DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

murmushi haydar yayi yace kefa kikace saidai muyi maganin juna toh kibari muyi, sapna ganin yana neman rabata da rigarta yasa tafashe da kuka tace dan Allah kayi hak’uri ban fa warkeba, ta6e baki haydar yayi yace ina ruwana da rashin warkewarki yau sai nayi maganin wannan bakin naki da baya mutuwa, kinga sai kiyi jinyar gaba d’aya,
Sapna cikin kuka tace dan Allah kayi hak’uri ba zan k’araba wlh har yanzu jikina ciwo yake min.
dariya haydar yayi yace ai ban d’auka zaki karaya dawuri hakaba ashe ke k’aramar marar kunyace, tureta haydar yayi tare da komawa yakwanta yalumshe idonsa,
dasauri sapna tamik’e tsaye tana gyara rigarta, hawaye suna zuba daga idanunta, kallon haydar tayi tamurga baki ahankali cikin mak’oshinta tace mugu kawai,
haydar baiji abinda taceba jin tana gunani yasa yabud’e idonsa yace me kika ce? dagudu sapna tabar wajen tana mamakin kunnuwan haydar da suke saurin jiyota, bedroom tashiga,
haydar tsaki yaja yace wannan yarinyar na lura da ita bakinta baya mutuwa ammah zamu had’e, mik’ewa yayi tare da d’aukar key d’in motarsa yaficce daga gidan,
sapna har kayi sallar isha’i batasa haydar a idontaba dan haka tatashi tashiga kitchen tadafa ‘yar indomie daidai cikinta taci tace kaikuma idan kadawo kasan abinda zaka ci,
wajen k’arfe tara tagama shirin baccinta tahaye gado tayi kwanciyarta, takaici duk yacikata ganin haydar har lokacin bai dawoba, tsaki taja tace wa ma yasani ko yana can wajen ‘yan matansa gabantane yashiga dukan ukku-ukku duk sai taji ba dad’i duk yadda taso tayi baccin ammah takasa juyi kawai take,
Jin tsayuwar motar haydar yasa tad’aga kai takalli agogo taga har k’arfe goma ta yi haushi yakamata tamaida idanunta tarufe,
haydar ko da yashigo baiyi mamakin ganin har ta kwantaba saboda ya santa wani lokacin da saurin bacci,
shirin bacci yashiga yi bayan ya gama fita yayi daga d’akin yanufi dining ammah bai tarar da komaiba, dan haka yadawo bedroom din tsaye yayi yana k’arema sapna kallo murmushi yayi sannan yace ke meyasa baki girka min komaiba,
shuru sapna tayi tare da k’ara lumshe idonta, haydar yace na fa san ba barci kikeba dallah malama kitashi,
ganin har lokacin batada niyar tashine yasa haydar yakai hannu yana shirin janye bargon da tayi rufa da shi, dasauri sapna tabud’e idonta tare da k’ara rik’e bargon, d’aure fuska tayi tace malam wai lafiya zakazo katasheni ina bacci?
harara haydar yawurga mata yace ahaka zakice bacci kike? meyasa baki ajemin abinciba?
sapna rau-rau idanuwanta sukayi da kwallah tace ‘yan matan da kaje wajensu su basu bakaba?
haydar da mamaki yake kallon sapna kishinsane k’arara yagani cikin idonta, abin yaso yabashi dariya ammah yak’unshe dariyar yace toh ya zanyi tunda ita bata baniba ai ba zan rok’etaba, toh mema zaisa indamu baccin ina da wadda zata girkamin a gida. kikwantar da hankalinki idan mukayi aure ai zata dinga yimun,
Sapna saboda takaici kamar tad’aura hannu bisa kai takwala ihu,
haydar murmushin cin nasara yayi yace yanzu dai tashi kije kisamarmin abinda zanci wlh yunwa nakeji,
sapna harararsa tayi tace ba zan girkaba sai kakirata ita tazo tayi maka ita, dasauri takoma takwanta tare da jawo blanket d’in tarufe har fuskarta, hawaye ne suka shiga tsiyaya daga idonta
haydar murmushi yayi yace shikenan ni bari inje insamu abinda zan ci, nasan da itace da bazata barni da yunwaba
sapna tana jin fitarsa kamar daman jira take nan tafashe da kuka tana jin zuciyarta tanamata zafi maganganun da haydar yayi mata suna mata yawo a cikin kwalwarta, ahankali tace shikenan ya cuceni ya rabani da budurcina kuma yanzu aure zaiyi, saida tayi kukanta mai isarta sannan tayi shuru.
