DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Washe gari tun da safe Aunty karima tadawo suka cigaba da shirye-shiryensu sapna sai wajen 11am tafarka bacci saboda bata kwanta da wuriba, cikin sauri tatashi tashiga toilet tayo wanka agurguje tashirya tatafi gidan kitso gudun kar ‘yan neman aure suzo suganta.
Su ummah saida suka gama komai sannan sukayi wanka suka shirya, baba sani ma ko da yadawo daga sallar azuhur shi da abokinsa gidan suka zo domin sutarbi bak’i kasancewar haydar ya fad’a musu bayan azuhur su daddynsa zasu zo.
daddy ne da k’anensa mahaifin Ahmad dukazo basusha wahala ba wajen gane gidan, cike da fara’a aka tarbesu bayan angama gaisawa nan aka cikasu da kayan ciye-ciye, bayan an nutsu nan suka fara tattaunawa akan maganar neman auren da yarda sukeso yakasance domin da shirin yin baiko sukazo, daddy yace basuson asa bikkin dayawa murmushi baba sani yayi yace toh shikenan Alhaji asa wata biyar, daddy shuru yayi sai chan yace muna dai neman alfarma abarshi nan da wata biyu domin wata biyar ya yi yawa, baba sani yace a’a adai k’ara abarshi wata hud’u, dakyar su daddy suka shawo kansa yabarshi a matsayin wata biyun domin yana Jin nauyinsu saisa ya amince, cike da jin dad’i su daddy sukayi godia nan sukaje suka bud’e boot d’in motarsu aka fito da kayan sa bikki suka had’a da kud’in na gani ina so sannan sukayi bankwana cike da farin ciki sukabar gidan sunji dad’in yarda aka karramasu tun daga yadda suka ga gidan da sapna tafito sukasan ‘yar mutunci ce, tun a hanya Daddyn Ahmad yakira haydar yafad’a masa yadda sukayi da dangin sapna da irin karramawar da akayi musu, haydar murmushi yayi yace daddy ai haka suke akwai mutunci,
Bayan sun gama wayar Haydar abokinsa Dr Ahmad yakira, Ahmad yana d’auka ko sallama baiyiba yace gwauro ya dai? Tsaki haydar yaja yace ba ko sallama? Dr Ahmad Dariya yayi yace sorry my friend nan yayi masa sallama bayan sun gaisa yace ya gwauranci? Murmushi haydar yayi yace kakwantar da hankalinka nan da 2 months nima zan angwance,
Dariya Ahmad yayi yace kai ni banason zolaya, haydar yace kai malam na ta6a yi maka irin wannan wasan? Ahmad yace toh ai abun ne yaban mamaki ya za’ayi ace ka fara neman aure batare da na saniba, haydar murmushi yayi yace kaje katambayi su daddy kaji idan ba gaskiya bane yanzu ma suka dawo daga chan, Ahmad yace yanzu batare da na saniba akayi komai?
Ta6e baki haydar yayi yace bana buk’atar kowa yasanine daman sai komai ya tabbata,
Tsaki Ahmad yayi yace wlh Haydar dan dai na San halinka nasan zaka aika, ammah da na ce na yi fushi,
Haydar cike da k’osawa da maganar yace kai ni fa ka dameni da hayaniya kawai dai kayi min addu’a,
Murmushi Ahmad yayi cike da jin dad’i yace Allah yasa alkhairi gaskiya naso insan wace mai sa’arce tasace zuciyarka domin ban ta6a kawo ma raina zakayi aure a wannan lokacin ba, d’aure fuska haydar yayi kamar yana gaban Ahmad, yace kar kayaudari kanka domin ni babu wacce tasace zuciyata kai ni fa zanyi auren nan ne kawai domin inhuta da surutun su Mami, ammah nan gaba ina tunanin zan samu kalar macen da nakeso in aura,
Cike da mamaki Ahmad yake sauraren haydar yace haba abokina ya za’ayi ace zaka auri wacce baka so kuma fa kai kaza6a ma kanka itafa, haydar yace nidai ka cika ni da surutu dan haka sai anjima, tun kan Ahmad yayi magana tuni haydar ya tsinke wayar, Ahmad bin wayarsa yayi da kallo cike da mamakin halin haydar jinjina kai yayi domin tabbas ya san yin hakan k’aramin aikin haydar ne, saboda ya sanshi fiye da yunwar cikinsa, yace lallai haydar har yanzu baka canza ba.
Matarsa yakalla da take sauraren firar tasu tace lallai hubby ashe haydar aure zaiyi gaskiya na tayasa murna Allah yasa wannan ta kirki ce, murmushi Ahmad yayi yace Ameen my wife wlh lamarin haydar yana bani mamaki wai har yana neman aure ammah ban saniba muna tare, Dariya salaha tayi tace toh ai ba abun mamaki bane tunda ka san halin abokin naka, murmushi Ahmad yayi yace hakane kuma na san k’aramin aikinsa ne dan ma na yi sa’a da ba sai ana gobe bikki yafad’a min ba, yanzu dai bari kiga intashi inje wajen mutumin nan nawa, Dariya salaha tayi tace ya dai kamata
salaha har bakin motarsa tarakasa saida taga tafiyarsa sannan tadawo gida cike da k’aunar mijin nata.
