DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Banza haydar yayi yacigaba da chart d’insa, ganin haka yasa sapna tayi kwanciyarta.
Kiran sallar asubane yatashi sapna daga baccin da take dakyar tamik’e jikinta sai ciwo yake, kallon haydar tayi da yake kwance yana baccinsa hankalinsa Kwance,
Haushine yakamata ahankali tace ai dole kayi bacci mai dad’i ka haye saman gado ka barni nan toh wlh ban k’ara yarda inkwana k’asa.
Haydar batare da ya bud’e idoba yace mi kikace? Sapna zaro ido tayi tace ba da kai nakeba, dasauri tawuce tashige toilet tad’auro alwallah bayan ta fito haydar yashiga.
Ko da taga sallar saman dardumar bacci yayi awon gaba da ita, saida gari yafara haske sannan haydar yadawo daga masallaci shima yakoma bacci.
Yau ma dai knocking d’in k’ofar da akene yatashesu daga bacci, haydar ne yatashi yafita domin yabud’e, sapna na ganin ya fita tatashi taje tagyara gadon talinke blanket sannan tashige wanka,
Lokacin da tafito d’aure take da towel sai tasaka hijab doguwa ta kusan kai mata k’asa, gaban dressing mirror taje, haydar batare da ya kalletaba yatashi har ya shiga toilet sai kuma yafito yazo inda take tsaye yace bani towel.
Sapna tace shi fane nake d’aure da shi kabari ingama shafa idan nasaka kaya sai inbaka,
Harararta haydar yayi yace nikuma sai inyi tsaye har kigama dallah malama kibani.
Sapna tace toh idan nabaka nikuma fa, ta6e baki haydar yayi yace kizauna hakanan mana I don’t mind, ke wata kunya gareki ko ba kaya akace kiyi yawo ai yi zakiyi.
Sapna cikin 6acin rai tace wai meyasa kake min haka kullum sai kadinga yadamin magana son ranka.
Harararta haydar yayi yace toh ai gaskiya nafad’a mutumin da yasaba bin maza da mata ai ba abin mamaki bane dan kinyi hakan.
Bai jira jin amsar da zata bashiba yawuce yaje yabud’e wardrobe yad’auko sabon towel sannan yazo yashige toilet,
Sapna ranta ya 6aci sosai harda ‘yar kwallarta, wucewa tayi tad’auko kayanta atamfa gown tasaka sannan tadawo tashafa powder da d’an lipstick tana jin haydar ya watsa ruwa taficce daga d’akin takoma parlour.
Haydar bayan ya gama shiri fitowa yayi a parlour saman kujera yaga sapna zaune sai d’acin rai take, yanayin yadda take fushin ya so yabashi dariya ammah yadanne yace malama muje kihad’a min breakfast inyi insamu infita tunda kinja na yi late,
Harararsa sapna tayi tace sai kace ni narik’eka da zakace ninaja kayi late?
Haydar yace toh ai kece kika shige toilet kika dad’e saikace wacce zata canza fata .
Sapna bata tanka masaba fuskarta a d’aure tatashi tabisa a dining tahad’a masa, tana shirin barin wajen haydar yace toh ke ba zaki had’aba?
Sapna cikin fushi tace nak’oshi
ta6e baki haydar yayi yace ke kika sani ai cikinki ne ba na waniba.
Sapna murgud’a baki tayi ahankali tace ai daman ba wani yace cikinka bane.
Haydar cikin 6acin rai yace ke zan 6a66allaki dawa kike?
Sapna tace ba fa dakai nakeba.
Haydar yace toh dawa kike? Tace na fa ce ba dakai nakeba
shareta yayi yacigaba da cin abincinsa ganin haka yasa sapna tawuce takoma parlour tazauna tana ta kumbure-kumburenta.
Haydar yana gamawa yaficce daga gidan, sapna sai da taji tashin motarsa sannan tatashi tace mutum sai jin kan tsiya ga iya ya6a ma mutum magana, tana ta k’uk’uninta tawuce taje tahad’a breakfast tayi, bayan ta gama gyara ko’ina tayi fes k’amshi yagauraye gidan sannan tadawo parlour tazauna.
Wajen k’arfe sha d’aya sapna tana zaune sai ga su hafsat sun shigo, cikin Jin dad’i sapna tatashi takar6i Afnan da take hannun nanny d’inta cike da jin dad’i tace gaskiya naji dad’i da aka kawo min my daughter, bayan sun zauna nan suka gaisa, sapna wasa takeyi ma afnan jefi-jefi suna fira da hafsat,
Murmushi hafsat tayi tace Aunty sapna gaskiya kina da kirki ga kyau ga uwa uba kunya, murmushi sapna tayi tace ammah ai kinfini kyau, zaro ido sapna tayi tace kirufa min asiri wlh kinfini, su mamina suna ta yabon nutsuwarki wlh sai yanzu mukansan yaya haydar ya yi aure, Sapna tace saboda me kikace haka?
