DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

haydar janye idonsa yayi daga kallonta, kallonsu lubna yayi da suma suke a tsaye suna ta yamutsa fuska, cike da 6acin rai yace uban me yakawoku gida, lubna dariya tayi irinta ‘yan duniya tace au wai da baka saniba? toh matarkace takiramu domin muzo mud’an d’ebe mata kewa,
sapna a tsorace take girgiza kai hawaye suna zuba daga idonta tace yaya haydar wlh k’aryane kayarda dani bani nakirasuba sune sukazo,
haydar ture sapna yayi daga jikinsa dasauri taduk’e k’asa tare da kare k’irjinta, wajen da su lubna suke tsaye yanufa yace uban wa yace kuzo min gida? matata kuke nema ko? ko alamun tsoro babu atare da su sukace matarka ce kuma baka isa kahanamu yin abinda yakawomuba tunda matarka ta amince mana,
zuciya tad’ibi haydar yad’aga hannu yamareta yace ban isaba kikace?
lubna dafe k’uncinta tayi da mamaki take kallonsa tace ni zaka mara?
wani marin yak’ara d’auketa da shi, yace ko zaki ramane, ta bud’e baki zatayi magana ya k’ara mata wasu marin biyu lafiyayyu nan hancinta yafara zubar da jini,
amfah tace kai bakada hankali kake marin..
tun kan ta ida rufe baki itama yad’auketa da mari saida yayi mata ukku lafiyayyu yace ko kema zaki rama?
gaba d’ayansu kallon haydar suke da gaba d’ayansa ya canza, ita kanta sapna ta tsorata da ganin yanayinsa,
cike da 6acin rai yace ku ‘yan iska ko? toh yau zanyi maganinku, lubna tace wlh kak’ara dukana sai nasa ankamaka, haydar shak’emata wuya yayi da dukkan k’arfinsa yace nikuma yau zan ga ubanda yatsaya muku, duk yadda lubna taso takwace daga rik’on da yayi mata kasawa tayi nan idanuwanta suka canza kala saboda tsananin shak’ar da yayi mata, sapna ce takwala k’ara tace yaya haydar dan Allah kasaketa kar tamutu, wullar da ita haydar yayi tafad’a k’asa yajawo amfah yawurga ta itama sannan yajawo charger yashiga zuba musu su duka biyun yana had’awa da ball dasu dak’afarsa, nan suka shiga kwala ihu, yana cigaba da zuba musu bulala, dakyar suka samu suka mik’e dagudu suka nufi hanyar fita suna gudu yana dukansu k’afarsu babu ko takalma har suka samu suka fita daga gate d’in gidan sannan haydar yakyalesu, jingine kansa yayi ajikin k’ofar gate tare da runtse idonsa cike da takaici tunowa yayi da yadda yasamu khadija kwance da mata biyu, gabansane yashiga fad’uwa cikin ransa yace da ban zo dawuriba da hakan zai faru da sapna girgiza kai tashiga yi cike da takaici yace nikuma kalar tawa k’addarar kenan,
ahankali yabud’e idonsa tare da kwalah ma maigadi kira, maigadi yana cikin d’akinsa ya k’ure volume yana ta sauraron radio, haydar lek’awa yayi d’akin maigadi, ganin haydar yasa yayi sauri yataso tare da kashe radion yace ranka yadad’e yi hak’uri hankalin yatafi nan dasauri yanufi wajen gate yana shirin bud’ewa haydar yace bance kabud’eba kaga matan nan da suka shigo gidan nan?
maigadi yana washe baki yace eh ai sunce wajen hajiya amarya sukazo,
haydar d’auke kansa yayi daga kallonsa yace kar kak’ara bari sushigo gidan nan duk ranar da kak’ara bari abakin aikinka,
dasauri maigadi yazube k’asa yace ranka yadad’e kayi hak’uri wlh nan nake samu ina ci da wannan aikin nadogara, haydar yace na dai fad’amaka dan haka kakiyaye, wucewa haydar yayi yanufi cikin gida
maigadi yace insha Allahu hakan ba zai k’ara faruwaba
yana shiga d’akin kallo d’aya yayi mata har lokacin tana nan yadda yabarta kuka take, ganinsa yasa dasauri tamik’e tare da jawo zanenta tarufe k’irjinta tanufi inda haydar yake tace please yaya haydar kafahimceni wlh bani nace suzoba,
haydar wucewa yayi yashiga bedroom sapna tana bayansa tana kuka tana masa magiya, har sukazo wajen toilet ganin har nan tabiyosa yasa yatsaya batare da yakalletaba yace toilet d’inma bina zakiyi?
