BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Haydar bayan sun gaisa da ummah nan ummah tak’ara yi masa godia yace bakomai ummah ai anzama d’aya, ganin har lokacin ummah hankalinta bai ida kwanciyaba yasa yadinga kwantar mata da hankali har sai da yaga ta saki jikinta nan sukasha firarsu sai wajen k’arfe tara yabar gidan.

Tun daga ranar sapna saida takai Zuciyarta nesa taduk’ufa da addu’a sannan tasamu tadaina shaye-shaye wani lokacin sai ta ji kamar taje tasiyo giya tasha sai kuma taji tsoron had’uwarta da ubangijinta sai taita istigfari, saidai kuma har yanzu tana shan tabs saboda feelings d’in da takeji kuma ba ta ji zata iya fad’a ma ummah.

Duk sim din wayarta ta cire ta aje wayar gaba d’ayanta gudun kar ma su lubna sukirata,
Lubna kusan kullum sai ta zo anguwar ammah ganin police k’ofar gidansu sapna yake hanata shiga har daga baya tagaji tadaina zuwa, bayan sati d’aya haydar yasallami police d’in suka tafi, sapna ko nan da k’ofar gida tadaina lek’awa.

Yau ma sapna kwance take saman gadonta yanayin yadda tafara jin jikinta yasa tatashi tanufi wardrobe d’inta domin tad’auko tabs d’inta tasha tana dubawa sai taga ya k’are dafe kanta tayi cikin rashin jin dad’i sannan takoma saman gadonta takwanta nan tayi ta juyi, tsaki taja tace daman ace mutum yana da tsayayyen saurayi ai da na yi aure na huta da wannan jarabar, ganin abun baida niyar lafa mata yasa tafara tunanin mafita domin tanaso taje tasiyo tabs d’in dabarace tafad’o mata dan haka tatashi tad’auko hijab inta tasaka tanufi d’akin ummah tana addu’an Allah yasa ta amince, dasallamarta tashiga tanufi inda ummah take tazauna, ummah kallonta take tana murmurshi tace mamana ina zakije?
Itama sapna murmurshi tayi tace ummah dan Allah so nake inje gidan Kawu sani mugaisa, murmurshi ummah tayi tace ya dai kamata kije domin suna ta min complain akan rashin zuwanki ya kamata kirik’e zumunci domin zumunci shi yake kaiwa Aljannah nidai har ga Allah ban hanaki zumunci da d’an uwan abbankiba, tashi kije Allah yayi miki albarka kigaishesu, Sapna tace Ameen y rabb nagode sosai ummah insha Allahu zan gyara, sapna har ta tashi ta fara tafiya sai ji tayi ummah ta ce sapna zo, juyowa sapna tayi tadawo tazauna ummah kallonta tayi tace sapna na gaji da zamanki gida hakanan babu aure dan Allah kidaina wulak’anta samari kisamu kifitar da d’aya ki aura domin aure shine mutuncin mace, sapna jikinta yayi sanyi tace toh ummah insha Allahu zanyi ammah har yanzu banga wanda yakwanta min ba, ummah tace ai dan baki tsayawa kisauraresu saisa bakiga wanda yayi mikiba, murmurshi sapna tayi tace zan gyara ummah, ummah tace ke dai kika sani,

Sapna ko da tafita saida tafara biyawa gidan kawu sani da yake bayan layinsu, ammah cikin rashin sa’a taga gidan a rufe alamun basunan dan haka kawai sai tawuce chemist domin tasiyo tabs d’in,

