DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Haydar yana ganin ta shige murmushi yayi har saida hak’oransa suka bayyana,abun ya so yabashi dariya musamman sunan da takirasa da shi wai dumkum,girgiza kansa yayi sannan yajuya yalumshe idonsa daman kwance yake yana shirin yin bacci motsin fitowartane yasa yafarka,
Sai wajen k’arfe biyar sannan yamik’e yaficce yabar gidan, Sapna tana jin tashin motarsa taja dogon numfashi tace Alhmdllh yau ‘yan kirkin na bisa kansa tunda baice min komaiba, saida talek’o tatabbatar da bainan sannan tafito takunna kallo tana yi.
Saida tayi sallar isha’i sannan tashiga kitchen tadafa musu indomie da dafaffen kwai, cikin k’aramar kula tazuba ma haydar takai saman dining ta aje, Sannan takoma tad’auko nata tadawo parlour tana ci,
Bayan ta gama takai kitchen saida tawanke duk abinda ta6ata tana fitowa bata dad’e da zamaba tajiyo motar haydar, dasauri tatashi tashige bedroom, toilet kawai tafad’a domin tayi wanka.
haydar ko da yashigo saida yazauna yayi dinner sannan yatashi yashiga bedroom lokacin sapna tana saka kaya, ko kallon inda take baiyiba yawuce yashiga toilet,
Sapna tana gama shiryawa tahaye gado takwanta, Haydar ma ko da yafito shirin kwanciya yayi bayan ya kwanta kallonta yayi yace kar kisaki kiyi mana irin baccin jiya domin na lura ke baki iya bacciba ina ma amfanin irin baccin da kike,
juyawa masa baya sapna tayi cikin ranta tace ka ji dashi dai sarkin ‘yan tsegumi.
Tunda suka kwanta har saida gari yafara haske sannan Haydar yafarka yace subhanallah ashe anyi sallah, sapna ce tabud’e idonta dakyar ganin gari ya fara haske yasa tazare Ido dasauri tatashi zaune tace nashiga ukku ashe har anyi sallah? kallon haydar tayi da yake shirin safka daga gadon tace yaya haydar shine baka tadani domin inyi sallaba har saida gari yayi haske?
Harararta haydar yayi yace nima akace miki na yi sallar? dasauri yatashi yashige toilet, sapna zaune tayi saman gadon tana mamakin irin baccin da sukayi yau har akayi sallah batare da sun saniba.
haydar yana fitowa tatashi tashiga itama tayo alwallah, lokacin da tafito yana sallah dan haka itama bayansa tashimfid’a dardumarta tayi tata sallar,
bayan ta gama saman gado takoma takwanta tabar haydar yana ta lazimi,
wajen k’arfe takwas haydar yatashi yaje yatasheta domin tahad’a masa breakfast,
wajen k’arfe tara da rabi tagama lokacin da tashigo bedroom har ya gama shirinsa, dasauri tashige toilet domin tayi wanka bayan ta fito lokacin haydar ya bar d’akin zama tayi a tsanake tayi kwalliyarta sannan tasaka atamfa java black nd yellow colour riga da zane kayan sun mata cif a jiki, bata d’aura kallabiba tafito parlour, lokacin haydar yataso daga dining zai fita, sapna tsayawa tayi tana kallonsa, shima haydar kallonta yatsaya yanayi saida sukayi kusan minti biyu suna kallon juna sannan sapna tafara janye idonta tace yaya haydar har ka gama breakfast d’in?
Ya mutsa fuska yayi sannan yace eh, har ya juya zai fita sai kuma yatsaya batare da ya juyoba yace yauwa da anjima su Ahmad da matarsa zasu zo dan haka kiyi girki da su idan akwai abinda kike buk’ata toh kifad’a sai inbayar asiyo akawo miki.
Sapna cikin jin dad’in jin ance Ahmad zai kawo matarsa yasa tace babu abinda nake buk’ata muna da komai enough, haydar yace ohk sai nadawo,
Sapna tace adawo lafiya.
agurguje sapna taje tayi breakfast bayan ta gama kitchen tashiga saida tayi wanke-wanke sannan tafara tunanin me zata dafa, chan dubara tafad’o mata cikin jin dad’i tace yauwa rice nd stew zanyi sai cowslow,
farar shinkafa tad’aura sannan tayi ‘yar stew wadda taji nama, saida tahad’a cowslow sannan tahad’a had’ad’en kunun aya.
Wajen k’arfe biyu Sapna ta gama komai, k’ara gyara d’akin tayi takunna turaren wuta nan k’amshi yagauraye ko’ina sannan tashiga tayo wanka
bayan ta yi wanka shiryawa tayi cikin shadda doguwar riga maroon colour wadda tasha aiki da pink d’in zare, kwalliya tayi sosai tafeshe jikinta da turare tana cikin fesawa sai ga haydar ya shigo d’akin tsaye yayi yana kallonta saboda wani irin kyau da tayi haydar cikin ransa yace wannan yarinyar so take tarikitani da salon gayunta, Sapna ganin yadda yatsareta da ido yasa tayi mai fari da ido tace ya dai yaya haydar ya kaganni juyawa tashiga yi tace nayi kyau ko?
