BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

daga nan suka wuce da sauran kayanta chan gidan haydar da ke jan-bulo lokacin an ma kusan gama gyaran gidan aka samu d’aki d’aya aka zuba mata d’ayan gadonta da su wardrobe, sun yaba tsarin gidan nata ko da cikin gyaransa ake ammah ya yi kyau sosai. Nan akayi ta santin gidan.

bayan la’asar su sapna suka dawo nan Aunty karima tatisata gaba taje tayi wanka domin wa’azi da za ayi, sapna da mamaki takalli Aunty karima tace Aunty daman za”ayi wa’azi shine ba a fad’a min ba, Aunty karima tace toh ai naga bikkin kamar ba so kikeba saisa bamu fad’a mikiba yanzu dai kiyi maza kiyi wanka kishirya kinga la’asar ta yi, sapna turo baki tayi tawuce tashiga wanka cike da takaici domin ita a ganinta daman ace wanda takeso ne da bazata damuba ammah wanda bataso kuma shima baya sontane, a toilet saida tasha kukanta sannan tayi wanka.

Bayan ta fito wankan shiryawa tayi cikin atamfarta pink nd ash colour tasaka hijab ash anan tsakar gidansu akayi wa’azin inda malama Aysha tagabatar da shi mutane dayawa sun samu zuwa abin har mamaki yaba sapna yadda akayi mutane sukasan da wa’azin da ita kanta bata san da shi ba.

Malama Aysha wa’azi tayi akan aure mai ratsa jiki nan masu karyayyar zuciya sukayi ta kuka hatta itama kanta amaryar saida tayi kuka sosai jikinta yayi sanyi.

Bayan angama wa’azin kayan da aka tanada domin araba ma mutane aka shiga rabawa..

Comments
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Page 3⃣2⃣

Rana bata k’arya saidai uwar d’iya taji kunya a yau asabar aka d’aura auren Sapna Aliyu da Aliyu (haydar) Kabir, inda mutane dubbai suka hallara a chan tsakiyar mutane nahango ango ya ci gayu sai fara’a yake yana gaisawa da mutane.

Gidajen biyu cike suke da mutane ‘yan bikki ana ta shige da ficce.

Sapna ko saida akayi dagaske sannan aka samu tayi wanka, a chan tsakiyar gado nahangota zaune fuskarta babu walwala idanuwanta kawai zaka kalla kashaida cewar ta yi kuka, gefenta k’awarta ce Amina zaune,

Bayan andawo daga d’aurin aure baba sani yasa aka kira masa Sapna yayi mata nasiha sosai tare da addu’an Allah yabasu zaman lafiya.

Sai gab da magrib sannan su Aunty karima suka tusata gaba taje tayo wanka da ruwan turare da aka tanadar mata, saida sukayi sallar magrib sannan Sa’adatu makeover tashiga yi ma amarya kwalliya, saida suka d’au kusan awa d’aya sannan aka gama kwalliyar nan kyaun Sapna yak’ara bayyana kowa ya yaba da kyaun da tayi, cikin kayan lefenta aka d’auko mata wani dank’areren less mai kyau da tsada maroon colour ne mai ratsin blue, d’inkin yaimata cifcif aka d’and’ara mata d’aurin kallabi, gyalenta da takalma da handbag duk suka kasance blue colour, saida sukayi sallar isha’i sannan aka kaita d’akin ummah nan ummah tayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki,

Wajen k’arfe takwas haydar ya aiko da motocin da za a kwashi amarya,

Sapna rungume ummah tayi tana kuka duk yadda ummah taso tadaure ammah takasa itama kukan tayi dakyar aka samu aka 6an6are Sapna daga jikin ummah aka tafi da ita, har aka shiga mota kuka take.