bayan ta siyo akan hanyarta takomawa gida sai ganin mota tayi ta yi parking gabanta damamakinta tad’ago kai saida gabanta yafad’i tatsorata da ganin lubna, tsaye tayi takasa motsawa, lubna bud’e motar tayi ahankali tataka taje inda sapna take tsaye murmushi tasakarmata tace baby kinyi mamakin ganina ko? Wlh nakasa daurewane shine nazo inbaki hak’uri akan abinda yafaru Wlh bazan k’araba dan Allah kidawo mucigaba da zamanmu yarda muke a da, sapna tsoro taji kar wani yaganta da ita dan haka wucewa tayi zata tafi dasauri lubna tajawota tace haba sapna minene haka nida nazo inbaki hak’uri kuma sai kimin wulak’anci?
Sapna tace Aunty lubna kisakeni intafi gida abinda dai kikesone bazaki samu daga gareniba, Lubna tace haba sapna miyayi zafi haka, dan Allah kimance da abinda yafaru, sapna cikin k’osawa da maganar tace toh na ji na hak’ura yanzu dai sakarni inje gida, lubna tace toh muje inrakaki, sapna tace a’a kibarshi kawai yanzu dai bari intafi inyaso munyi waya, lubna tace haba dear wayarki fa ina kira ammah kashe take, sapna tace eh ammah zan kunnata yanzu dai kitafi, lubna kashe mata ido d’aya tayi tace baby ya naga kamar kina guduna yanzu? Sapna ta6e baki tayi tace ni ba gudunki nakeba koma dai minene zamuyi waya, lubna murmushi tayi tace as u wish dear, bye sai munyi waya, sapna saida taga tafiyar lubna sannan taja tsaki juyowar da zatayi tacigaba da tafiya saida gabanta yafad’i cike da tsoro take kallon haydar da yake tsaye k’ofar gidansu ya kafeta da ido, dakyar taja k’afarta tatafi har taje zata shige gida kawai sai ji tayi haydar ya jawota tafad’o jikinsa, da mamaki tad’ago kai takallesa shima kallonta yake cikin 6acin rai idanuwansa sun kad’a sunyi jawur yana hucci yace daga gidan ubanwa kike? Daman iskancin naki yana nan har yanzu ko? Daman nasan dakyar kibar wannan mummunar d’abi’ar taki, cikin d’aga murya tace enough haydar, enough!!! Kar kasaki kanemi kaci min mutunci kawai daga ka ganni da ita shikenan sai kanemi kazargeni, cikin 6acin rai haydar yace abinda nagani da idona dashi zanyi amfani, kiciniyar kwace kanta tashiga yi tace ni kasakeni na je na yi, tureta yayi har takusan fad’uwa cikin 6acin rai yace daman mai hali ba zai ta6a barin halinsaba, cike da 6acin rai sapna tace baidai kamataba kashiga harkar da bata damekaba inkuma kaima kanaso katayane toh bismillah ai abun kasuwanci ne, mari haydar yazabga mata, cikin sauri sapna tadafe k’uncinta tace ni kamara? A harzuk’e haydar yace na mareki karuwar banza ke ko neman matan nake kina tunanin zan nemi irinki banza ai bakida abinda zan so a jikinki, tureta yayi yawuce yashige gidan, sapna takaici ya Ida kasheta maganganun haydar sunyi mata ciwo share hawayenta tayi tashiga gida, 6oye damuwarta tayi tashiga d’akin ummah lokacin suna gaisawa da haydar, ummah tace a’ah sapna har kin dawo? Murmushi tayi tace eh ummah na ma je basunan saisa nadawo dasauri tawuce taficce daga d’akin, murmushi ummah tayi tabita da kallo har taficce sannan tamaida kallonta ga haydar da shima yatsareta da ido tace haydar a rayuwata inaso inga sapna ta yi aure ammah ta k’i tasaurari samarin
Bare har tafitar da miji cikinsu wlh hankalina baya kwanciya inga sapna tana yawo ba aure more especially ma yanzu da wannan abun yafaru, murmushi haydar yayi yace ai sai hak’uri ummah kuma aure lokacine, ummah cikin takaici tace haydar ba zaka ganeba a da ina da burin inbaka sapna ka aura saboda na yarda da tarbiyarka ina da buri sapna ta auri miji irinka wanda zai kula da ita a matsayinta na maraini wlh nasan ko bayan mutuwata zaka kularmin da ita ammah yanzu kash hakan ba zai ta6a yuwuwa ba saboda yanzu ka fi k’arfinta inma na baka ita toh na cuceka, saboda sapna tun a saman titi ta saida mutuncinta inma ba sa’a ba bana tunanin akwai wanda zai aureta a haka,

haydar da tunda ummah tafara maganar yakafeta da ido yana mata kallon mamaki, tausayin matarne yaji ya kamasa ganin yadda take zubar da hawaye ahankali yabud’e baki yace ummah saboda mi kike tunanin hakan ba zai yuwuba? Sapna ko ba komai k’anwatace kuma kina da ikon kikawo wata tadaban wacce ba sapna ba in aura bare sapna jininki, wlh na kar6i sapna zan aureta zan zauna da ita tsakani ga Allah, ko da a da nata6a aure K’ADDARA CE tarabani da matata ban ta6a tunanin zanyi aure dawuriba ammah yanzu insha Allahu zan auri sapna, ummah cikin kuka tace a’a haydar wlh idan nabaka sapna ban maka adalciba domin sapna ba mutuniyar kirki bace, murmurshi haydar ysyi yace kar kidamu ummah insha Allahu very soon zan turo magabatana ayi maganar auren, ummah cikin Jin dad’i tace nagode sosai haydar Allah yasaka da alkhairi wlh kataimaka mata Allah yabiyaka kaida iyayenka yadda kataimakemu kaima Allah yataimakeka, haydar yace bakomai ummah kar kidamu koma dai minene zamuyi magana, bari intashi intafi naga magrib ta gabato, ummah tace toh mungode Allah yasaka da alkhairi, haydar ko da yafito d’akin sapna yatura da mamakinsa k’ofar a bud’e take, yana shiga lokacin sapna tana zaune saman gadonta ta dafe kanta, jin anbud’e k’ofar yasa tad’ago kai ganin haydarne yasa tabisa da kallo fuskarta d’auke da mamaki, shigowa yayi fuskarsa d’auke da murmurshi yace sannu ko ‘yan mata ina tayaki murna zaki shiga gidan Haydar a matsayinki na wacce tayi kwantai tarasa maiso kokuma ince ballagaza, sapna cikin 6acin rai tace ya isa haka haydar inma kana tunanin zan aureka toh wlh kadaina domin ni nafi k’arfinka na wuce ajinka, dan haka kafitar min daga d’aki, harararta yayi yace ke kina tunanin zan soki? Toh bari kiji sadakarki aka bani dan haka kitanadi maganin hawan jini da na ciwon zuciya ki aje wannan shawarace nabaki dan haka sai anjimanki……..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button