BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

salaha tace haba ya ma za’ayi infara nida nake tare da kai.
Ahmad harararta yayi cikin wasa tace kinji da fadancinki indai natashi k’ara aure ai bai isa yahananiba.

Haydar yace ai saidai idan ban raye zakayi ma k’anwata kishiya domin duk inda zakaje neman aure sai na shiga na fita na tarwatsa maganar,
Ahmad yace mugu wlh nasan zaka aika.

dariya sukayi gaba d’ayansu sannan Ahmad yace toh mudai muntafi naji ana shirin kabbara sallah, Salaha tace toh sai kun dawo

ita dai sapna batace komai ba d’ago kai tayi suka had’a ido da haydar, janye idonsa yayi daga kallonta sannan yaficce.

bayan sun tafi Salaha kallon Sapna tayi tana murmushi tace k’anwata taso muyi sallah,

sapna batayi musuba tatashi suka shiga bedroom bayan sunyi sallah suka dawo parlour suka zauna, salaha kallon sapna tayi tace K’anwata wane irin zama kukeyi da haydar dan tunda mukazo ina lura da yadda kuke takun sak’a a tsakaninku kamar baku ma magana sosai ko ma ince sai kace wad’anda akayi ma auren dole ba auren soyayya kukayiba,

murmushi sapna tayi tace bakomai Aunty salaha wlh lafiya lau muke zaune,

salaha kallonta take fuskarta d’auke da mamaki tace ammah kuma naga baku tattalin juna? ni bance dole sai naji sirrin aurenkuba koda na san halin haydar miskiline na sosai ammah inaso kisan wani sirri shi namiji yana son kulawa Indai kina tattalinsa kina tsafta ladabi da biyayya girki, sannan kuma aduk lokacin da yabuk’aceki kina basa had’in kai, ki iya fad’a masa lafazi mai dad’i, ya kamata ace kin iya k’issa da tafiyar Jan hankali, kinuna kinfi sa son yakyautata ma danginsa,

toh wlh zaki moresa sosai, zakiga yadda zai susuce miki, zai koma miki kamar akalar rak’umi sai yarda kikayi da shi, za a dinga ganin kamar kin shanyesa, wasuma zasu fara tunanin kamar asiri kikayi masa nan ko ba asan ba boka ba malam iya zaman aurene kawai,

sapna cike da mamaki take kallon salaha cikin ranta tace anya harda irin su yaya haydar?

Salaha kamar ta shiga zuciyar sapna murmushi tayi tace k’anwata Indai kika d’ore da haka duk wannan girman kan na haydar sai ya ajesa ya biki, kigwada kigani dakanki zaki ban labari.

Ni wlh kin ban mamaki a matsayinki na ‘yar boko ban d’auka zan zo inganki hakaba na d’auka zanga wayewarki ta wuce haka, na san kunyace take d’awainiya dake ya kamata ki aje kunyarki gefe kitattali mijinki inkuma ba hakaba wlh ina nan da ke wata mace zata sace zuciyar haydar.

sapna saida gabanta yafad’i dasauri tad’ago kai takalli Aunty salaha, gyad’a mata kai Aunty sahala tayi tace tabbas hakane domin irinsu haydar mata dayawa suke burin susamu ke tun kafin haydar yayi aure wasu ‘yan matan har gida suke binsa suna rok’onsa yasosu wani lokacin har gidana suke zuwa susamu mijina Ahmad suyi masa maganar haydar, dan ma Allah ya taimaka haydar mata basu gabansa wlh da ace wani mai neman matan ne da matan da zai 6ata suna da yawa toh sai Allah yasa shi ba halinsa bane haka.

sapna cike da mamaki take kallon salaha jikinta ya yi sanyi sosai, salaha tace kuma kiyi duba da aikin da yake zuwa kinsan dai dole yaduba patients mata, dan haka ya kamata ki aje kunya kitattali mijinki kituna masa TATTALIN SO

Sapna kogon tunani tafad’a cikin ranta tace taya zan 6ulloma al’amarin haydar shi da baya sona baya k’aunata anya k’iyayyar da yake min zata iya zama soyayya alhali ina ganin tsanata a cikin k’wayar idanuwansa? musamman ma da yasan halina yasan wacece ni, anya zai yarda yayi rayuwar aure da ni?……..

