DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Sapna ko da takwanta k’asa juyi kawai take takasa bacci saboda bata saba kwanciya ba saman gadoba, Sai gab da asuba sannan bacci yayi awon gaba da ita,
Kiran sallar asubane yatashi haydar daga baccin da yake, dasauri yasafko daga saman gadon yashiga toilet yad’auro alwallah, ko da yafito har lokacin Sapna bacci take har zai wuce, ko mi yatuno kuma sai yadawo yace ke kitashi, Sapna dakyar tabud’e idonta taganshi tsaye, batare da ya kalletaba yawuce yafita.
Dakyar tamik’e ko’ina na jikinta yana mata ciwo saboda ta yi kwanciyar da bata saba irinta ba, toilet tashiga tad’auro alwallah tazo tayi sallah ta dad’e saman darduma tana addu’a sannan daga baya tatashi takoma saman shimfid’arta takwanta,
Bata dad’e da kwanciya ba taji shigowar Haydar, nan shima yahau gado yakwanta.
Wajen k’arfe goma kwankwasa k’ofar da akene yatashesu haydar ne yafito yaje yabud’e,
Hafsat ce tsaye da basket a hannunta nan tasakar masa murmurshi shima yamaida mata tace yayana dafatan kun tashi lafiya, haydar yace lafiya lau k’anwata, Hafsat tace daman mami ce tace akawo muku breakfast, murmurshi haydar yayi yace mungode sosai sannan yabata hanya tashigo,
A dining area tajera musu sannan takalli haydar tace Aunty Sapna bata tashiba?
Murmurshi haydar yayi yace eh bacci take.
Hafsat tace toh idan ta tashi agaisheta bari intafi nabaro Afnan tana ta kuka, Haydar yace ni ai nad’auka kin koma gidanki tun jiya, murmurshi Hafsat tayi tace toh yaya ai dadyn Afnan baya gari saisa yace inzauna sai ya dawo,
Haydar yace toh shikenan Allah yamaidosa lafiya, Hafsat tace Ameen my lovely Bro.
Tana fita haydar yamaida d’akin yarufe sannan yakoma bedroom har lokacin Sapna kwance take, nan yawuce yashiga wanka,
Sapna tana jin shigarsa tatashi talinke blanket d’in sannan tagyara gadon, nan takunna turaren wuta kasancewar ta saba a chan gidansu da tatashi sai ta fara gyara d’akinta sannan take shiga wanka.
Lokacin da haydar yafito tana tsaye wajen wardrobe tana duba kayan da zata d’auka nan tad’ago kai takallesa lokacin yana tsane ruwan da yake jikinsa da d’an k’aramin towel, jikinsa d’aure yake da towel, dasauri tad’auke kai daga kallonsa.
Material tad’auko black colour mai ratsin red sannan tad’auki inner wears d’inta tawuce zata ra6a gefensa tashige toilet,
Haydar fuskarsa a d’aure yace ke baki iya gaisuwaba? Shuru Sapna tayi kamar ba da ita yakeba, Haydar jawota yayi tafad’o jikinta har kayan da suke hannunta suka zube, yace ba da ke nake magana ba? Sapna babu alamun tsoro a tare da ita tace ni kasakeni,
Haydar cikin 6acin rai yace ba zan sakekiba nace baki iya gaisuwaba? Sapna tayi rau-rau da ido kamar zatayi kuka tace na iya, haydar yawurga mata harara yace dan kin raina ni shine bakijin zaki iya gaisheni,
Sapna ahankali tace ai ban d’auka kana son gaisuwarba, ina kwana?
Haydar batare da ya amsaba yasaketa yacigaba da abinda yake, Sapna duk’awa tayi tatattara kayanta tashiga toilet tamaida k’ofa tarufe ahankali tace mugu kawai,
Ko da tagama wankan saida tafara tsane ruwan jikinta sannan tasaka kayanta tafito, lokacin haydar yana tsaye yana fesa turare sanye yake da galilarsa red colour.
Jira tayi saida yamatsa daga gaban mirror d’in sannan taje tazauna tafara kwalliya, lokacin haydar yana waya.
Bayan ya gama kallonta yayi yace idan kin gama kifito parlour ga breakfast nan, bai Jira jin amsartaba yawuce yaficce,
Ta cikin mirror Sapna tarakasa da harara tare da Jan guntun tsaki, saida tagama shirinta tas sannan tafito tanufi parlour saboda wata irin yunwa da takeji, a chan dining area tahango haydar zaune yana breakfast yana dannar wayarsa,
Itama chan tanufa tazuba chips tahad’a tea daidai wanda zai isheta tazauna tafara ci ta ma d’auka haydar zai yi mata magana tabar wajen ammah taga ko inda take bai kallaba.
