BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Shi kansa yaya haydar da kingansan a lokacin kinsan yana cikin damuwa saboda duk ya rame, kuma ko za a tambayesa abinda yake damunsa baya fad’a kinsansa akwai zurfin ciki.

Wata rana yaya haydar ya fita wajen aiki, ya saba wajen k’arfe biyu ko ukku yake dawowa ranar akayi rashin sa’a yadawo k’arfe sha biyu tun daga parlour yake sallama ammah yaji shuru, dan haka direct yashiga d’akin khadija, abinda idanunsa suka gane masa ya girgizasa Khadija ce da mata biyu kwance saman gado basu ma san shigowarsaba, Hankalinsa ya tashi sosai,

Runtse idanunsa yayi yafara karanta innalillahi wa’innah ilaihiraji’un, Sai a lokacin suka lura da shi cikin tashin hankali duk suka janyo bargo suka lullu6e jikinsu, yaya haydar takaici ya ishesa yakasa ce musu komai saidai hawaye yakeyi, fitowa yayi yadawo parlour yazauna tare da dafe kansa, bai jima da zamaba sai kasu sun fito sanye da kayansu dagudu suka fita sukabar gidan, ahankali yatashi yakoma d’akin khadija kallonta yayi tana ta kuka yace khadija kin ban mamaki miye narageki da shi da zaki sakamin da haka? Ban ta6a zarginkiba saboda banyi tunanin haka daga garekiba, ammah bakomai kije ke da Allah kitashi kije na sakeki saki ukku,

K’ara khadija tasaki tace haydar dan Allah karufa min asiri wlh ina tsoron had’uwata da iyayena, harararta haydar yayi yace watau baki tsoron had’uwa da ubangijinki saidai iyayenki ko? to kitashi na baki minti talatin kifita kibarmin gida,

Hafsat tace kinsan abinda yafito daga bakin khadija da yace mata haka? Sapna da tayi zuru jikinta duk ya yi sanyi tagirgiza ma Hafsa kai,

Murmurshi hafsat tayi tace bud’ar bakinta sai cewa tayi toh saime dan ka sakeni wlh banyi nadamar kamani da kayiba domin matan nan da kake gani sune jin dad’ina saboda namiji baya gabana dan haka rabuwa da kayi dani sauk’i kasamarmin domin daman nagaji da rashin fita yawon bud’e idon da nake garuruwa,

Cikin 6acin rai Haydar yajawo charger d’in waya yafara zura mata ba shi yabartaba saida yaga bata iya motsin kirki sannan yabarta tare da yi mata gargad’i akan kar yadawo yatarar da ita gidansa.

Cikin 6acin rai yaya haydar yad’au motarsa yabar gidan, lokacin nazo gaida su mami nan yake fad’ar sakin da yayi ma Khadija, saida akayi da gaske sannan yafad’i abinda take aikatawa,

Tun daga lokacin aure yafita ran yaya haydar, lokacin ma dayazo da batun aurenki kowa ya yi mamakin hakan.

Sapna cikin ranta tace lallai yanzu naga dalilin da yasa haydar yake hantarata, dogon numfashi taja tace Allah sarki banji dad’in faruwan hakanba Allah yasa tagane gaskiya tadaina.

Hafsat tace Ameen y rabb, ammah daga chan tayi chan mu dai munyi mata nisa saidai idan wasu masu tsautsayin suka jajabu ma kansu ita, mu dai Allah yayi mana tsari.

Sapna murmushi kawai tayi batace komai ba.

Comments
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Page 3⃣4⃣

Kiran sallar azuhur ne da aka fara yasa Hafsat tamik’e tare da cewa Aunty Sapna bari intafi zan dawo da anjima, Sapna marairaicewa tayi tace kai dan Allah mummyn Afnan sai kubarni ni kad’ai, nasan idan kika tafi ba dawowa zakiyi ba.

murmushi Hafsat tayi tace zan je inshirya ne saboda zan je gidan iyayen nura ne, Sapna tace Allah sarki mummyn Afnan ni kad’ai zaku bari,

Dariya Hafsat tayi tace toh ai yayana yanzu zai dawo, Sapna shuru tayi batace komaiba, hafsat cikin wasa tace toh ko zakizo mutafi? Cikin jin dad’i Sapna tace eh wlh Aunty hafsat kinga sai mutafi tare bari inje inshirya, hafsat zaro ido tayi tace rufan asiri kar kija yaya haydar yakakkaryani, ni wasa nake miki kibari nan gaba idan kin fara fita zamuje.

murmushi Sapna tayi tace toh mummyn Afrah sai kin dawo, Allah yakaiku lafiya yamaido mana ku lafiya, Mummyn Afrah tace Ameen.