Toh nima dai kaina ban san amsar tambayarkiba sapna ammah ga fan’s d’inki nan sai subaki amsa

Comments
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Masoya nagode sosai da kulawarku da addu’o’inku agareni, wad’anda ban samu damar maida masu reply ba kuyi hak’uri nima ba dan naso hakanba ammah kar kudamu a kowane lokaci ana tare, I hrt u all????

Page 3⃣6⃣

Aunty salaha girgiza sapna tayi da tatsunduma cikin kogon tunani, firgit sapna tayi takalli Aunty salaha, murmushi Aunty salaha tasakar mata tace tunanin me kikeyi sapna?

Sapna shuru tayi tare da sunkuyar da kanta k’asa, Aunty salaha batadamu da shurun da sapna tayiba tacigaba da cewa kikwantar da hankalinki sapna kigwada yadda nace miki insha Allahu zakiji dad’in zama da haydar,

Sapna idanuwanta suka cika da kwallah batasan lokacin da tayi su6ul da bakaba tace wannan mugun?

Dariya Aunty Salaha tayi tace a’a sapna kidaina cemasa mugu baki fahimci wanene haydar bane ammah nan gaba dakanki zakice haydar ba mugu bane.

Aunty Salaha handbag d’inta tajawo tad’auko wata roba k’arama mai murfi tamik’a ma sapna tace my k’anwa ga wannan kid’an fara amfani da shi ba sai na fad’a miki sirrinba na tabbata nan gaba kema dakanki zaki nema,

murmushi sapna tayi tace Aunty Salaha ni ai bana Amfani da magunguna.

dariya Aunty Saliha tayi tace kar kidamu wannan baida illah nima ai bana amfani da kowane magani wannan ma dandai wata tsohuwa ce ‘yar maiduguri take had’o min shi, had’in su zuma ne akayi amfani dasu, d’an sha kiji,

Sapna murmushi tayi kamar ba zata sha ba sai kuma taga ba zata iya yi ma Salaha musuba dan haka tabud’e tunda takafa kai saida tasha kusan rabin robar,

zaro ido salaha tayi tace Sapna daga kid’and’ana shine kika sha dayawa? dariya sapna tayi tace Aunty Salaha akwai dad’i wlh , dariya salaha tayi tace to ai kad’an ake sha zakiga amfaninsa nan gaba da kanki zaki nema akawo miki yanzu dai jeki ki adana a d’aki,

tashi sapna tayi takai bedroom ta aje nan tadawo tazauna suka cigaba da hira Aunty Salaha tana ta k’ara Koyamata yadda zata kula da tattala mijinta itadai Sapna abun dariya kawai yake bata.

atare suka shiga kitchen sukayi girkin dare bayan sungama sukaje suka jera a dining sannan sukayi sallar isha’i,

Sai wajen takwas da rabi sannan Haydar da Ahmad suka dawo gidan, nan sukayi musu sannu da zuwa daga nan suka nufi dining nan Sapna tayi serving d’in Haydar ita kuma Salaha tayi Serving d’in Ahmad sannan suka zauna suna cin abincin suna hira sama-sama ahaka har suka gama, Sapna da Aunty Salaha suka kwashe kwanikan suka kai kitchen suka gyara wajen sannan suka dawo parlour,

Ahmad kallon salaha yayi yace my ya kamata mutafi gida, Murmushi Salaha tayi tace toh Sweetheart.

Marairaicewa Sapna tayi tace kai dan Allah Aunty salaha kubari sai da anjima, Dariya salaha tayi tace kokuma mukwana nan ko?

Cikin jin dad’i Sapna tace eh wlh Aunty kinga sai mukwanta nan parlour su kuma sukwana a bedroom, Haydar kallon Ahmad yayi sukayi murmushi,

itama salaha murmushi tayi sannan takalli Ahmad tace ai ni bana iya bacci batare da sweetyna yana kusa da ni ba.

Shuru sapna tayi sai kuma chan takalli Haydar tace yaya haydar toh mubar musu bedroom mu sai mukwanta nan parlour ko?

Haydar dariyar da yake shirin yi ce yadanne sannan yace eh haka za’ayi kawai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button