Ta6e baki haydar yayi yace ba laifi kin d’anyi, haushine yakama Sapna jin yadda haydar yabata amsa cikin ranta tace wannan mutumin ba a abun arzik’i da shi, batasan lokacin da tace ina ma amfanin irin wannan halin,
haydar isowa yayi kusa da ita yace me kikace? Sapna zaro ido tayi domin bata d’auka maganar da tayi ta fito fili ba, tace magana kaji na yi? Haydar jawota yayi tafad’o jikinsa dasauri Sapna talumshe idonta tana jira taji saukar mari, Haydar zuba mata ido yayi yana kallonta tun daga fuskarta, Sapna jin shurun da yayi ne yasa tabud’e idonta tasafkesu saman fuskar haydar da yake kallon k’irjinta, muryarta tana kyarma tace yaya haydar please kasakeni, Haydar janye idonsa yayi daga kallonta tare da tureta gefe batare da ya kalletaba yace kifito gasunan parlour suna jiranki,
Sapna da itama jikinta duk ya yi sanyi tace toh, Haydar yana fita Sapna tad’auko gyalenta pink tayafa saida tak’ara kallon kanta a cikin mirror sannan tafito, Da fara’a takalli Ahmad da salaha tace sannunku da zuwa yaya Ahmad sai yau muke ganinku? Ni na ma yi fushi tun tuni ba a kawo min Auntyna ba sai yau,
Murmushi Ahmad yayi yace kiyi hak’uri Amarya daman mun barine kusha amarcinku sai muzo, kunyace takama Sapna ta iso tazauna bisa 2 seater d’in da haydar yake zaune samanta,
Cikin jin kunya Sapna tagaishesu suka amsa mata, Salaha tace gaskiya Doctor ka iya za6en mata dole kake 6oyeta, Murmushi kawai haydar yayi,
Salaha tace k’anwata ya bak’untar, Sapna ma murmushi tayi tace Alhmdllh, Ahmad yace amarya me kikeba abokina naga har ya yi k’iba, harara haydar yawurga masa yace banson iskanci daman chan ai haka nake,
Dariya suka sa gaba d’ayansu sannan Salaha tace haba sweetheart kaima dai ka san aure rahamane kaima ai saida mukayi aure sannan kak’ara k’iba, Kallonta Ahmad yayi yace to tunda na ta6o mutumin naki ai dole nikuma kitona min asiri.
gaba d’ayansu sukasa dariya haydar yace ahto kaima ka san Salaha ta wajenace,
Ahmad yace eh naga alama ai saisa ni kuka turani rana kukuma kuka shige inuwa, nima ai yanzu ga k’anwata nan Sapna nasan tana tare da ni,
murmushi Sapna tayi tace aikam dai ina bayanka yayana,
Sapna kallon haydar tayi tace yaya haydar abincin fa?
haydar mik’ewa yayi tsaye sannan yakalli su Ahmad yace kutaso muje muci lunch,
gaba d’ayansu suka tashi suka nufi dining, Sapna ce tayi serving d’in kowa sannan tazauna itama,
tunda suka fara cin abincin salaha da Ahmad santin abincin kawai suke,
Sapna satar kallon haydar tayi taga yana ci yana yamutse fuska, cikin ranta tace ka ji dashi ko mak’iyina ya san girkin nan ya yi dad’i.
Bayan sun gama sapna tatattara kayan takai kitchen saida tawanke sannan tadawo ta taddasu a parlour zaune suna ta hira bisa kujerar da salaha take zaune taje tazauna,
kallonta salaha tayi tace k’anwarmu masha Allah kedai kunyarki har ta yi yawa ko bak’untarce har yanzu bata sakekiba?
murmushi sapna tayi tace a’a Aunty,
Haydar kallon Ahmad yayi yace abokina taso muje masallaci naji ana kiran sallar la’asar idan mukayi sallah sai mud’an fita, salaha tace yauwa ai k’ara kutafi kubamu waje, Ahmad yace to ka ji abokina korarmu ake saboda za ayi gulmarmu, dariya salaha tayi tace ai ko zanyi gulmar kowa ai banda ta doctor saboda shi nahannun dama na ne, Kawai dai kutafi munaso mud’an tattauna ne, Haydar kallon sapna yayi da tasadda kanta a k’asa tana ta murmushi sannan yamaida kallonsa ga salaha yace shikenan k’anwata ai nasan ko kowa zaiyi gulmata toh banda ke,