Bayan ta fita Sapna zama tayi saman kujerar tare da dafe kanta da hannu biyu, tunani take cike da mamaki akan labarin haydar da hafsat tabata, girgiza kai Sapna tayi kwallah tacika mata ido cikin d’aga murya tace daman haydar ya ta6a aure shine bai fad’a min ba, yanzu ya ta6a rayuwa da wata macen kafin ni? chan kuma sai taja tsaki tace akanme nake damuwa da rayuwar mutumin da bai d’aukeni da darajaba ai k’arama da hakan takasance da shi, tashi tayi tashiga bedroom tacire kayanta tashiga wanka, bayan ta fito kwalliya tayi sosai sannan tabud’e wardrobe tad’auko English wears riga da skirt kayan sun kamata sosai kasancewar robane, gyara gashin kanta tayi tatufke, sannan tayi sallar azuhur, bayan ta gama tajiyo ana knocking d’in k’ofa saida tacire hijab d’in sannan tafita tabud’e, lami mai aikice takawo masu lunch,

bayan ta jera saman dining sai tadawo saman kujera tazauna har a lokacin labarin auren haydar ya tsaya mata a rai yawo kawai yake mata a kwakwalwa duk yadda taso takauda tunanin ammah ta kasa, daga k’arshe dai tsaki taja tace miye amfanin tunanin mutumin da yatsaneni mutumin da baya cikin tsarin rayuwata… bud’e k’ofar da akayi ne yasa tamaida kanta ga kallon k’ofar, haydar ne yashiga da sallamarsa, kallo d’aya sapna tayi masa tajanye idonta daga garesa, haydar tun da yashigo yakafeta da Idon, chan kuma ko mi yatuno dasauri shima yakauda fuska, wutowa yayi zai shiga bedroom har yazo bakin k’ofa sai kuma yatsaya batare da ya juyoba yace Ke naga kina shishigema Hafsat toh inaso kisani ko da dawasa kar ki kuskura inga wani abu daga cikin tarbiyar da mukaba Hafsat ya canza saboda hafsat mutuniyar kirkice ba irin kiba, sapna tunda yafara maganar kallon bayansa take cike da mamaki, ranta ya 6aci sosai tace haydar kenan sannunku masu tarbiya gaskiya natayaku murna iyayenku sun iya bada tarbiya tunda gashi sun baku tarbiya maikyau,

haydar juyowa yayi cikin tsawa yace ke! kar ki kuskura kisaka iyayena a ciki, inkuma kika sa su wlh zan sassa6amiki yanzun nan,

harara sapna tawurga masa tace toh ai ni nawan basu bani tarbiyaba kake nufi, inma kana tunanin k’anwarka ne toh inaso kasani k’anwarka batakai matsayin wacce zan 6ataba saboda ni bata gabana da ace ba dan kakawo gidankaba kana ma tunanin daga kai har k’anwartaka zaku isheni kallo? Ni daman za ka taimaka kasakeni da nafi kowa farin ciki saboda kai baka cikin tsarin mazajen da nake….. wani gigitaccen mari da Haydar yad’auketa dashine yasa takasa k’arasa maganar da take cikin bakinta,

Idanuwan haydar suka kad’a sukayi jawur ransa ya 6aci sosai cikin d’aga murya yace ke kina tunanin nima na aurekine saboda ina sonki? Inma kina tunanin hakan toh inaso kicire hakan daga cikin ranki domin yaudarar kanki kike, darajar mahaifiyarki kawai kikaci na aureki, da badan hakaba wlh ko a k’afa aka d’aura minke sai na kwance, dalilin da yasa na ajeki nan gidan saboda idan na auri matar da nikeso ita zan kai chan gidana in zauna da ita kar ma kiyaudari kanki kid’auka kekad’ai zan zauna da ke, sannan magana ta gaba daga gobe zaki kar6i girki kar kisaki ki6ata lokaci baki gama min girkiba, kar kimance da na gargad’eki akan tsafta wlh kar kikuskura kimin k’azanta a gida, sannan innerwears d’ina ke zaki dinga wankesu kar kisaki inga baki wanke min ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button