Hafsat tayi murmushi tace naga ke kina da kirki ba kamar waccan matar da yayana yata6a yiba,
Gaban Sapna saida yafad’i da mamaki takalli hafsat tace daman ya ta6a aure?
Itama hafsat da mamaki take kallonta tace kina nufi baki saniba? Sapna cikin ranta tace wannan d’an jin kan zai fad’a min, sai kuma chan tayi Murmushi tace a lokacin da yafad’a min ammah a lokacin na d’auka wasa yakemin.
Hafsat tace Ai koma bai fad’a mikiba ba abun mamaki bane saboda yaya haydar miskilancinsa ya yi yawa akwai zurfin ciki wlh wani lokacin ko iyayensa ba zasu iya sanin abinda yake cikinsaba.
Sapna jinjina kai tayi cike da mamaki cikin ranta tace indai wannan mugunne zai aika, gyara zama tayi tafuskanci Hafsat tace toh menene silar rabuwarsa da matarsa?
Hafsat mik’a ma nanny Afnan tayi tace jeki da ita chan part d’in mami kihad’a mata friso tasha, bayan nanny ta fita hankalinta tamaido gaba d’aya wajen Sapna tace zanzu zan fad’a miki komai ammah in briefly.
Lemu tad’auka takur6a sannan tace Alhaji kabir Aliyu shine mahaifinmu su biyu iyayensu suka haifa shi da k’anensa Ibrahim, matar kakanmu Hafsat, k’anwarta itace tahaifi mami da matar baba Ibrahim,
Iyayenmu sunyi karatu mai zurfi sannan daga baya aka had’asu a tare akayi musu aure kasancewar tsakanin daddynmu da daddy Ibrahim ba wata tazara bace sosai. Inda aka had’a mahaifina da Sa’adiya aure shi kuma daddy Ibrahim da sa’adatu
Bayan anyi bikkin mahaifiyata da ‘yar uwarta suka samu ciki tare murna wajen Iyayenmu maza ba a magana, bayan wata tara saida matar daddy Ibrahim tafara haihuwa da kwana ukku sannan mahaifiyata tahaihu duk maza suka haifa dan haka aka d’aga sunan akayi tare, Inda Mahaifina yasa ma d’ansa sunan mahaifinsu wato Aliyu, shi kuma Daddy Ibrahim yasanya ma d’ansa sunan mahaifinsu mami,
yara suka taso a tare kansu d’aya tun daga kansu Iyayenmu basu k’ara ko 6atan wataba k’ara ma Mummy mahaifiyar yaya Ahmad ita ta yi 6ari sau biyu.
Daga nan har sun fitar da rai daga haihuwa sai Allah yaba mami cikina murna wajensu ba a magana bayan wata tara aka haifoni na samu gata sosai daga gidajen biyu kai har ma a wajen yayyen nawa, domin yaya Haydar yana sona sosai
Yaya Haydar da Yaya Ahmad kansu a had’e suke sun taso suna son junansu atare sukayi karatunsu Inda sukaje india sukayi karatu akan likitanci,
Nikuma a nan nayi karatuna, bayan na gama akayi min aure da wani d’an abokin daddynmu mai suna Nura, Ni da Nura mun kasance muna son junanmu. Sai daga baya Allah yabamu haihuwar Fatima muna kiranta da Afnan kasancewa sunan mahaifiyar Nura ce.
Bayan su yaya Haydar sun kammala karatunsu sun dawo daddy yamatsa musu akan sufitar da mata suyi aure, Yaya Ahmad shi yafara samun mata d’iyar k’awar mummynsu ce, ammah yace saidai tare da Haydar za ayi bikkinsu shi ba zaiyi aure yabarsaba,
Yaya haydar wa jen bikkin abokinsane suka had’u da khadija nan suka fara soyayya tsawon shekara d’aya suna tare yaya haydar yana son khadija sosai sannan daga baya akayi bikkinsu.
Khadija tun da tashigo gidan nan kamar mutuniyar kirki muna sonta itama ta nuna tana sonmu, saidai matsalarta guda yawan kawo abokai mata dan kusan kullum gidanta cike yake da mutane saikace gidan bikki, daga baya sai tatsiri wulak’anta danginmu yazamana aka kwaurace ma zuwa gidan yaya haydar, hatta shi kansa yaya haydar sai da takusan fin k’arfinsa dan ma yaya haydar tsaye yake, ammah duk da haka girki batayi saidai yaxo gida yaci, nima kaina bata barniba indai zanzo wajen yayana toh a ranar bamu kwashewa dakyau, idan ko wani yaxo neman taimako wajensa toh wulak’anci iri-iri takeyi har ma wani lokacin tanemi tahana sa saidai a6oye yake bayarwa.