A dank’areren gidan su haydar akayi horn dasauri mai gadi yazo yahangame musu gate, part d’in su mami aka nufa da ita fuskarta tana a lullu6e har lokacin da sauran ‘yan bikki a gidan, hafsat ce cike da farin ciki tataresu tayi musu jagora zuwa d’akin ummah, nan ma cikin fara’a aka tarbesu aka gaggaisa, itadai Sapna tana cikin gyalenta sai hawaye take bayan an damk’a ma su mami amanarta sannan aka tafi da amarya part d’inta kasancewar akwai tazarar tafiya tsakanin part d’inta da iyayen haydar, saida aka kaita bed room sannan aka zaunar da ita saman gadonta, sannan ‘yan kawo amarya suka fara zagayewa suna kallon tsarin gidan kowa ya yaba tsaruwa da kyaun da yayi tare da jinjina ma ummah k’ok’arin da tayi Wajen yi ma ‘yarta kayan d’aki masu tsada,

Nan mutane suka fara watsewa Amins da Aunty karima ne suka zauna suka k’ara gyara mata gidan, ko da zasu tafi dakyar Aunty karima takwace daga rik’on da Sapna tayi mata, nan suka bar Sapna tana kuka baka jin motsin komai gidan ya yi shuru,

Wajen k’arfe goma bacci yayi awon gaba da Sapna kasancewar a gajiye take.

Haydar sai wajen k’arfe sha d’aya yashigo fuskarsa a d’aure babu alamun fara’a a tare da shi hannunsa rik’e da bak’ar leda, saida yarufe k’ofar sannan yashiga bedroom tsaki yaja ganin Sapna a kwance saman gado ta k’udundune jikinta sai bacci take, bai tashetaba sai da yashiga yayo wanka yashirya, sannan yanufo inda take fuska a d’aure yace ke kitashi,

Sapna cikin bacci taji kamar ana kiranta ahankali tabud’e idonta da mamakinta sai ganin haydar tayi a tsaye k’afarsa d’aya bisa gadon fuskarsa a d’aure, dasauri Sapna tatashi zaune tare da k’ara gyara gyalenta, haydar d’auke kai yayi daga kallonta yace kin dai shiga kin fita saida kika samu na aureki toh ina tayaki murnar shigowarki gidana, da mamaki Sapna take kallonsa ya kashe mata baki ta kasa cewa komai, yace kibud’e kunnuwanki kisaurareni dakyau ammah kafin nan hannu yamik’a yace bani wayarki, Sapna batayi musuba tad’auka tamik’a masa SIM d’inta yazare yakarya ya aje wayar saman bedside yace bana buk’atar ganinki da waya sannan kar ki kuskura inga wata k’awarki ta zo min gida idan har kika saki hakan takasance wlh sai na 6ata miki rai, babu yawo ko nan da k’ofar get bance kilek’aba dole kibar wannan d’abi’ar taki ta yawon iskanci, kuma daga yanzu k’asa shine zai kasance wajen kwanciyarki saboda ba zan iya had’a shimfid’a da ke ba, kar kisaki kibar min gidana da dirty duk ranar kuma da kika bari hakan takasance toh kema kinsan sauran sbd ni bana son k’azanta dan haka dole ki aje k’azantarki tunda kin shigo gidana, wannan mummunar d’abi’ar taki da iskancinki dole ki ajesu gefe, murmushi yayi yace kar ki d’auki kanki a matsayin matar haydar domin baki kai matsayin da zaki kasance matataba. Dafatan kin ji kashedin da nayi miki.

Sapna tunda haydar yafara maganar hawaye kawai take takaici ya cikata, duk yadda taso tayi magana ammah kasawa tayi kallon haydar kawai take, haydar cikin rashin damuwa yace malama bacci nakeji kisafka kiban waje zan kwanta, murmushin takaici Sapna tayi tace haydar nagode sosai da bak’ak’en maganganun da kaya6a min sannan kar kad’auka na ji haushi, girgiza kai tayi tace a’a ko d”aya banji haushiba domin daman tun kan inshigo gidanka nasan abinda zan tarar kenan daga gareka saidai abinda yaban mamaki shine ban d’auka iyakar nan zaka tsaya a wulak’ancin nakaba, Sapna a shirye take k’ofa a bud’e take kayi mata duk wulak’anci da cin mutuncin da kaga dama ammah kuma inso kasani bana d’aukar raini, dariya haydar yayi yace ashe kina da baki haka lallai na tayaki murna, Sapna shiru tayi tare da tashi tajawo blanket tashimfid’a k’asa takwanta, ganin haka yasa haydar yahaye saman gadon yayi kwanciyarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button