BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Haydar yadaka mata tsawa yace dake nake magana, sapna har saida ‘yan hanjin cikinta suka kad’a saboda tsoro tace Allah yabaka hak’uri ni ba da kai nakeba,

Haydar yace toh da wa kike? Sapna tayi rau-rau da ido tace ba fa dakai nakeba, tureta haydar yayi har takusan fad’uwa, yace ashe iskancin naki bai kai inda nake tunani ba tunda har kika tsorata,

Wucewa yayi zai shige bedroom, sapna ahankali tace Allah ya isa,

Juyowa haydar yayi yace me kikace? A tsorace sapna tazaro ido tace wani abu kaji na ce? tace ni bance komai ba.

Tsaki haydar yayi sannan yashige bedroom, bai dad’e da shigaba taga ya fito ya ficce daga gidan, tana ganin haka tatashi tak’ara gyara parlournta takunna turaren k’amshi sannan tawuce bedroom taje tana k’ara shirya kayanta, duk abinda taga jeransa baiyi mataba nan tahau gyara,

Wajen k’arfe d’aya tagama komai sannan tashige toilet tayo wanka tare da d’auro alwallah, bayan ta fito, zama tayi gaban dressing mirror tayi kwalliya sosai, bayan ta gama atamfa tad’auko riga da skirt lemon green colour tasaka, nan d’inkin yayi cif-cif a jikinta, tamurza d’aurin kallabi, sannan tayi sallar azuhur bayan ta gama tadawo parlour tazauna har lokacin haydar bai dawoba… …

Comments
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Masoya Nagode Sosai inajin dad’in comments d’inku masuyi a groups da masuyi min ta pc, wlh ina jin dad’in hakan Allah yabarmu tare, I heart you all????????

Page 3⃣3⃣

bata dad’e da zamaba taji ana knocking d’in k’ofa, tashi tayi taje tabud’e, hafsat ce tagani tsaye murmushi sapna tayi tace sannu da zuwa, itama hafsat murmushin tayi tace yauwa, masha Allah matar yaya kinyi kyau sosai, murmushi sapna tayi tare da kar6ar basket d’in da yake hannun hafsat suka shigo, a tare sukaje suka jera kulolin a dining area sannan suka dawo saman kujera suka zauna,

Sapna takalli hafsat da tatsareta da ido murmushi tayi tace maman Afnan ina wuni? itama hafsat murmushin tayi tace lafiya lou matar yaya, ya bak’unta, mun barki ke kad’ai ko?
‘yar dariya sapna tayi tace Alhmdllh, ina Afnan kika barota?
hafsat tace tana wajen nanny d’inta nabarota,
sapna tace ina ta sa ido inga ko za’a kawo min ita ammah shuru,
hafsat tace haba rufa mana asiri idan tazo matsamiki zatayi, rarrafe take ammah idan tayi miki wata 6arnar sai kace mai tafiya.
murmushi sapna tayi tace eh bakomai nidai akawo min ita. hafsat tace toh shikenan insha Allahu za a kawo miki ita dakanki zaki maidota ai.
sapna cikin jin dad’i tace aikam da na ji dad’i.

daidai lokacin haydar yashigo dasallamarsa, ganin hafsat yasa yasaki murmushi, nan suka amsa masa sallamar kallon sapna yake ganin yadda taci kwalliya, ko mi yatuno kuma, dasauri yad’auke idonsa daga kallonta
yakalli hafsat yace a’ah my sister ashe kina nan? ai k’ara da kikazo domin kid’ebe mata kewa tunda ni bana nan,

murmushi hafsat tayi tace yayana ai naga ka tafi ka bar mana ita itakad’ai saisa nazo mud’anyi hira.

haydar yace aikam dai kin kyauta bari ind’an shiga ciki inwatsa ruwa, hafsat tace toh yayana sai ka fito, sapna dai shuru tayi batace komai ba.
nan suka cigaba da hirarsu.

