BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

‘Dago kai yayi yakalleta yace daman dan Allah so nake ki aramin sapna tarakani anguwa ammah idan babu damuwa, murmushi ummah tayi tace haba haydar wannan ai ba wani abun damuwa bane bari inje inyi mata magana tashirya kutafi, nima yanzu zan je gidan kawunta muyi maganar, haydar cikin jin dad’i yace toh ummah.

Ummah lokacin da tashiga d’akin sapna daidai lokacin sapna tafito wanka, ummah fuskarta babu walwala tace kishirya zaku fita ke da haydar, sapna marairaicewa tayi tace ummah ina zamuje? Ummah wucewa tayi zata fita daga d’akin tace nima ban san inda zakujeba ko ma dai ina ne kindai san ba saidake zaiyiba dan haka kiyi sauri kishirya kar ki6ata masa lokaci, nima yanzu zan je gidan kawunki, sapna tace toh ummah, tsaki taja tace ko ina zai kaini? cikin sauri tad’auko gown ta atamfa pink nd brown colour tasaka, gyara fuskarta tayi sannan tasaka hijab brown colour tafeshe jikinta da turare sannan tasaka flat shoes tafito fuskarta babu yabo babu fallasa tashiga d’akin ummah da sallamarta, suka amsa mata kallo d’aya haydar yayi mata yad’auke kai tare da had’e fuska, gudun kar ummah tayi mata fad’a yasa sapna tagaishesa ciki-ciki, shima a wulak’ance ya amsa mata,

sapna tace ummah na shirya, ummah tace ai ga wanda zakuyi tafiyar da shi nan, haydar tashi yayi yace toh ummah sai mundawo, ummah tace adawo lafiya Allah yakiyaye hanya, sapna ga d’ayan key d’in gidan domin ban saniba ko zaku rigani dawowa, kar6a sapna tayi tace toh ummah.

Suna fita haydar yabud’e motarsa yashiga, sapna tsaye tayi ganin batada niyar shiga yasa haydar yak’ara tsuke fuska yace kishigo mana malama kin wani yi min tsaye,

Sapna tsaki taja ahankali sannan tabud’e gaban motar tashiga, nan haydar yatada motar tafiya suke ammah ba wanda yatanka ma d’an uwansa su dukansu fuskarsu a d’aure take har suka iso AKTH

Mamakine yakama sapna ganin ya kawota asibiti, ko da yayi parking a wulak’ance yace fito muje, sapna kallonsa tayi tace ina kuma za ni? Me zanyi a nan? Cikin tsawo haydar yace nace kifita muje, sapna turo baki tayi tare da bud’e motar ta fita,

haydar yana gaba tana biye da shi a baya har sukaje wani office, haydar knocking yayi daga ciki aka basu izinin sushiga, ko da suka shiga mutumin zaune yake yana sanye da lab-cut da ka gansa ka san Doctor ne, ganinsu yasa yamik’e cikin fara’a yace a’ah Dr haydar ashe kaine, hannu haydar yamik’a masa suka gaisa yace sauri nake nazo dan nasan halinka kana iya fita, dariya Dr salim yayi yace aikam dai da yanzu nake shirin fita dan ma ka ce min zakazo saisa nazauna, ;kallon sapna yayi da take tsaye bayan haydar ta had’e fuska, murmushi Dr salim yayi yace sannu ‘yan mata, sapna fuskarta a d’aure tace yauwa, Dr salim kallon haydar yayi yace Doctor wannan ce? Haydar yace eh itace,

Dr salim yace ohk, ‘yan mata kizauna mana, sapna shuru tayi kamar ba da ita yake magana ba, haydar ganin batada niyar Zama yasa yace bakiji ana miki magana?
Sapna tsaki taja sannan tajawo kujerar ta zauna, shima haydar Zama yayi, Dr salim allura yad’auko yadawo inda sapna take zaune yace ‘yan mata kawo hannunki,
Kallonsa sapna tayi a wulak’ance tace ance maka banda lafiya ne da zakayi min allura?

