DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

DAF d’in tashi tayi da motarsu nan suka kife.
dagudu mai daf d’in yagudu yabarsu nan.
kafin kace me mutane sun taru a wajen dakyar aka samu aka d’aga motar aka fito dasu gaba d’ayansu jini yake zuba daga jikinsu babu mai motsi, AMBULANCE ce tazo aka sakasu aka tafi dasu Aminu Kano Teaching Hospital dasu direct emergency aka nufa dasu cikin sauri aka kar6esu likitoci dadama suka hau dubasu nan suka tabbatar da babu rai atare da amfah dan haka aka kaita freezing inda ake adana gawa.
aiki ake sosai akan lubna kowane Dr yana dubata a fannin da yafi k’warewa karaya goma aka samu a jikinta, har alokacin batasan inda kanta yakeba,
sai da takwana d’aya sannan itama tace ga garinku nan.
su teema sai bayan kwana ukku sannan sukaji mutuwar su Lubna dan haka suka tattara duk abinda su lubna suka mallaka, suka siyar da gidan suka raba kud’in kowa yakama gabansa.
Soyayyace tsaftatacciya haydar da sapna sukeyi kowa burinsa yaga ya faranta ma d’an uwansa rai haydar kwata-kwata bayaso yaga yayi nisa da sapna kullum suna manne da junansu, aiki ma dan babu yadda ya iya daurewa kawai yake yana tafiya ammah kuma basa minti talatin batare da sunyi wayaba,
ita kanta sapna sai alokacin tasan kowanene haydar domin ayadda tad’aukesa mugu ba haka yakeba mutum ne mai sauk’in kai da iya kula, akoda yaushe godia takeyi da Allah yabata miji irin haydar,
bayan sati biyu haydar yad’auketa yakaita gidan k’anwarsa hafsat da gidan Dr Ahmad gaba d’ayansu sunji dad’in ziyarar da suka kawo musu sukaita nan nan dasu.
bayan kwana biyu yad’auketa sukaje gidan ummah sukayi mata wuni ummah taji dad”i sosai ganin yadda sapna da mijinta suke zaune lafiya, sai bayan sallar isha’i yad’auketa suka dawo gida,
a mota kallon sapna kawai yake yadda take turo baki alamun fushi, murmushi haydar yayi tare da rik’o hannunta yace baby fushin me kike?
sapna kwantar da kanta tayi a kafad’ansa tace my nifa ban gaji da ganin ummanaba shine baka barni nayi mata ko kwana d’ayaba,
haydar murmushi yayi yace baby kinsan dai ummah ba zata ta6a yarda kikwanaba kuma nima kinsan bana iya bacci batare da ke ba.
sapna cikin shagwa6a tace toh yaya haydar kwana d’aya fa kawai zanyi, yace ai ko wuni d’aya dak’yar nake iyawa batare da ke ba kiyi hak’uri wani lokacin mun dawo, sapna janye kanta tayi daga kan kafad’arsa takoma tajingina da murfin mota, kallonta haydar yayi yana murmushi daidai lokacin aka hangame musu gate suka shiga, sapna ko da haydar yatsaya direct part d’in su mami tawuce,
dasallamarta tashiga su mami da daddy suna zaune suna hira, sapna har k’asa tatsugunna tagaishesu suka amsa mata da fara’arsu domin har cikin ransu suna son surikar tasu, mami cike da kulawa tace ashe kun dawo?
sapna kanta a k’asa tace yanzu muka dawo mami,
mami tace toh sannunku ya wajen umman taku?
Sapna tace lfy lou suke suna gaisheku,
daddy da mami sukace muna amsawa
daidai lokacin haydar yashigo d’akin kusa da k’afar mami yaje shima yazauna yagaishe da iyayen nasa
gaba d’ayansu suka amsa masa cike da kulawa,
daddy yace son ya aikin duk yau bamu had’uba
haydar kwantar da kansa yayi saman cinyar mami yace daddy Alhmdllh lokacin da nashigo ka fita ko mami?
mami shafa kan d’an nata tayi tace hakane my son
haydar shagwa6a yayi ta zuba ma iyayen nasa suna biye masa.
daddy yace son wai ma yaushe ne kace zaka koma gidan ka?
haydar murmushi yayi yace jibi zan koma daddy ai angama komai
Daddy da mami sukace Allah yakaimu
Haydar yace Ameen.