haydar ko da yafita kitchen yaje yaci sa’a akwai ruwan zafi nan yahad’a coffee yadawo parlour yana sha yana ma sapna dariya ahaka har yagama yatashi yakoma bedroom,
shima gadon yahau yakwanta yana jin sapna tana ta juyi tana tsaki k’asa-k’asa abinma yaso yabashi dariya yashareta ahaka bacci yayi awon gaba da su
da asuba kusan tare suka tashi sapna saida tajira haydar yayi alwallah yatafi masallaci sannan tashiga tayo,
bayan ta idar da sallah saman gado takoma takwanta saboda har lokacin baccin bai ida sakintaba kasancewar batayi bacci da wuriba, bata dad’e da kwanciyaba shima haydar yadawo yakwanta.
basu suka farkaba sai wajen k’arfe goma, sapna ganin haydar ya shiga wankane yasa tatashi tagyara d’akin tazauna jiransa yafito domin itama tashiga.
ko da yafito taso tabashi dariya ganin har lokacin fushi take, ko kallon inda yake batayiba tawuce zata shige toilet,
haydar rik’o hannunta yayi yace baby wai meyake faruwane kiketa fushi ko breakfast din ba zan samuba kike nufi ko duk kishine?
sapna harararsa tayi tace Allah yasauk’e inyi kishinka ai abinda akeso shi ake kishi ba Wanda ba a soba, dariya ce takusan kufce masa yace haba baby wani lokacin ma ana kishin abinda ba a so, ammah kikwantar da hankalinki very soon zanyi aurena sai intare da amaryata a sabon gidana kinga ke sai kiyi zamanki nan hankalinki akwance tunda daman ba sona kikeba
Sapna ta cika tayi fam kamar tafashe, kasa magana tayi domin tasan da tayi magana to kuka zai biyo baya kuma batason haydar yazargi wani abu game da ita, dan haka fisge rik’on da yayi mata tayi tawuce tashige toilet.
haydar murmushi yayi yace sapna kenan abinda kike 6oyewa azuciyarki idanuwanki suna bayyanamin komai, cikin jin dad’i yayi sauri yashirya, wata leda ce yad’aura mata saman gado da d’an short note sannan yaficce yabar gidan ganin har 11 ta kusa.
sapna ko tunda tashiga toilet shower takunna nan tacigaba da kuka dak’arfi zuciyarta har zafi take, kishin haydarne take ji ya mamaye zuciyarta cikin kuka tace meyasa nake kishinsa alhalin ba sonsa nakeba? k’ara fashewa tayi da kuka tace Allah sai ya saka min, saida tayi kuka mai isarta sannan tayi wanka tafito idanuwanta duk sun kumbura,
ganin haydar baya d’akin yasa tazauna tatsara kwalliyarta bayan ta gama taje tabud’e wardrobe tad’auko English wears riga da skirt tasanya, rigar ja skirt din kuma bak’i, tatufke gashin kanta sannan tafeshe jikinta da turare
juyowar da zatayi sai alokacin takai kallonta ga ledar da take saman gado, da mamaki take kallon ledar, takawa tayi tanufi wajen ledar, zama tayi bakin gadon sannan tad’auki ledar, takardar da take k’asan ledarne tagani tayi sauri tad’auka tana dubawa taga yasa baby ga wayanan kicigaba da amfani da ita, kikiyaye kar kisaki inga number d’in k’awa ko wani, ummah kawai na’amince kidinga waya da ita, dafatan za’a huce daga fushin da ake dani, ni natafi wajen aiki dafatan zan samu lunch idan nadawo
your’s haydar forever
ta6e baki sapna tayi tace wani aiki kaidai kawai kace ka tafi wajen ‘yan matanka, dasauri tabud’e ledar taciro wayar daga cikin kwalinta iPhone 7 ce cike da jin dad’i tace wow gaskiya wayannan ta burgeni, chan kuma sai tayi murmushi tace hmm tunda ka gama wulak’antani son ranka ai dole kaban waya ammah zan kar6ane kawai saboda inaso indinga jin ummana ammah da badan hakaba da namaida maka kayanka banso,
cike da jin dad’i tatashi taje tajona wayar caji, sannan tafito tanufi kitchen tea kawai tahad’a tasha sannan tagyara ko’ina,
zaune take tana kallo jin ana knocking d’in k’ofane yasa tatashi domin taje tabud’e, tana bud’ewa taga hafsat rik’e da afra cike da jin dad’i tace oyoyoo mummyn afrah hannu takai ta’amshi afra sannan suka zo suka zauna, sapna tana murmushi takalli hafsat tace mummyn afrah ai da har nayi fushi kwana biyu baki lek’oniba, itama hafsat murmushin tayi tace ayya kiyi hak’uri matar yaya wlh sai jiya nadawo kuma gobe ma zan koma gidana, sapna tace kai dan Allah? hafsat tace ai namad’auka bro ya fad’a miki.