Bayan kamar kusan minti goma sai ga haydar ya fito sanye da k’ananun kaya ya yi kyau sai k’amshi yakeyi, gaba d’ayansu suka d’ago suka kallesa, hafsat ce tace masha Allah yayana ka yi kyau, haydar kallon sapna yayi suna had’a ido tasadda kanta k’asa cike da jin kunyar ganinta da yayi ta kallesa.

shima kallonsa yamaida wajen hafsat yana murmushi yace nagode sosai my sister, sannan yakalli sapna yace my dear please muje kibani lunch inci wlh yunwa nakeji,

sapna cike da mamaki take kallonsa, hafsat tace itama daman bata ciba sai kuci tare ni bari intashi intafi nasan yanzu Afnan farka. sapna tace haba tun yanzu?
murmushi hafsat tayi tace ai zan dawo da anjima, sapna tace toh dan Allah kitafo min da Afnan, hafsat tace toh insha Allahu.

Hafsat tana fita sapna tatashi tanufi dining da mamakinta taga haydar fuskarsa a d’aure kamar ba shi bane yagama dariya, batare da ta tanka masaba tazuba masa abinci, itama tazuba nata tazauna, haka suka ci abincin ba wanda yatanka ma d’an uwansa,

Bayan sun gama Sapna tattara kwanukan tayi takai kitchen tawanke bayan ta gama tafito a parlour ta tadda haydar kwance saman 3 seater hannunsa rik’e da waya yana ta dannawa. ganin haka yasa itakuma tashige bedroom taje tazauna bakin gado kad’aici duk yacikata tsaki taja cikin Jin haushi tace mugu kawai da ace ya barmin wayata ai da ko ummah ce na kira munyi hira tana nan zaune har aka kira sallar la’asar tashi tayi tashiga toilet takuskure bakinta kasancewar tana da alwallah,

tana fitowa daidai lokacin haydar yashigo d’akin suna had’a ido dasauri kowa yajanye idonsa daga kallon juna, tawuce taje tashimfid’a darduma, haydar bayan yayi alwallah fitowa yayi yatafi masallaci.

sapna bayan ta gama sallar la’asar parlour tadawo tazauna har ta tashi zata kunna kallo domin tarage kad’aici sai taga ba ayi wearing din kayan kallonba dan haka tafasa tadawo tazauna cike da jin haushi,

Har tayi sallar magrib ammah haydar bai dawoba, tsaki taja tace shi ya ficce ya barni ni kad’ai gida sai kace mayya da ace ya zauna ko da ba magana zamuyiba ganinsa kawai da zanyi a gidan zaisa ind’anji sauk’in kad’aicin,
k’arshe dai alk’ur’aninta tad’auko tana karantawa

Bayan sallar isha’i Mai aikin gidansu Haydar tazo takawo mata dinner, sapna takai saman dining ta aje, sannan tabata kulolin da aka kawo musu abincin rana ciki sai sukayi sallama,
bataci abincin ba tayi kwanciyarta saman kujera k’arshe bacci yayi awon gaba da ita.

Around 9pm haydar yadawo gidan, Kallon sapna yayi da take kwance saman kujera tana bacci, wucewa yayi yashige bedroom saida yayo wanka yayi shirin bacci sannan yadawo yaje dining abinci kad’an yaci yatashi, har zai shige bedroom sai kuma yaga bai iya barin sapna takwana ita kad’ai parlour ba, Dan haka yadawo, daga gefen kujerar da take kwance yad’an bubbuga, ahankali sapna tabud’e idonta batare da ya ce mata komaiba yashige bedroom,

Mamakine yakama sapna ganin yadda bacci mai nauyi yad’auketa har batasan dawowar haydar ba. Tashi tayi itama tashiga bedroom lokacin haydar yana saman gado ya yi d’ai-d’aya sai chart yake, turo baki tayi ahankali tace mugu kawai ya yi d’are-d’are saman gado, wardrobe tabud’e tad’auko night gown d’inta sannan tashiga toilet bayan ta yi wanka saida tasaka rigar sannan tafito, cikin fushi tajawo blanket tashimfid’a k’asa saida takashe hasken d’akin sannan takwanta, haydar batare da ya kalletaba yana dannar wayarsa yace wa yace kikashe min gloves,

Sapna saida takwanta harararsa tayi cikin duhun sannan tace ammah ai naga darene kuma bacci za’ayi,
Haydar yace ni ba yanzu ai zanyi baccin ba dan haka kikunna min.

Sapna tace haba Dan Allah ba ga hasken wayarkaba kana gani da shi wlh idan haske ya yi yawa bana iya bacci, toh kakunna marar haske ta nan saman bedside.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button