BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

k’wallah ce cike taf da idanunta tace idan nak’i yi fa, haydar jawota yayi tare da damk’e mata gashin kanta dasauri sapna tarik’e hannunsa da yadamk’e mata gashi, murmushin mugunta haydar yayi sannan yace duk ranar da hakan takasance zan fiddo miki zahirina zakisan wanene haydar. bai jira jin abinda zata ce ba ya wurgata har saida tafad’a saman kujera, yashigewarsa bedroom.

Sapna kife kanta tayi bisa hannun kujera tadinga rusa kuka, haydar ko da yashiga bedroom saman gado yazauna tare da dafe kansa cike da takaicin sapna, chan kuma yamik’e yashige wanka.

bayan ya shirya yafito har lokacin sapna kuka take ko inda take bai kallaba yawuce yaje dining dakansa yayi serving d’in kansa, ci yake ammah kukan da sapna takeyi a hankali yana jinsa har cikin ransa, a k’arshe ma kasa cin abincin yayi yaturesa yatashi yaficce daga d’akin saboda shi a rayuwarsa ya tsani yaji kukan mace.

Sapna saida tayi kuka mai isarta sannan tatashi taje tawanke fuskarta har lokacin tana jin kanta yana mata ciwo duba gashinta tashigayi taga ko ya cire mata gashi, tace mugu kawai wlh sai Allah ya sakamin.

Sapna saida tasha paracetamol sannan tayi kwanciyarta saman gado har saida aka kira sallar la’asar sannan tatashi tayi sallah.

bayan ta gama tadawo parlour har ta zauna sai tatashi tanufi dining tahad’a lunch tad’anci kad’an sannan tatattara kayan takai kitchen,

Sannan taje tatattara masa inner d’insa tawanke tas tana wankewa tana Jera masa Allah ya isa ahaka har tagama.

har tayi sallar isha’i ammah haydar bai dawoba haka tayi ta zama har aka kawo musu dinner d’insu da kamar ba zata ciba ammah tana ganin jalop d’in macaroni ne yasa tad’an zuba kad’an taci sannan tatashi tashiga bedroom.

Saida tayi wanka tayi shirin bacci sannan tahaye saman gado takwanta tace mugu kawai shi yanata hutawa nikuma ya barni k’asa ina kwanciya toh wlh ban k’ara yarda da hakan.

juyi takeyi saman gadon ahaka har bacci yayi awon gaba da ita,

haydar ko da yadawo gidan ganin bata parlour yasa yazauna yafara cika cikinsa sannan yatashi yayi wearing d’in kallo yazauna yanayi sai wajen 11 sannan yatashi saboda bacci da yakeji yashiga bedroom.

yana shiga bedroom d’in ganinta yayi saman gado ta yi d’ai-d’ai haydar ransa ya 6aci sosai yace lallai yarinyarnan na lura nema kike kiraina ni ammah ina zuwa.

bai tashetaba saida yafarayin wanka yashirya sannnan yatafo daidai saitin kanta yabubbugi katifa yace ke tashi, dakyar tabud’e idonta yanayin yadda tabud’e idon da kaganta kasan tana cikin jin dad’in baccin aka tasheta, haydar d’aure fuska yayi yace malama kisafka zan kwanta,

itama sapna d’aure fuska tayi batare da fargaba ko tsoroba tace insafka inje ina? Harararta haydar yayi yace kikwanta inda kika saba kwanciya domin kinsan ba zan iya kwanciya da ke ba ko? sapna d’auke kai tayi daga kallonsa tace nima ai bance kakwanta dani ba ammah wlh ba zan k’ara kwana k’asaba dan nima ko a gidanmu ba a k’asa nake kwanaba indai zaka kwanta saman gadon toh sai kakwanta chan gefen nikuma inkwanta nan kaga sai musa pillow a tsakiyarmu,

Harararta haydar yakumayi yace ke kar kimaidani k’aramin yaro ni kisafka kiban waje kin tsaya 6atamin lokaci.

Sapna ta6e baki tayi tace wlh ba zan kuma kwana k’asaba inkuma kai zaka kwanta toh bismillah ammah nidai nagama.

komawa tayi takwanta tace ka ma ga kwanciyata idan tsarin yayi maka toh inkuma baiyi makaba toh kayi yarda kakeso nidai ina nan.

takaici yacika haydar yama rasa me zaiyi saboda ta kashe masa baki, tsaki yaja yace yarinya inma kina tunanin wani abu toh ba zaki samuba domin ni ba irin mazan da kika saba bibiya bane, banza sapna tayi masa tarufe idonta kamar mai bacci ganin haka yasa haydar yad’auki pillow yakoma parlour saman kujera yakwanta.