ita dai sapna kallon ikon Allah kawai take abun har yaso yabata kunya, suna had’a ido da haydar yad’aga mata gira tare da kashe mata ido d’aya
dasauri sapna tajanye kanta daga kallonsa
mami murmushi tayi tace dota kutashi kuje kuhuta dare yayi
haydar ne yafara mik’ewa tare da kallon sapna yace baby muje,
sapna saboda kunya kamar tanutse k’asa dakyar ta iya mik’ewa sukayi ma su mami sallama suka fito,
sapna tana gaba haydar yana biye da ita suna shiga part d’insu yatsaya haydar yarufe k’ofa ita kuma tashige bedroom.
haydar ko da yashigo lokacin sapna tana tsaye tana cire kayan jikinta zata shiga wanka, bata ankaraba sai ji tayi ya rungumota ta baya,
murmushi tayi cikin shagwa6a tace yaya haydar wanka fa zanyi,
haydar shima murmushin yayi yace baby kuma shine ba zaki bari muyi tareba?
sapna shuru tayi batace komai ba
juyota haydar yayi suka fuskanci juna yana kallon cikin idonta yace baby wai yau menayi miki naga sai fushi kike da ni.
sapna ratayo hannunta tayi a kafad’ansa tace hubby bakayi min komai ba ai kai baka laifi
haydar jan hancinta yayi yace toh Jan ajin ne yamotsa?
sapna d’aga masa gira tayi tace ai kasan mata sai da jan aji.
dariya haydar yayi yace toh kibi dai ahankali kar ajin dai yatsinke, na ma mance ashema tuni ya tsinke
sapna turo baki tayi tace kaida ma zaka k’ara aure kuje kutare da amaryarka a chan gidanka.
murmushi haydar yayi yace jibi ai zan tare da amaryata chan.
yanzu dai muje kiyi min wanka saboda agajiye nake.
turesa sapna tayi tawuce tazauna bakin gado tana ta kumbure fuska.
murmushi haydar yayi yawuce yashiga toilet yayi wankansa.
bayan ya fito sapna tatashi taje tashiga.
haydar dariya yakeyimata k’asa-k’asa,
ko da tafito lokacin haydar har ya kwanta, yar 6ingilin nyt gown tajawo tasaka, sannan taje takwanta chan k’arshen gado,
haydar jawota yayi jikinsa yace baby me kuma nayi?
sapna turesa tashiga yi tace ni kakyaleni.
haydar tallabo fuskarta yayi yace baby banason fushin nan please kifad’a min laifin da nayi miki,
ko dan zan tare da amaryata?
sapna kwallah ce tacika mata ido tace ni ina ruwana da auren da zakayi ai daman nasan ba sona kakeyi ba.
haydar kwantar da ita yayi a k’irjinsa yace baby kidaina cewa haka domin kece ZA’BIN ZUCIYATA duk wani bugawa d’aya da zuciyata zatayi tare da sonki takeyi,
daga ke babu k’ari ke kad’ai kin isheni daman zaulayarki nake ba aure zanyi ba, sapna d’ago kai tayi takallesa tace yaya haydar dagaske kake?
gyad’a mata kai haydar yayi yana murmushi,
rungumesa sapna tayi tace nagode sosai yaya haydar Allah yabarmu tare,
haydar shafa bayanta yayi yace Ameen baby tunda dai anhuce da fushin to aji dani.
sapna mirginawa tayi takwanta chan gefensa cike da shagwa6a tace yaya haydar a gajiye fa nake,
haydar shima samanta yakoma yad’aura kansa a saman k’irjinta yace baby kitaimaka lada fa zaki samu,
shafa kansa sapna tayi tace ammah fa kar ka wahalar da ni please.
dariya haydar yayi yace kar kidamu ba zaki wahala ba daga nan suka lula duniyar masoya.
BAYAN WATA UKKU
su sapna tuni sun tare a sabon gidansu soyayyarsu kawai suke zubawa su kad’ai a gidansu yanzu hankalinta ya kwanta sosai tak’ara kyau da haske da ka ganta kasan tana cikin kwanciyar hankali hatta shi kansa haydar saida yayi ‘yar k’iba yak’ara fresh
yau ma bayan sallar la’asar haydar ne kwance saman cinyar sapna suna kallon Indian films, sapna tana shafa gashin kansa, sapna kallonsa take cike da so da k’auna tace hubby yaushe zamuje mugaishe da su mami kaga tunda muka dawo gidan nan ban fitaba, haydar murmushi yayi tare da kissing d’in cikinta yace baby sai kin haihu sannan zamuje.
sapna zaro ido tayi tace yaya haydar har sai nan da wata shidda kake nufi? haydar shima kallonta yayi yace eh baby banason kiwahalar min da unborn babyna, sapna cike da shagwa6a tace kai yaya haydar zumunci fa zamuyi kuma fa babynka ina kular maka da shi nice ma yake wahalarwa,