BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Page 3⃣7⃣

Haydar shima zama yayi saman gadon hannu yakai yad’agota yace sapna kidaina cewa haka wlh ni masoyinkine na hak’ik’a duk abinda nake miki wlh ba a son raina nake miki ba son kine sila trust me.

sapna cikin tsawa tace enough Haydar! Please katashi kaban waje inba so kake tsanarka tak’aru a cikin zuciyata ba,
Haydar kamar zaiyi kuka yace please sapna ki saurareni
sapna cikin tsawa tace nace katashi kaban waje,

Haydar mik’ewa yayi jiki ba k’wari yana tafiya kamar wanda k’wai yafashe mawa a ciki saida yakai bakin k’ofa sannan yatsaya yajuyo yakalli sapna murmushin takaici yayi yace sapna ko da ace ba zaki yarda da ni ba ina so kisani abinda yake cikin zuciyata ne nafad’a miki, ina sonki kuma na tabbata akwai ranar da zaki gane cewa ni masoyinkine na gaskiya, yana gama fad’ar haka yajuya yaficce daga d’akin ko breakfast bai tsaya yi ba yaficce yabar gidan.

Sapna sai da tasha kukanta sannan tatashi tawanko fuskarta tafito parlour, zuwa tayi tahad’a breakfast tad’anci sannan tagyara ko’ina, bayan ta gama saman kujera takoma takwanta, tsaki kawai take duk yadda taso tacire abinda Haydar yayi mata a ranta ammah ta kasa, tana nan kwance har aka kira sallar azuhur sannan tatashi takoma bedroom, saida tayi wanka sannan tad’auro alwallah bayan ta fito gaban dressing mirror tazauna tayi kwalliya sosai sannan tatashi tanufi wardrobe ta dad’e a tsaye tana tunanin kayan da zata sanya a k’arshe dai tad’auko English wears riga da wando tasaka, kayan sun kamata sosai, tufke gashin kanta tayi sannan tasaka hijab doguwa tayi sallah.

bayan ta gama parlour tadawo takunna kallo sannan tazauna tana yi cike da jin dad’in ana best film d’inta a bollywood, tana cikin kallon taji tsayuwar motar haydar, nan fara’ar da take fuskarta taragu,

haydar bai shigoba saida yabiya part d’in mami suka gaisa, yasa aka zuba masu abinci a kula sannan yadawo part d’insu da sallamarsa yashigo d’akin, sapna ko inda yake bata kallaba, haydar ganin tana ta had’e rai ne yasa yawuce dining ya aje kular da take hannunsa sannan yadawo inda take kwance, daga gefen fuskarta yazauna yace baby ko d’an welcoming d’in nan ba zan samuba? shuru sapna tayi takyalesa tacigaba da kallonta, haydar murmushi yayi yace har yanzu fushin akeyi da ni? dan Allah kihuce hakanan hannu yakai yashafi fuskarta, sapna wani yarrr taji dasauri tajanye fuskarta, ahankali haydar yace baby har yanzu akwai sauran zazza6in kinsha magani,

Sapna cikin tsawa tace dan Allah malam kakyaleni sai damuna kakeyi da surutu kabarni inyi kallo mana, ba za ayi welcoming d’in nakaba juya masa baya tayi,

ganin haka yasa haydar yamik’e yashige bedroom yana mamakin masifar sapna da kwata-kwata ta kasa fahimtarsa,

bayan ya yi wanka ya shirya yafito har lokacin kwance take yarda yabarta komawa yayi wajenta yace sapna kitaso muje muyi lunch, shuru tayi masa,

haydar yace ko nan zan kawo mana muci? cike da gadara sapna taja tsaki tace bana ci kaje kaci haba,

haydar ya’ida k’ulewa ta6e baki yayi yace ai cikinki ne, dan kinga ina lallashinki shiyasa kike yadda kikaga dama kar dai kimance da taimakonki nayi da ban taimaka mikiba ai da baki kai ynz ba.

sapna harara tawurgamasa tace ai bani nace kataimaka min ba ai da ka bari na mace tunda daman ba sona kakeba, kai dai kawai daman abinda kakeso kenan kasamu kuma ka samu hankalinka ya kwanta.