Ahmad ko da yaje gidansu haydar nan yatadda danginsu sosai sai a lokacin yatabbar da abinda haydar yafad’a masa, bayan sun gaisa da su mami sannan yawuce part d’in haydar lokacin haydar yana shirin fita ganinsa yasa yafasa suka koma ciki, Ahmad nan yafara tsokanar abokin nasa duk yadda yaso haydar yafad’a masa yadda akayi yafara neman aure ammah yak’i tanka masa ganin haka yasa Ahmad yakyalesa domin ya san abokin nasa bakowa yake iya bugun cikinsaba sai inyaso kasan wani abu game da shi sai yafad’a maka.
Sapna sai bayan la’asar Sannan tadawo gida ita har ma ta mance da batun neman aurenta, tana shigowa tatarar da su ummah zaune suna ta kasa kayan sa bikki tsaye tayi takasa motsawa daga inda take, Aunty karima ce talura da shigowarta nan tasaki gud’a tace Alhmdllh Sapna yau gashi muna cin kayan sa bikkinki nan da wata biyu kin zama amarya
Allah yakaimu lokacin da zamu kaiki gidan haydar,
Sapna fashewa tayi da kuka cike da takaici tace yanzu ummah dagaske haydar zaki aura min? Kuma sai kace angaji da ni za a ce nan da wata biyu za ayi min aure, Wlh bana sonsa shima baya sona,
Cikin 6acin rai ummah tace ko da zaki mutu wlh indai ina numfashi sai kin auri haydar, Aunty karima da tayi sororo tana kallon Sapna cikin kwantar da murya tace haba Sapna menene abun k’i atare da haydar gashi mutumin kirki,
Sapna k’ara fashewa tayi da kuka tace wlh Aunty bana sonsa,
Ummah cikin 6acin rai tamik’e zata nufi inda Sapna take tsaye dasauri Aunty karima tarik’eta tace a’ah maman Sapna kar kita6ata, ummah cikin fad’a tace karima kibarni inkarya d’iyar chan inhuta da bak’in cikinta tunda ita butulu ce batasan mutunci ba, Aunty karima tace kiyi hak’uri maman Sapna abi ta ahankali sai komai yazo cikin sauk’i.
Dasauri Sapna tashige d’akinta tana kuka tabbas tasan tunda ummah tafurta toh sai ta auri haydar, jin yarda kanta yake sara mata yasa takwanta k’asa nan da nan zazza6i yarufeta,
Ummah tun abun baya damunta ammah ganin har bayan magrib bata ji motsin Sapna ba yasa tafara damuwa domin bata tunanin yau sapba ta ci wani abu, dan haka tatashi tanufi d’akinta,
Tana shiga tatadda Sapna a kwance sai rawar d’ari take dasauri ummah ta isa inda take cike da tashin hankali tace Sapna lafiya? Rungumota ummah tayi a jikinta tace sapna zazza6i kike? Sapna lumshe idanunta tayi hawaye suna fita ta kasa cema ummah komai, cikin damuwa ummah tace sapna na d’auka ina da ikon Za6a miki kowane irin miji kuma kikar6esa hannu bibbiyu ashe yarda nake tunani ba haka bane, haydar na yarda da tarbiyansa nasan ko bayan raina zai kular min da ke ni ina ganin gatane nayi miki a matsayina na mahaifiyarki ashe a wajenki ba gata bane ummah k’wallah ce tacika mata ido tace shikenan sapna tunda baki sonsa bari amayar musu da kayansu nima nima na fasa idan haka kikeso kicigaba da rayuwa babu aure toh sai muyi ta zama gidan har mai rabawa tarabamu, ahankali sapna tabud’e idanuwanta da suka k’ank’ance saboda kuka tasafkesu akan fuskar ummah ganin ummanta tana hawaye yasa hankalinta yak’ara tashi tafashe da kuka muryarta tana rawa tace ummana kigafarceni wlh na amince zan auri haydar tabbas nasan bani kyauta miki ace kina zubar da hawayenki saboda ni na kar6i za6inki hannu bibbiyu domin nasan ba zaki ta6a za6amin abinda zai cutar da ni ba dan Allah kiyafe min insha Allahu na yi miki alk’awali ba zaki k’ara zubar da hawayenki saboda da ni ba, cike da jin dad’i ummah tace nagode sosai sapna insha Allahu ba zaki ta6a da nasaniba akan aurenki da haydar domin ina ji a raina Alkhairi ne aurenku, sapna rungume ummah tak’ara yi tace nagode ummana insha Allahu zaki sameni mai biyayya ammah bana so kina zubar da hawayenki saboda da ni, ummah goge hawayen fuskarta tayi tashafa kan sapna tace Allah yayi miki albarka sapna, murmushi sapna tayi tace Ameen ummana,
Ummah dakanta taje tazubo ma sapna abinci tatisa a gaba saida taci sannan tasha magani takoma takwanta nan take wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, cike da tausayinta ummah tagyara mata lullubinta sannan tatashi tafita tabar d’akin.
Ko da tatashi dasafe zazza6in ya safka dan haka tadaure tana 6oye damuwarta gudun kar tatada hankalin ummanta.