DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Nagode sosai wlh ina jin dad’in comments d’inku masu yi a group, da masu bina ta pc har ma masu kirana a waya nagode domin comments d’inku shi yake k’aramin k’warin gwiwa nagode masoya Allah yabarmu tare????????
Page 5⃣➖6⃣
Tana gama sallah addu’a tashiga yi tana mai k’as-k’antar da kanta a kullum burinta Allah yabata ikon gyara rayuwarta ita kanta tana k’yamar rayuwar da takeyi kuma ta rasa dalilin da yasa takasa dainawa a ko wane lokaci tafara wannan tunanin sai taji kanta yana mata ciwo, ta dad’e tana addu’a sannan tatashi lokacin mummy lubna ba ta d’akin.
Hijab d’in tacire tad’auki bak’in gyalen tayi rolling masha Allah abu ga kyakkyawar mace fara nan da nan kyanta yak’ara fitowa.
Turare tafeshe jikinta dashi sannan tasaka takalminta hills bak’ak’e bata d’au komai ba sai wayarta.
Falo tafito ta tadda mummy lubna da sumy zaune suna fira.
Binta sukayi da kallo sukace masha Allah gaskiya sapna kinyi kyau sai kace zaki gasar sarauniyar kyau,
Murmushi tayi masu tace nagode.
Mummy lubna tace kizauna sapna kafin Alh surajo yazo na kirasane shi zai kaimu saboda kinga motata tana wajen gyara.
6ata fuska tayi domin ita tun lokacin da Alhaji zubairu yanemi yabiya buk’atarsa da ita tak’i taji duk ta tsanesa, ahankali tace mummy toh maimakon mushiga napep?
No na fison akaimu.
Ammah kuma mummy…..
Ix ohk sapna!!! Banason gardama kin sani,
Cinyeki Alh zubairun yace zaiyi? Na lura duk lokacin da nace shi zai kaimu anguwa toh sai kinja raina ya 6aci.
Kallonta tayi taga yadda Sapna tayi da fuska kamar zatayi kuka,
Tasowa tayi tajawota tazaunar da ita kusa da ita tace sapna tunda dai har kikace bakiyi wlh ba zan miki doleba kuma babu Wanda ya isa yayi maki dole kikwantar da hankalinki kinji ko?
Toh mummy
Yauwa gud gurl.
Dariya sumy tayi tace lubna gaskiya sapna ta cika tsoro dayawa nima fa kaina tsorona take ji.
Murmushi lubna tayi tace ai dole taji tsoronki sumy na fa san halinki, toh wlh baya-baya keda sapna tunda bata so kikyaleta.
Kinjiki kekuma da wani zance.
Nidai na fad’a maki dai na san halinki sarai…
Dai-dai lokacin wayar lubna tafara ruri, ganin wanda yakira yasa tayi Murmushi tace ina tunanin ya iso sapna taso mutafi.
Sumy idan humairah ta zo pls kice mata na fita kar tajirani tatafi kawai.
Dariya sumy tayi tace au kice yau ba a muradin humairah.
Batare da ta bata amsaba tafice daga d”akin sapna tana biye da ita a baya.
Wajen motar Alh zubairu suka nufa sapna tad’aure fuska tare da bud’e bayan motor tashiga.
Lubna tabud’e gaban motar tashiga tana Murmushi irin nasu na ‘yan duniya tace Alhajin mai rabo sannu da hanya.
Yauwa my baby ganinki fa yana wahala.
Haba Alhaji saidai idan ba a so ganinmu ba,
Hakadai kikace Ammah kema kinsan sai kinso ganin mutum ake ganinki.
Ta glass d’in motar yakallo sapna yaga ta yi kichin-kichin da fuska Murmushi yayi yace hajiya sapna abun ba gaisuwa?
Dakyar tabud’e baki ta gaishesa a wulak’ance.
Murmushi yayi sannan ya amsa yamaida kallonsa ga lubna da taketa danna waya yace
Baby gaskiya inason sapna dayawa Ammah ta k’i amince min ko da sau d’ayane, dan Allah kisa baki a ciki wlh zan baku kud’i masu tsoka.
Dariya lubna tayi irinta yan duniya tace Alh mai rabo wlh sapna ce sai ahankali har yanzu bata ida wayewaba idan kaganta kamar duka kenan ammah har ynz dasauranta.
Gaskiya ya dae kamata lubna ku wayar da ita ai na d’auka laifinkine tunda kina da iko da ita.
Kallon sapna tayi ta glass taga yadda tad’aure fuska murmushi tayi tace bakasan sapna da taurin kai bane.