Haydar a fusace yace kibada hannunki mana,
Harararsa sapna tayi tace ba zan bayarba ni lafiyata lau,
Cikin 6acin rai haydar yace ko kibada ko insa6a miki yanzun nan, Dr salim yace haba doctor kabita a hankali man, ganin dagaske yake yasa sapna tamik’a hannunta nan Dr salim yad’ibi jininta sannan yawuce yace kujirani bari indawo,

Sapna kwallah ce tacika mata ido nan tafara hawaye tana gogewa, ko inda take haydar bai kallaba dannar wayarsa kawai yake, sai da akayi kusan minti goma sannan Dr salim yadawo hannunsa d’auke da result yamik’a ma haydar cikin fara’a yace Alhmdllh a iyakar bincikenmu mun gano bata tare da kowace irin cuta, haydar kar6a yayi yana dubawa, da mamaki sapna take kallonsa tace wai daman gwaji kakawoni ayi min? Haydar a wulak’ance yace kina tunanin zan aureki a haka? Wuce muje, sapna bayansa tabi cike da takaici bata ma tsaya amsa ma Dr salim da yake ta yi mata bankwana ba, tafiya take tana kwallah har suka shiga mota, kife kanta tayi a saman cinyarta daurewa kawai take kar tayi kuka domin bataso tanuna ma haydar tun ynz ta karaya yaji dad’in wulak’antata,

Haydar kallonta yayi yana murmushi yace bai dace ace tun yanzu kin fara zubar da hawayenkiba ya kamata ki adanasu har sai kin shigo gidana, sapna d’ago kai tayi dasauri tashare hawayenta tace haydar tabbas a yanzu na ida gane kai mak’iyinane, me yasa ka amsa zaka aureni alhali ka san baka sona? Kamar yarda baka sona toh nima haka bana sonka dan haka kajanye aurena,
Ta6e baki haydar yayi yace toh ya zanyi tunda sadakarki aka bani kuma ba zan iya musu da mahaifiyarki ba dan haka kawai kishirya Zama da ni,

sapna takaici yacikata takasa ce masa komai ahaka har suka isa gida.

Ko da suka iso gida lokacin ummah bata dawoba dasauri tabud’e gidan tashiga dagudu, tana shiga d’akinta tafad’a saman gado kukan da take 6oyewane yaci k’arfinta nan tafara rusawa saida tayi kuka sosai cike da takaici tace yanzu ni haydar zai kai ayi ma gwajin HIV? Lallai na yarda da maganarsa da yace kafin inshiga gidansa in tanadi maganin ciwon zuciya da hawan jini, tsanar haydarce tsantsa taji ta kamata…..

Comments
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Page 3⃣1⃣

Ummah ko da taje gidan baba sani ta yi sa’a yana gida, cike jin dad’i matarsa tatarbeta tayi mata iso har d’akin baba sani, bayan sun gaisa nan take shaida ma baba sani game da neman auren sapna da za a zo gobe, kasancewar su baba sani sunsan haydar dan haka cike da jin dad’i baba sani yace Alhmdllh, Allah yakaimu Allah yasa ayi da mu, nan yace ma ummah tarubuta abinda take buk’ata Wanda za’a tarbi bak’i da su zai siya, nan ummah tayi masa godia.

Ko da ummah tadawo gida bata fad’ama sapna komai ba game da neman aurenta da za’azo, saida Aunty karima matar baba sani tazo domin tataya ummah aiki nan sapna take samun labari a wajenta da cike da mamaki takalli ummah tana shirin yin magana ganin yadda ummah tahad’e fuska yasa takasa cewa komai dan haka tatashi cike da takaici tashige d’akinta takwanta saman gadonta tafara rera kuka cikin kuka tace tabbas yanzu na tabbatar dagaske ummah dai haidar zata aura min mutumin da baya sona ya tsaneni nan tasake fashewa da wani sabon kukan cike da tausayin kanta, saida tayi mai isarta sannan tayi shuru nan tajawo wayarta domin tayi chart tasamu sauk’in abinda yatokare mata mak’ogwaro, tunowa da tayi da new Sim ne ummah tacanza mata dan haka tafasa chart d’in takunna film tana kallo, tana ji su ummah suna hidimarsu ammah tak’i zuwa tatayasu saboda haushin kowa takeji, a ranar a d’akinta tawuni ko abincin dare bata fito taciba a haka takwanta bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button