BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

ta cikin mirror d’in haydar yaga tana harararsa murmushi yayi tare da takowa inda take, sapna bata ankaraba sai ji tayi ya rungumeta ta baya,

sapna wani irin shock taji dasauri taruntse idonta, cikin kunnenta taji yana rad’a mata magana ahankali, muryarsa tatsinkayo yana cewa baby menayi miki kike fushi da ni?

sapna ture hannunsa tashiga yi ammah takasa kwacewa daga rungumar da yayi mata, haydar hannu yakai yana shirin kwance mata d’aurin towel d’inta,

sapna dasauri tarik’e towel d’in tare da bud’e idonta tace malam miye haka ni kasakeni, murmushi haydar yayi yana kallonta tacikin mirror, itama kallonsa takeyi tamurgud’a masa baki, baice mata komaiba kissing d’in wuyanta yashiga yi hannunsa na rik’e da k’ugunta, sapna lumshe idonta tayi tana amsar sak’on da yake aika mata bata ankaraba sai ji tayi ya cire mata towel d’inta,

dasauri taturesa da dukkan k’arfinta, jikinta sai kyarma yake tajawo towel d’inta tamaida, nan tabar haydar tsaye tawuce tanufi wajen kayanta.

haydar dakyar yaja k’afa yafita yabar d’akin ko da yaje parlour saman kujera yazauna tare da dafe kansa yana maida numfashi saida yasamu nutsuwa sannan yatashi yanufi dining kad’an yad’anyi breakfast d’in yatashi yaficce daga gidan.

Sapna dakyar tashirya takoma saman gado tazauna cike da jin kunyar haydar ga wata kasala da yak’ara sakarmata, saida taji tashin motarsa sannan tafito daga bedroom d’in.

bayan ta gama breakfast tashiga kitchen tafara shirin girkin rana, tuwon shinkafa da miyar ganye tayi sannan tahad’a had’ad’en kunun aya.

cikin kulolinta tad’auko wasu set masu kyau tazuba ma su mami,

wajen 1:30pm ta gama komai agurguje taje tayo wanka tashirya cikin atamfa riga da skirt ash nd brown colour, saida tafarayin sallah sannan tad’auko hijab brown har gwiwa tasaka,

kitchen taje tad’auko basket d’in da tazuba ma su mami tafito tarufe part d’inta tanufi wajen su mami.

lokacin da tashiga da sallamarta lokacin su mami da hafsat suna zaune a main parlour suna kallo, da fara’arsu suka amsa mata hafsat tataso tana mata oyoyo tare da kar6ar basket d’in da yake a hannunta,

sapna cike da jin kunya taduk’a tagaishe da mami, mami tana murmushi ta amsa mata tare da tambayarta ya suke?

sapna k’ara sunkuyar da kanta tayi tace Alhmdllh, mami tace ya bak’unta kuma? murmushi sapna tayi batare da ta ce komai ba,
mami ma murmushi tayi tace sapna kisaki jikinki nan ma gidane, sapna ahankali tace toh mami

mami tace tashi kizauna saman kujera mana, sapna tace mami nan ma yayi,
mami tace a’a sapna tashi kizauna,
sapna batayi musuba tatashi tazauna kusa da hafsat,
kallonta hafsat take tana murmushi tace matar bro ina wuni? sapna ma murmushi tayi tace ina wuni mummyn afrah?
hafsat tace lafiya lou y bak’unta?
murmushi sapna tayi batare da ta ce komai ba.

hafsat kaima mami kular tayi, mami cikin fara tace masha Allah mungode sosai, Allah yabada lada, hafsat tashi taje tad’auko plate tazo tazuba tace wow delicious food gaskiya matar yaya kinyi k’ok’ari yau abincinki zanci,
murmushi sapna tayi,

daganan tazauna suna ci suna hira, sapna ganin mami hankalinta yana wajen kallone yasa tasaki jikinta suna hira sosai da hafsat, mami kad’an kad’an take jan sapna da hira.
daga baya hafsat tajata takaita d’akinta sapna mamakine yakamata sosai ganin tsarin d’akin hafsat gashi da aurenta ammah har d’aki gareta cikin gidansu, nan tatayata ta’ida shirya kayanta.