Dai-dai lokacin suka iso wani gida mai kyau maigadi ne yataso tahangame masu gate suka shiga.
Dasauri sapna tafito daga cikin motar tatsaya tana jiran lubna tafito.
Lubna tace Alh mai rabo sai yaushe?
Toh ni koyaushe kikaban dama zan zo ko da yau ne am free,
Murmushi tayi tace saidai gobe kashigo gaskiya.
Toh ranki yadad’e nagode am indawo d’aukarku ko zaku tafi da kanku?
Juya ido tayi tace kabarshi kawai in mungama zamu tafi.
Kud’i yad’ebo dayawa yamik’o mata yace ga wannan kafin inshigo.
Kar6a tayi tana murmushi tace angode Alhajina sai ka shigo,
Cikin jaka tazuba kud’in tare da bud’e k’ofa tafito daga motar,
Alh zubairu yakalli sapna yace baby tunda ba magana sai anjima.
Ko kallon inda yake batayiba.
Lubna ta ta6e baki tace kyaji dashi dae kedai wlh ban san wace kalar yarinya bace.
Wucewa tayi fuuu cikin gidan sapna na biye da ita a baya.
Direct cikin parlour suka nufa gaskiya ba k’arya d’akin ya k’awatu dayawa domin ita kanta sapna saida ta jinjina ma had’uwar d’akin,
wata macece ta hakimce saman kujera zaune tana kallo,
Ganinsu yasa tataso da sauri tanufi inda lubna take suka rungume juna tace dear gaskiya baki kyauta min ba ace ganinki yana wahala.
Murmushi lubna tayi tace sorry friendy wlh hidimarce kinsan sai ahankali.
Tabb lailai lubna wlh kin ciri tuta dayawa.
Kallonta takai wajen wacce take bayan lubna tace wow masha Allah friendy wannan fa.
Murmushi lubna tayi tare da rik’o hannun sapna da take tsaye ta tsaresu da ido suka nufi kujera suka zauna.
Murmushi meerah tayi tare da kashe ido d’aya tace ko dai itama d’in ‘yar hannu ce,
Lubna ta gane abinda take nufi tace no wannan saidai hange daga nesa tsakaninku wlh.
Dariya meerah tayi tace kai my friendy bakida dama bari akawo maku abun motsa baki,
Cika masu table akayi da kayan motsa baki.
Meerah kusa da lubna tadawo tazauna suna ci suna hira, ita dai sapna ba ta sanya masu baki a cikin hirar tasu, apple tad’auko tana ci tana kallon T.V
Mik’ewa tsaye meerah tayi tace lubna idan kin gama kisameni a bedroom tare da kashe mata ido d’aya,
Lubna takalli sapna tana murmushi tace daughter bari inzo,
Tashi tayi tanufi bedroom d’in meerah, kallonta sapna tayi batace komai ba domin ta gano abinda take nufi.
Ta6e baki tayi tare da kwanciya bisa kujerar tajawo wayarta tahau chart…..
Yawan comments yawan typing✍????
masu cewa ink’ara tsawon page kuyi hak’uri dan Allah kuyi la’akkari da novel biyu nake rubuta at d same time, ammah insha Allahu zanyi iya k’ok’arina na ganin anba kowane novel hak’k’insa nagode sosai????
Muje Zuwa
????????????????
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
????????????????
Written By ~ Sis Nerja’art
DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA nd Sainah Ummun meenal
INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….✔
kuyi hak’uri jina da kukayi kwana biyu shuru wlh busy nake ammah duk da haka kuna raina fan’s nagode da k”aunarku
masu biye da ni a novel d’in K’ADDARA CE kuyi hak’uri ba zan samu damar muku typing ba ammah insha Allahu gobe zan muku ????
sis zernav ina tayaki murnar fara novel d’in BASSAM Allah yak’ara basirah da zak’in hannu muna biye dake muje zuwa my sisto????
7⃣➖8⃣
Sai da tayi kusan awa biyu kwance ganin har lokacin basu fitoba gashi lokacin sallah ya yi yasa ta tashi.
Kwankwasa d’akin tayi daga ciki akace wanene?
Jin muryarsu yasa tagane halin da suke ciki, tace nice mummy lubna lokacin sallah ya yi inaso inyi alwallah,
Muryar meerah tajuyo ta ce shigo mana sai kiyi alwallar sapna,
Sai da tad’an dad’e tsaye sannan tabud’e k’ofar tashiga yanayin da tagansu yasa gabanta yafad’i bata kalli inda suke ba tanufi wata k’ofa da tagani da alama nan ne toilet d’in.