haydar dariyar rainin wayau yayi yace kar kiyi tunanin kina da abinda zan so a jikinki, har yanzu ke yarinyace shar,

sapna a harzuk’e tamik’e tsaye tace eh naji ni yarinyace ammah ahaka jiya ba ko kunya aka dinga santina har da sumbatu, me ma kace?

haydar ransa ya 6aci sosai yace ke zan6a66allaki ba dan kinga wani abu ya shiga tsakaninmuba kinemi ki raina niba, me kike tak’ama da shi?

sapna dariya tayi tace eh naji d’in abinda ake k’wak’wa shi nake tak’ama da shi? kai dai kawai borin kunya kakeyi, girma dai ne ya riga da ya zube,

haydar cikin 6acin rai yad’aga hannu zai mareta, cikin zafin nama tagocewa, dagudu sapna tawuce tashige bedroom tamaida k’ofa tarufe tana dariya,

haydar cike da takaici yazauna bisa kujera tare da dafe kansa ahankali yace meyasa na aikata hakan da ace ban kwanta da itaba ai da bata rainani ba haka, miyasa nabayyana mata sirrin da yake cikin raina? haushin kansane yaji, tsaki yaja yace ai laifina ne DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA AI SHI RUWA KAN DOKA

ya dad’e a zaune sannan daga baya yatashi yanufi dining yazuba abinci yaci, bayan ya gama yadawo saman 3 seater yakwanta tare da kunna kallo yana yi ammah kwata-kwata hankalinsa ba a wajen kallon yakeba tunanin sapna kawai yake,

Sapna tunda tashige bedroom tamaida tarufe saman gado takoma takwanta cike da jin haushin haydar, ga yunwa da takeji.

chan dai da taga ba kanta yunwar ta addabetane yasa tatashi tabud’e k’ofar ahankali talek’a ganin haydar a kwance yasa tafito, haydar ko inda take bai kallaba ganin haka yasa tawuce tanufi dining tazuba abinci taci, bayan ta gama gyara wajen tayi sannan tadawo saman kujerar da take opposite d’insa tazauna itama tana kallo,

kallosa tayi taga idanuwansa a lumshe suke tsaki taja tace mutum dan rigima ba kallon yaleba ammah har da canza min channel, tashi tayi talalla6a taje za ta zare remote d’in da yake a hannunsa saboda ta yi tunanin bacci yake, tsaki taja tace ji dan Allah yadda yawani hakimce yana bacci mutum sai iya yin tsiya, tana rik’e remote d’in haydar yabud’e idonsa,

tsorata sapna tayi tazaro ido shirin juyawa take taruga haydar cikin zafin nama yajawota tafad’o jikinsa, gaba d’ayansu saida sukaji wani irin shock, haydar d’aure fuska yayi yace maimaita me kikace,

sapna marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace ni fa ba da kai nakeba,
harararta haydar yayi yace akwai wani mutum ne bayan mu biyu a d’akin nan da zakice ba da ni kikeba?

sapna so tayi tatashi daga jikinsa ammah ta kasa saboda rik’on da yayi mata, turo k’aramin bakinta tayi tace dan Allah yaya haydar kasakeni,

haydar yace ai sai fa kin maimaita abinda kikace sannan zan kyaleki inkuma ba hakaba yanzu zanyi maganinki domin naga kin raina ni dayawa,

zaro Ido sapna tayi tace kai yaya haydar yaushe naraina ka? haydar cikin fushi yace au k’arya ma nake miki ko? aikam yanzu zanyi maganinki,

sapna ahankali tace saidai muyi maganin juna, bata d’auka ya ji ta ba saidai ji tayi ya ce haka kikace ko?

Sapna harararsa tayi tace yoh me kaji na…. bakinsune da yahad’e waje guda yasa takasa k’arashe maganar da take cikin bakinta, turesa tashiga yi ammah takasa, ganin haka yasa haydar yacanza salo nan da nan yarikitata tafita hayyacinta takasa ko motsi, hannunsa taji yana yawo a cikin rigarta tunowa tayi da wahalar da yabata, dasauri tabuge hannunsa tare da zare bakinta haydar da idanuwansa suke lumshe yabud’e tare da maida hannuwansa cikin rigarta, sapna idanuwanta sukayi rau-rau da kwallah cikin muryar tsoro tace dan Allah yaya haydar kadaina,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button