sapna girgiza kai tayi tare da fad’in a’a, nan tatsaya bakin toilet d’in shikuma yashiga yad’auro alwallah,
sapna tana ganin yafito tace yaya Haydar dan Allah, dasauri haydar yad’aga mata hannu fuskarsa a d’aure yace wuce kije kiyi alwallah gashinan ana kiran sallah, yana gama fad’in haka yawuce yafita yabar d’akin, sapna naganin fitarsa yatade kai tasake fashewa da wani sabon kukan tace shikenan nashiga ukku ko dai yaya haydar ya yarda da abinda sukace, nan tacigaba da kukanta har saida masallaci aka tada sallar magrib sannan tawuce tashiga toilet saida tayi wanka sannan tad’auro alwallah,
bayan ta fito rigarta tad’auko doguwa tasaka sannan tatayar da sallah, bayan ta gama zaune tayi saman darduma takasa tashi har lokacin hankalinta atashe yake, tun tana sa ran dawowar haydar ammah shuru har akayi sallar isha’i,
zaune tayi tabuga tagumi tunani kawai take idan har haydar yasaketa tasan ba zasu kwashe da dad’iba da ummah domin tasan itama ummah zata iya korarta, tana cikin tunanin sai ji tayi haydar ya bud’e k’ofar, dasauri tad’ago kai takallesa har a lokacin fuskarsa a d’aure take, ta bud’e baki zatayi magana kenan yarigata yace tashi muje kici abinci, sapna dakyar tamik’e tabi bayansa tana share hawayen fuskarta,
haydar shi yayi serving d’in kansa har yafara ci ammah sapna bata da niyar zubawa taci har a lokacin idonta na akansa, kallonta yayi yace kizuba kici man,
sapna kad’an tazuba tana ta juya spoon d’in acikin plate sai da taga haydar ya kalleta sannan tafara ci, shima kad’an yaci yatashi yabarta,
tana ganin ya tashi yashige bedroom dakyar tak’ara 4 spoon sannan tatattara kwanukan tamaida kitchen, saida tawanke sannan tadawo kasa shiga bedroom d’in tayi saida tayi kusan 5 minutes a tsaye sannan tatura k’ofar ahankali tashiga, lokacin haydar yana sa kaya da alama daga wanka yafito, ko inda take bai kallaba har yagama yawuce yahaye gado yakwanta kansa yana kallon cilin,
sapna ahankali tatako tazo bakin gadon tazauna, muryarta tana rawa tace yaya haydar,
wani irin kallo da yayi matane yasa tayi shuru, murmushi haydar yayi tare da janye idonsa daga kallonta ahankali yabud’e baki yace sapna kenan me kuma kikeson cemin? daman ai kin fad’amin baki sona saidai ban saniba ko sune kikeso saisa ni narasa masauki acikin zuciyarki,
sapna girgiza kai tayi tana hawaye tace wlh yaya haydar bahaka bane, juyowa yayi yakalleta yace sapna toh yayane?
rik’o hannunsa tayi tace wlh yaya haydar ina sonka sosai dan Allah kar karabu dani wlh bansan matakin da umma zata d’aukaba akaina, dan Allah kar kasakeni nima ina sonka
murmushi haydar yayi tare da Janye hannunsa daga rik’on da tayi masa yace sapna ya akayi sukazo min gida?
sapna girgiza kai tashiga yi tace wlh yaya haydar bani nace suzoba nima bansan yadda akayi suka san gidanba, yaya haydar wlh suna da had’ari sosai mutanen nan natabbata tunda har suka furta toh ba zasu ta6a gyaleniba.
haydar cike da tausayi yake kallonta yace sapna kidaina cewa haka babu abinda zasu iya yimiki Allah yana tare da ke.
sapna gyad’a masa kai tayi cikin kuka tace yaya haydar lubna ta cutar da rayuwata a baya kaduba kaga yadda tamaidani kowa zargina yakeyi, haydar rungumota yayi jikinsa cike da tausayi yace kikwantar da hankalinki sapna ai ni nasan wacece ke kuma na yarda da ke zan zauna da ke har k’arshen rayuwata, sapna k’ara lafewa tayi a jikinsa tace nagode sosai yaya haydar saidai ina tsoro,
haydar tallabo kanta yayi yace me kike tsoro? kallonsa take ta kasa cemasa komai
haydar bakinsa yakai cikin nata yafara kissing d’inta sapna jikinta yana rawa tashiga mayar masa,