Tun da yakwanta juyi kawai yake ya kasa bacci saboda baiji dad’in kwanciyar da yayi saman kujerar ba, har wajen 1am ya kasa bacci ak’arshe dai yatashi yad’auki pillow d’in yakoma bedroom,

Haushi yakamasa ganin yadda sapna tayi d’ai-d’ai tsakiyar gado tana ta sharar baccinta, tsaki yaja yaje yatasheta yace ke tashi, dakyar sapna tabud’e idonta tace malam lafiya ina bacci zaka tasheni, harara yawurga mata yace dallah kimatsa chan, sapna turo baki tayi tare da matsawa gefe, chan k’arshen gado haydar yakwanta yana ta balbala fad’a shikad’ai ita dai sapna bata ma San yana yi ba domin tuni ta koma baccinta, saida yagaji dan kansa yayi shuru, daga k’arshe shima yayi bacci,

Wajen k’arfe ukkun dare juyawar da zaiyi cikin bacci sai ji yayi anmatsesa sosai, Cikin bacci yabud’e idonsa sai ganin Sapna yayi dab da shi k’afarta d’aya ma bisa shi take, duk ta fake wajen sai bacci take hankalinta a kwance, haydar cikin 6acin rai yakaimata duka ak’afar da tad’aura masa, sapna dasauri tabud’e idonta kamar zatayi kuka tace malam me nayi maka zaka dokeni, harararta haydar yayi yace wannan wane irin wawan baccine kikeyi dallah ni janye min k’azamar k’afarki ki matsa chan kin wani zo kin matseni, Sai a lokacin talura da k’afarta da ke jikin haydar sannan tamatsa chan gefe tacigaba da baccinta.

tsaki haydar yayi yakoma yakwanta yace ina ma amfanin irin wannan baccin.

kiran sallar asubane yatashesu saida haydar yafara yo alwallah yafito sannan sapna tashiga tayi.

ko da tagama sallar Saman gado takoma takwanta, haydar ma bayan ya dawo daga masallaci shima komawa yayi yakwanta.

Sapna dayake ta sa ran farkawa da wuri tun k’arfe takwas tafarka, kallon haydar tayi da yaketa baccinsa cikin nutsuwa yanayin yadda yake baccin ya burgeta, zuba masa ido tayi tana kallonsa nan gabanta yashiga fad’uwa, ganin ya motsa yasa tasafka daga saman gadon dasauri, taje tawanke bakinta sannan tashiga kitchen, tsaye tayi tana tunanin me zata had’a musu na breakfast chan dai sai tad’auko doya tafere tadafa, bayan ta dahu sai tasoya da kwai, sannan tadama musu kunun shinkafa, bayan ta gama a chan dining taje tajera, saida tawanke duk abinda ta6ata tagyara kitchen d’in sannan tadawo parlour tagyara nan k’amshi yagauraye gidan,

Tana shiga bedroom tsaye tatarar da haydar yana taje gashin kansa bayan ya fito daga wanka, ko kallon inda yake batayiba taje tana gyara gado, ta cikin mirror haydar yakalleta yace ke baki iya gaisuwaba wai ke ko gidanku babu manya,

Sapna d’ago kai tayi takallesa tace Allah sarki ai ni gidanmu babu manya kuma ba a bani tarbiya mai kyauba dan haka ba zaka samu gaisuwa daga gareniba, Haydar a zuciye yanufo inda take, dagudu Sapna tayi hanyar toilet tashige tamaida tarufe, haydar tura k’ofar yayi yaji ta sa sakata, k’wafa yayi yace idan ke ‘yar iskace zaki fito kisameni zan nuna miki nafiki iskanci.

Sapna tana jinsa dariya kawai take ahankali tace tunda abin naka rainin hankaline toh wallahi na gama kyaleka karaina min wayau, nan tacire kayanta tayi wanka.

Saida ta daidaici lokacin da haydar yabar d’akin sannan tafito d’aure da towel gaban dressing mirror tatsaya tana goge jikinta sannan tafara shafa mai,

Haydar har ya zauna ya fara breakfast sai yatuno da wayarsa da yabari saman bedside, ture plate d’in yayi yatashi yanufi bedroom d’in, tura k’ofar yayi yashiga akan sapna yasafke idonta da take tsaye tana shirin bud’e wardrobe domin tasaka kaya, itama Sapna a tsorace take kallonsa domin gani take kamar dukanta zaiyi akan rashin kunyar da tayi masa d’azun a tsorace tace yaya haydar dan Allah kayi hak’uri wlh na daina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button