bayan sunyi sallar la’asar ne tayi bankwana da su, mami godia tayi ma sapna sosai sannan hafsat tarakata, hafsat kallonta tayi tana murmushi tace toh mudai daga nan zamu wuce gidanmu sai inkinfara fita my bro zai kawo minke yace, sapna duk sai taji ba dad’i nan tace toh Aunty hafsat nagode sosai Allah yakiyaye hanya sai munzo, ashafa min kan afrah naga tunda nazo bacci take bata farkaba, murmushi hafsat tayi tace kinsanta akwai bacci,

ko da takoma part d’inta da mamakinta taga har tym d’in haydar bai dawo gidanba saboda yadda ta’aje masa abincin haka tadawo tatarar da shi.

bedroom taje tacire abayarta sannan tadawo parlour tazauna takunna kallo tana yi kad’an-kad’an take kallon agogo


lubna ko da suka dawo kano ta so tafara wucewa gidansu sapna ammah amfah tace a’a tabari suje gida suhuta sannan suje ba dan tasoba haka tahak’ura suka wuce gida, tsaraba sosai sukayo ma su teemah,

bayan sunyi wanka sun huta chan wajen bayan la’asar suka shirya a motar lubna suka shiga ita da amfah suka nufi gidansu sapna.

lokacin da suka isa gidan su sapna, amfah ganin lubna bata da niyar fita sushiga gidan ne yasa takalleta tace dear kinyi zaune muje, murmushi lubna tayi tace ai ba zan iya shiga hakanan ba ammah bari in aika akira mana ita idan tak’i shigowa sai mushiga inkuma mukaga da matsala sai muwuce wajen malam kawai ko ya kikace?

murmushi amfah tayi tace hakan kawai za’ayi, wani yarone da tahango kusa da wani gida yana wasa takirasa bayan ya zo tace dan Allah shiga nan gidan kace ana kiran sapna,

yaron kallon mutanen yayi har zai wuce sai kuma yadawo yace sapna fa ta yi aure kusan sati d’aya kenan, a firgice sukace aure kuma?

yaron gyad’a musu kai yayi alamun eh, lubna kallon amfah tayi cike da tashin hankali itama amfah kallonta takeyi, chan sai amfah tamaida kallonta ga yaron tace anya ka gane sapna da muke nufi?

yaron yace eh nagane ta wannan gidan ko? wlh dagaske nake tayi aure kuma kushiga ummanta tana ciki sai kutambayeta,

lubna kife kanta tayi a steering ganin haka yasa amfah tazaro 100 naira acikin jakkarta tamik’a ma yaron tace gashi mungode,

yaron kar6a yayi yana murna yayi godia yaruga,
amfah dafa lubna tayi tace dear minene mafita? lubna d’ago fuskarta tayi idanuwanta sunyi jawur cikin d’aga murya tace yanzu ni sapna zata yaudara har tayi aure batare da nasaniba? bak’in cikina ma wani yarigani saninta wlh ba zan ta6a barintaba sai nagano gidan da take aure sai na kashe mata aure inyaso sai tadawo mucigaba da cin duniyar tare,

amfah dogon nufamshi taja tace toh ta yaya kike tunanin zamu iya shiga gidansu har mahaifiyarta tafad’a mana gidanta?

lubna ta6e baki tayi tace wannan k’aramin aikine yanzu fito muje mushiga makwabtansu, amfah ganin lubna ta fitane yasa itama tabud’e k’ofar tafito,

gida da yake lik’e da gidansu sapna suka shiga da sallamarsu, wata mata da take zaune tsakar gida saman tabarma ce ta’amsa musu, ganin mata ‘yan gayu yasa tace kushigo, bayan sun shigo har d’aki takaisu bayan sun gaisa lubna tace yauwa daman nan gidansu sapna mukazo ayi mana kwatancen gidanta sai muka tarar da mahaifiyarta batanan kuma gashi lokacin da akayi bikkinta bama gari, mun kira wayanta bata shiga dat’s y mukace bari toh mushigo nan ayi mana kwatancen gidan idan Allah yasa kunsan inda aka kaita.

matar tace Allah sarki wlh kau sapna ta yi aure, ammah nayi mamaki da kukace ummanta batanan domin banji fitartaba ko dai gidan ne arufe?

murmushi amfah tayi tace tun d’azun dai muke Knocking ba a bud’eba ammah indai babu damuwa ayi mana kwatancen gidan nata domin munaso muje yau saboda gobe zamubar garin.

matar tace Allah sarki aikam dai sapna tana chan gidan mijinta da yake a hotoro ammah gidansu mijinne ita gidanta ba’a ida gina mataba, nan matar tayi musu kwatancen gidan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button