DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Lubna tace su sapna ustazai ba a wasa da sallah,
Bata tanka mataba taje tad’auro alwallah tafito, ba tare da ta kallesu ba tace saura hijab,
Murmurshi meerah tayi tace ba ma a iya kallonmu kenan toh bud’e wardrobe kid’auka.
Tana d’auka tafito daga d’akin tadawo parlour tayi sallarta,
Ta dad’e saman sallaya tana addu’a sannan ta tashi takoma saman kujera tazauna.
A chan d’akin meerah takalli lubna tana murmushi tace dear wai ina kika samo wannan cute lady d’in gaskiya ba k’arya ta had’u da alama za ta bada wuta.
Ta6e baki lubna tayi tace bakisan yadda nake fama da yarinyar nan ba wlh ina sonta da yawa ammah ko da sau d’ayane ta k’i amincewa da ni,
Kuma abun bak’in cikin babu abinda nake nema wajenta tayi min gardama sai wannan,
Ni ban ma San ya zanyi ba wlh yarinyar ta shiga raina da yawa.
Kallon mamaki meerah take mata tace lallai dear kin daure dayawa kina tare da wannan yarinyar har zaki iya hak’ura kibarta kina kallonta?
Hmm meerah ba zaki gane bane banso inyi forcing d’inta tazo ta gujeni wlh ban iya rayuwa babu ita
Zan cigaba da binta ahankali nasan wata rana zatozo hannu,
Lallai kam kinada aiki a gabanki lubna,
Hmm meerah kenan.
Charting kawai take hankalinta a kwance, gajiya tayi da chart d’in d’ago kai tayi takalli clock d’in dake jikin bangon d’akin tsaki taja ganin har k’arfe shidda ta kusa,
Karatun alk’ur’ani takunna tasa earpiece a kunnanta tare da lumshe idonta tana saurare kanta taji yana mata nauyi sosai kasancewar indai za ta kunna karatun alk’ur’ani ko kuma zata karanta toh tana jinta cikin wannan yanayin da ita kanta bata san daliliba.
Baccine yafara d’aukarta a hakan maganar mummy lubna ne yakatseta xare earpiece d’in tayi tana kallonta tace me kikace mummy?
Tsaki lubna taja tace sapna kodai baccin ne bai sakekiba har ynz, naga inata magana kinyi shuru.
Am so sowie mummy wlh earpieces ne a kunne na shiyasa.
Ohk, tashi mutafi gida kar muyi dare.
Meerah ce tafito daga bedroom da k’atuwar leda tace muje inyima driver magana yamaidaku tunda ba zaku kwana ba dear.
Kallon sapna tayi tace baby ko ke zaki kwana ne?
Sapna da tunda taga matar takejin haushinta saboda ganinta matsayin matar aure ammah batasan hak’in aureba, d’aure fuska tayi tace a’a gida zan je.
Murmushi meerah tayi tace ko nima tsorona kikeji kar incinyeki,
Bata tanka mataba tawuce tayi gaba.
Lubna takalli meerah tace kinga halin nata ko dear?
Hmm kibarta kawai zata zo hannu zan samo maki mafita nima kinga daga nan sai inbi layi domin yarinyar ta burgeni.
Tabb lallai dear kice kema dai kin k’yasa zan gani dai idan zan iya.
Daidai lokacin suka iso parking space meerah takwala ma driver d’inta kira yataso,
Sallama sukayi tasaka masu ledar a cikin motar sannan suka kama hanya.
Tun da suka d’au hanya sapna ko inda lubna take zaune bata kallaba, ganin haka yasa lubna itama ta shareta har suka isa gida.
Direct d’akin mummy lubna suka wuce toilet sapna tafad’a tad’auro alwallah domin gabatar da sallar magrib ganin lokaci har ya d’an wuce.
Lubna saman gado takwanta tana daddana wayarta.
Ko da sapna tagama sallah kallon lubna tayi taga batada alamar tashi tayi sallar, bata tanka mataba saida tagama addu’a sannan tadawo saman gadon tazauna.
Ahankali tace mummy lubna sallah fa?
Harararta lubna tayi tace miye naki a ciki?
Marairaicewa sapna tayi tace ammah mummy naga sallah fa ita take banbantamu da kafirai mummy hakan bai daceba ace kina musulma ammah baki sallah shin baki tsoron gamuwarki da ubangijinmu kuma. ….
