BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

toh bari kiji kinyi babban kuskure da kika bari damarki tawuce miki, bakiyi amfani da itaba a lokacin da kike da dama sai lokacin da tawuce miki, duk abinda kika aikata kije dan kanki saboda kanki kika cuta, kuma alhaki kwikwiyo ne, ni nagode ma Allah da gaskiya tabayyana nagane ainahin wacece ke,
nuna sapna yayi yace kidubi wannan baiwar Allah wlh ko hak’inta ba zai ta6a barinkiba saboda kece silar fad’awanta cikin mummunan hali kuma inaso kisani duk abinda tayi bacikin hayyacintaba toh laifin nakine,

tsanartace tabayyana k’arara a idanunsa yace khadija na tsaneki bana fatan nasake sakaki a cikin idona dan haka kitashi kifitar min daga gida.

sapna cikin kuka tazo tatsugunna gaban haydar tace yaya haydar dan Allah kayafe mata tabbas kuskurene ta san ta aikata kuma ta gane hakan ta zo ta nemi afuwa dan Allah kayafe mata.

haydar d’ago sapna yayi daga duk’awar da tayi yazaunar da ita kusa dashi sannan yakalli deejah da take durk’ushe k’asa tana kuka yace yau sai gaki kinzo gabana kina neman yafiyata toh kije na yafe miki albarkacin wannan baiwar Allah

deejah cike da jin dad’i tace nagode sosai haydar.
haydar hanya yanuna mata yace tashi kifitar min daga gida tunda na yafe miki kuma kar kikuskura kibari ink’ara ganin k’eyarki a gidana,

sapna har ta bud’e baki zatayi magana , wani irin kallo da haydar yawurga mata yasa taja bakinta tayi shuru, tana kallon deejah tatashi tafita tabar gidan.

tana fita, haydar tashi yayi yashige bedroom d’insa sapna binsa tayi da kallo bai dad’e da shigaba yafito rik’e da key din motarsa ko inda sapna take bai kallaba yaficce yabar gidan.

sapna dafe kanta tayi da hannu biyu tacigaba da kuka k’asa-k’asa, saida tayi mai isarta sannan tatashi tashiga d’akinta saboda sallar magrib da taji ana kira,

har akayi sallar isha’i batasa haydar a idonta ba sai wajen 8:30pm sannan taji dawowarsa, tashi tayi tashiga toilet d’inta tayi wanka,

bayan ta fito shiryawa tayi cikin wata nyt gown ‘yar k’arama iyakarta cinya ta d’ameta sosai, sannan tatufke gashinta da band tafeshe jikinta da turaruka, tsayuwa tayi gaban dressing mirror tana k’ara kallon kwalliyar da tayi, murmushi tayi ganin tayi irin shigar da haydar yakeson ganinta a cikinta, kallon d’an k’aramin cikinta tayi da yafara fitowa sannan tafito tanufi master bedroom.

haydar kwance yake saman gadonsa kansa yana kallon ceiling ya yi pillow da hannuwansa, k’amshin turarentane da yaji yasa yamaida kallonsa ga k’ofa

ganin sapna yayi tsaye bakin k’ofa ta zuba masa ido tana kallonsa, haydar ma zuba mata ido yayi yana kallonta daga sama har k’asa, ganin batada niyar zuwa inda yake yasa yamik’a mata hannu alamun tazo.

sapna mak’e kafad’a tayi alamun a’a.
haydar murmushi yayi yace please my princess.
Sapna ahankali tataka tana tafiya ta jan hankali har ta iso bakin gadon,

haydar jawota yayi tafad’o jikinsa, sapna ‘yar k’ara tayi cikin shagwa6a tace yaya haydar sai kaje ka ji ma babynmu ciwo?

haydar muryarsa tana rawa yace sorry my princess kece ai kika rikitani har namance da baby, hannu yakai yad’age mata rigarta yana shafa cikinta.

suna had’a ido da sapna suka sakarma junansu murmushi, sapna shafa sajen fuskarsa tayi tace yaya haydar nagode ma Allah da yamallaka min kai amatsayin mijina tabbas nasan nayi sa’ar miji, murmushi haydar yayi tare da sumbatar bakinta yace sapna a kullum idan nakalleki ina gode ma Allah, domin nasan nayi dacen mace tagari, tabbas nasan had’uwata da ke alkhairi ce, fatana Allah yasafkeki lafiya yabamu baby mai kama da ke,

murmushi sapna tayi tace a’ah yaya haydar mai kama da kai dai ai kafini kyau sosai.

lakuce hancinta haydar yayi yace a’a baby kinfini kyau, indai mace kika haifa toh sunan ummah nake da burin sanya mata saboda inaso tad’auko irin hak’uri irin na ummah domin kema wajen ummah kika gada.
murmushi sapna tayi tace nagode sosai yaya haydar,

d’aura hannunsa yayi a saman bakinta yace don’t mention it my dear

sapna kwantar da kanta tayi a k’irjinsa tace yaya haydar ina mai k’ara neman ma deejah gafara, dafatan ka yafe mata har cikin zuciyarka wlh kau taban tausayi kaduba kaga duk kyaun nata duk kud’in da Jin kan ammah ammah bazasu iya yi mata amfani ba, kalli yadda takoma

ganin sapna tana shirin yin kuka yasa haydar ya rungumeta yace baby nayafe mata wlh daman ita rayuwa haka take, a lokacin da duniya takeyi da kai zakayi yadda kaso ammah mai hankaline yake barinta tun kan tajuya masa baya domin aikinka nak’warai kawai zai iya cetonka.

sapna tana hawaye tace hakane yaya haydar Allah yasa mudace.
Ameen haydar yace.

Sapna janye jikinta tayi daga na haydar tamik’e.
haydar yace my princess ina zakije?

murmushi sapna tayi tace yaya haydar ka san babyn nan naka shi yake sa ni kwad’ayi zan je insha abinda yake so,

dariya haydar yayi yace haba yarinya daman chan da kwad’anki babu ruwan babyna.

sapna wucewa tayi tafita tana dariya, haydar yabita da kallo cike da so da sha’awa.

bayan kamar minti biyar sai gata ta dawo hannunta rik’e da kwalbar lemu gashin kanta a baje yake a kafad’anta, tafiya take tana tangyad’i kamar zata fad’i,

dasauri haydar yamik’e yaje yatarota yace my princess ya dai? ko kin tunada da ne?
kallonsa sapna tayi suka sa dariya gaba d’ayansu sannan tamik’a masa kwalbar lemun shima yad’an sha sannan ya aje a bedside, jawota yayi suka fad’a saman gado suna dariya tare da janyo blanket suka rufa.

toh Sapna sai dai muce Allah yasafkeki lafiya.

Alhamdulillah anan nakawo k’arshen wannan littafin mai suna Duk tsuntsun da yaja ruwa abinda muka fad’a daidai Allah yabamu ladar, kurakuren da suke ciki Allah yayafe mana

fatan Alkhairi agareku masoya, sis Nerja’art tana sonku sosai????????

Sis Nerja’art✍????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button