Wurin Shuru yayi bakajin motsin komai sai na spoons d’insu, haydar batare da ya kalletaba yace idan kin gama kid’auko gyalenki muje mugaishe da su mami,
Sapna tace toh sannan tacigaba da breakfast d’inta, haydar tashi yayi yakoma parlour yazauna,
Sapna Bayan ta gama gyara wajen tayi tatattara kayan takai kitchen tawanke sannan tafito tawuce sa a parlour taje bedroom tad’auko red d’in gyalenta tayafa sannan tafito,
Nan haydar yamik’e yana gaba tana biye da shi a baya har sukaje part d’in su mami,
Da sallamarsu suka shiga lokacin su daddy suna zaune suna hira, ganinsu yasa hafsat tataso dagudu tarungume sapna tace oyoyoo amaryarmu, gyalen da sapna tajanyo har yakusa rufe mata ido hafsat tajanye tace sai na riga kowa ganinki,
Su mami dariya sukayi mata, haydar yace wai hafsat miye haka, murmushi hafsat tayi tana kallon sapna da ta sadda kanta k’asa tana murmushi, Hafsat tace masha Allah my lovely Bro wlh ka iya za6en mata ga kyau ga kunya, d’ago ma sapna kai hafsat tayi tace kin had’u Aunty sapna,
Sapna kallon hafsat tayi ak’allah hafsat zata girme mata da shekara d’aya ko biyu nan tasakar ma hafsat murmushi tace nagode,
rik’o hannunta tayi sukaje suka zauna k’asa gefen su mami, nan fahad ma yaje yazauna yagaishe da iyayensa, cikin girmamawa cike da kunya sapna tagaishesu,
cikin sakin fuska suka amsa mata, daddy yace ya bak’unta? Sapna cike da jin kunya tace Alhmdllh,
Murmushi Mami tayi tace d’iyarnan tawa akwai kunya kisaki jikinki muma ai iyayenkine,
Murmushi daddy shima yayi yace kinjiki da wata magana ai dole sai takwana biyu idan tasaba da mu sai tasake, kema lokacin da aka kawoki ai haka kikayi, k’ara ma ita, ammah fa kiyi hak’uri gaskiya nafad’a.
Gaba d’ayansu sukasa dariya, daddy yace toh Alhmdllh amarya muna miki barka da shigowa family d’inmu, Allah yasa albarka a cikin aurenku Allah yabaku zaman lafiya, Su mami sukace Ameen.
Daddy yacigaba da cewa haydar a matsayinka na babba wannan amanace a gareka karik’eta tsakani ga Allah, haydar yace insha Allahu daddy,
Daddy yace kema haka sapna kibi mijinki kuzauna lfy kurik’e sirrin junanku idan har haydar yayi miki wani abu badaidaiba toh ga mahaifiyaku nan kifad’a mata insha Allahu mu kuma zamu d’au mataki yanzu k’ark’ashinmu kike mune iyayenki dan haka duk abinda kike buk’ata mu zaki tuntu6a, Sapna ahankali tace toh daddy mungode,
Daddy kallon mami yayi yace ko kina da abinda zaki fad’a?
Murmushi mami tayi tace duk abinda zance ka gama fad’ansa Allah yabasu zaman lafiya adaiyi hak’uri da juna domin zaman aure sai da hak’uri, kaikuma haydar karage wannan muguwar zuciyartaka karik’e matarka tsakani ga Allah,
Murmushi haydar yayi yace mami ai yanzu na daina, mami tace eh toh dasauk’i ka dai rage za a ce.
Daddy yace toh masha Allah, Allah yabada zaman lafiya gaba d’ayansu sukace Ameen, nan daddy yayi musu addu’a yace sutashi sukoma part d’insu, godia sukayi ma su daddy sannan suka tashi suka tafi,
Suna komawa part d’insu haydar kallonta yayi cike da jin haushi yawurga mata harara yace kallarki dan Allah sai wani sunne musu kai kike waike mai kunya nan ko ba’asan ‘yar iska bace ta bugawa a jarida,
Cikin 6acin rai sapna tace eh na ji ni ‘yar iskarce ina ce shima iskancin sai mutum ya amsa sunansa sannan zai iya, in kanaso sai ayankar maka ticket d’in kaima kabi layi, tsaki taja tawuce zata bar wajen.
Cikin zafin nama haydar yajawota tafad’o jikinsa Cikin 6acin rai yace ubanwa kikeyi ma tsaki? Ni tsarankine? Sapna d’ago kai tayi takallesa gani tayi saboda 6acin rai idanuwansa har sun kad’a sunyi jawur,