Keh! dakata kar kidameni da wani wa’azinki kije kiyi kedai kabarinki daban nawa daban kar kisaki kice zaki shiga rayuwata harara tawurga mata tace kema ya kamata kigyara rayuwarki kafin kiyi ma wani wa’azi ke kina da tabbas d’in sallarki tana kar6uwa? Mayb ma duk d’aya muke bamuda dambanci, tsaki taja sannan tatashi fuuuuu taficce daga d’aki.
Kwanciya Sapna tayi saman gadon tace Allah gamu gareka…….
kuyi hak’uri da wannan ba yawa
Muje Zuwa
????????????????
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
????????????????
(TRUE LIFE STORY)
Written By ~ Sis Nerja’art
DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA AND SAINAH uMMUN MEENAL
INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….✔
BASED ON 2RUE LIFE
Page 9⃣➖1⃣0⃣
Tashi tayi tajawo hijab doguwa tasanya wadda takaimata har gwiwa jakarta da waya tad’auka tafito daga d’akin,
Falo ta iske lubna zaune tana danna waya,
Matsowa tayi kusa da ita tace mummy lubna zan tafi gida.
Ba tare da ta d’ago ta kalletaba tace kikoma nan zaki kwana,
Ammah mummy ai ban fad’a ma ummana ba
Sai lokacin tad’ago kai takalleta tace sai kikirata ynz kifad’a mata ai ammah babu inda zakije ynz dan haka kikoma ki aje kayanki.
Baki taturo sannan takoma d’akin ta cire hijab d’in tafad’a saman gado cikin 6acin rai tace wai miyasa ake juyani kamar waina ammah banda ikon komai
Wayarta tajawo takira number d’in ummanta bugu d’aya tad’auka.
Sallama tayi mata
Amsawa tayi sannan tace sapna ya baki dawoba har yanzu? Kuma kince min ba kwana zakiyi ba,
6oye damuwarta sapna tayi tace ummana kiyi hak’uri ynz muka dawo ganin dare ya yi ne yasa Aunty lubna tace muwuce gidanta.
Ajiyar zuciya ummah tayi tace toh bakomai sapna tunda kuna tare da lubna, daganan sukayi sallama.
Tashi sapna tayi taje tagabatar da sallar isha’i tana gamawa tayi karatun alk’ur’ani sannan tatashi, toilet tafad’a tayi wanka tashirya cikin nightgown doguwa har k’asa milk colour, hijab tajawo iyakar gwiwa tafito parlour tasamu su mummy lubna zaune suna hira tare da wasu mata biyu bak’in fuska, d’auke kai tayi tanufi kitchen cake guda biyu tad’auko tadawo tawucesu takoma bedroom.
Binta sukayi da kallo teema tata6o d’ayar tace amfah wannan kallonfa da kika bita dashi? Lashe le6enta tayi tace yarinyar ta tafi da imani na gaskiya lubna inason kibani d’ani dariya lubna tayi tace wannan ai ba irin zubinki bace amfah, ta6e baki amfah tayi tace nidai wlh ko ma dai minene ki aramin ita ko da 2hrs ne dariya lubna tak’ara yi ganin yadda duk k’awartasu da takawo musu ziyara tarud’e, tace kije in ta amince miki ai gaki gata inkuma tak’i wlh kar ki matsa mata, barema ba zata amince ba inji teema
Hararanta amfah tayi tace kar kiyimin fata bari dae inje ingwada sa’a ta kudai kujirani kuga.
Tashi tayi ranufi d’akin lubna tura k’ofar tayi tashiga lokacin sapna tana zaune saman 3 seater tana cin cake da fanta bata d’ago kaiba bare taga ko wacece tashigo, inda take amfah tanufo tana tafiya tana karairaya irin nasu na ‘yan duniya, cikin isa tazauna inda sapna take tare da kashe murya tace baby sapna sannunki da hutawa abun ba gayyata?
Ba tare da takalletaba tace yauwa sannu tare da k’ara tsuke fuska.
K’ara matsawa tayi daf da ita kamar zata shige mata tace naga ke kad’aice shine nazo intayaki fira dafatan kina buk’atar hakan daga gareni.
Kallonta sapna tayi a wulak’ance tace no bana buk’ata kitafi kawai nagode, k’ara kwantar da murya Amfah tayi tace haba sapna ya kamata kidamu da wanda yadamu dake nasan kinsan komai kinsan harkar nan, bari inbar 6oye-6oye infito fili infad’amiki ni fa sonki nake kuma zuciyata ta k’wad’aitu dake inaso mudinga kasancewa da juna.