskiya k”awata naji dad’i da wannan shawarartaki yanzu dai taso muje gidan nasu, amfah tace a”a lubna ba haka yakamata ayiba kyau dai mufara zuwa chemist ayi miki dressing a ciwon da yake Saman goshinki inyaso daga baya sai muje idan nasu tunda kince mahaifiyarta ma tana k’ark’ashin aikinki,
Dariya lubna tayi irin ta ‘yan duniya tace yanzu dai muje muyi wanka inyaso daga baya sai muje chemist d’in tunda naga jinin ya tsaya, daga chan kuma sai mu wuce gidansu sapna dan ba zan barotaba sai naga ta hak’ura inma naga komai ya zo dasauk’i sai mutafo da ita bayan kwana biyu sai incika aiki, amfah shewa tayi tare da mik’ama lubna hannu suka kashe tace agaisheki agogo sarkin cika aiki wlh na ma hango nasara atare da ke, yanzu dai muje muyi wankar sai mutafi dan naga har magrib ta yi.
Sapna ko da tagama sallar la’asar bata tashiba saboda lokacin baifi 30 minutes ba akira sallar magrib dan haka tad’auko Alqur’ani takaranta tunda tafara da mamakinta bataji wata kasala ko ciwon kai ba kasancewar mafi akasari idan zata karanta Alqur’ani sai ta yi dagaske take samu takaranta rubi’i d’aya ammah yau sai gashi ta karanta kusan izif d’aya.
Saida aka kira magrib sannan tarufe tayi addu’a sai tatashi tagabatar da sallah,
Haydar lokacin da ya iso anguwar da mamakinsa yahango motarsu lubna chan gaba da layinsu sapna kad’an tabbas yasan police d’in da suka gani ne yasa suka kasa k’arasawa gidan, tsaki yaja yace kai wad’annan mutanen anyi ‘yan iska wato har gida suka biyota Allah dai yakyauta, daidai lokacin ya isa k’ofar gidansu sapna yakalli police din da suke wajen yace kar susaki subar wad’anchan nacikin motar sushiga gidan, sukace toh angama ranka yadad’e.
Lubna tun da suka hango police a k’ofar gidan suka parka motarsu daga chan nesa da su, Lubna tace amfah anya wad’anchan police d’in na lafiya ne? me sukeyi a k’ofar gidansu sapna? Amfah dogon numfashi taja tace nima amsar da nake nema kenan, Daidai lokacin sukaga wucewar motar haydar nan suka bita kallo amfah tace gaskiya k’awata akwai kaya ga mai motarnan da alama, lubna tace gaskiya kam dan ni har na hango ya tayani, dariya amfah tayi tace lallai k’awata bakida dama, ganin ya faka a k’ofar gidansu sapna duk sai mamaki yakamasu sukasa ido suga ko wanene ammah har yafito basu ga fuskarsaba ya juya baya yana magana da police ko da yagama batare da ya juyoba yashige gida, lubna dogon numfashi taja tare da jingine kanta saman sit d’in da take tace k’awata wlh guy d’inchan ko da ban ga fuskarsaba ya tafi da imanina da alama zani huta sosai idan nasamesa, amfah tace ba keba wlh nima ya burgeni abun mamaki ko me yazoyi gidansu sapna? Ko dai yayantane? Lubna tace kai bana tunanin tana da yaya domin deejah kamar ita kad’ai ce tace mana, dariya amfah tayi tace toh ko itama irin na deejah tayi mana kinsan itama bamusan wanda ta auraba sai ranar bikki muka gansa, lubna tace shegiyar gora wai ma yanzu tana ina? Ta6e baki amfah tayi tace tana kd, yanzu dai ja motar mutafi mun dawo wani lokacin,