DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

K’arfe goma tafarka lokacin d’akin wayam ba kowa dasauri tatashi tashiga wanka, bayan ta fito shafa tayi tabud’e wardrobe d’in mummy lubna 6angaren kayanta taduba tad’auko atamfa pink colour riga da skirt ne daidai jikinta ko da tasanyasu sun kar6eta sosai abu ga farar fata .
‘Daurin kallabi tamurza tajawo farin veil tayafa tafeshe jikinta da perfume, takalmanta farare tazura sannan tad’auko white bag, freezer tabud’e tad’auko kwalbar giya d’aya tasaka a cikin jakarta.
Parlour tafito nan ta tadda su mummy lubna zaune suna hira, zuba mata ido sukayi suna kallonta sai kace yau suka fara ganinta, sapna kallon lubna tayi tace mummy zan tafi, awulak’ance lubna ta kalleta tace ina zakije? Mummy gida zanje,
‘Dauke kai lubna tayi daga kallonta tace kikoma sai anjima zaki tafi,
Kwallace tacika ma sapna ido tace mummy dan Allah kibarni intafi wlh ummana tana chan tana jirana,
Cigaba lubna tayi da dannar wayarta tace kin dai ji abinda nafad’a miki, bana son gardama.
Juyawa Sapna tayi zata koma d’aki hawaye duk ya cika idonta, har ta bud’e k’ofa zata koma sai taji muryar lubna ta ce kizo kitafi,
Toh tace sannan tawuto tace sai anjimanku, su teemah sukace sai kin dawo.
Lubna ce tace sai munyi waya kigaishe da umman.
Toh mummy.
Mai adaidaita tasamu tafad’a mashi inda zai kaita, har k’ofar gidansu yakaita tabiyasa kud’insa,
Tura k’ofar gidan tayi tashiga da sallamarta ummah da take cikin d’aki ta amsa mata, d’akin ummah tashiga tana murmushi dasauri tanufi jikin ummah tafad’a, murmushi ummah tayi tace ni d’agani kar ki karyani.
Cikin shagwa6a tace ummah ba karyaki zanyiba, ina kwana ummah?
Lafiya lau sapna, ya kuka tashi?
Lafiya lau ummah, Aunty lubna tana gaisheki,
Saida gaban mummy yafad’i duk lokacin da sapna za ta ambaci sunan lubna sai gabanta ya fad’i, k’irk’iro murmushi tayi dan kar sapna tagane tace ina amsa sosai, tashi kije kikai jakarki d’aki, nima yanzu zan shiga kitchen indubo girkin da rabi take,
Tashi sapna tayi tace laah ummah ashe rabi ta dawo? Eh tun jiya ma tadawo ta ma shigo ta yi min girki.
Ayyah toh nima bari inzo inkama maku, a’a sapna kije kihuta daga dawowarki sai girki? Murmushi tayi tace bakomai ummah zan iya. Nidai na ce a’a kije kihuta.
‘Daukan jakkanta sapna tayi tanufi d’akinta, ko da tabud’e komai fes, kayanta ta aje tak’ara gyara d’akin,
kunna kallo tayi bollywood takunno domin a rayuwarta tana k’aunar kallon indian film……..
Wani katafaren gidane a hotoro tundaga ginin gidan zaka gane na manyan mutane ne, fad’in girman gidanma 6ata lokacine yana d’auke da d’akuna ak’alla sun kai goma tsaruwar gidanma sai wanda yagani
Wani d’akine nagani daban chan gefe daga gani kasan wanda yamallakesa mai gidan ne inkuma ba shi ba toh d’an gidan ne,
Wani k’aton d’akine mai d’auke da room nd bed room komai na cikinsa ash nd black colour ne, kwance nahango wani mutum a kwance yana bacci, K’arar Wayarsa ce tafarkar da shi daga baccin da yake dakyar yajawo wayar yayi picking d’in call d’in tare da sallama, a chan 6angaren aka amsa mashi yace Dr Haidar yau fa yakamata ace yanzu ka shigo hospital domin kana da patients sosai, dakyar yabud’e baki yace gani nan tafe.
Daga chan 6angaren dariya Dr Ahmad yayi yace kace dai bacci kake mu da ganinka ai sai kusan 10, please kaje kakama min kafin inzo, dariya doctor Ahmad yayi yace nikuma nawa aikin fa? Saisa nace maka kayi aure kahuta ammah ka k’i, da lokacin da kake da aure ai baka makara,
Dan Allah malam ya isa haka idan ba zaka kama min ba kabarshi, kashe wayersa yayi,
Dasauri yasafko Daga saman makeken gadonsa, wani dogon matashine wanda ba zai gaza 30 years ba, ba fari bane kuma ba bak’iba zamu iya kiransa da chocolate colour, yana da dogon hanci, bakinsa d’an madaidaici, yana da manyan idanuwa, baida k’iba ammah baida rama sosai jikinsa daidai shi.
Dasauri yafad’a toilet dan yin wanka, bayan yafito shiryawa yayi cikin k’ananun kaya yataje sumarsa key d’in motarsa yad’auka yafito direct room d’in mummynsa yanufa, dasallama yashiga wata ”yar dattijuwa ce a zaune wadda ak’allah zata kai 52 years, murmushi d’auke a fuskarta tace my son ka fito?, wajenta yanufa yazauna k’asa kusa da k’afafuwanta yace mummyna ina kwana? Lafiya lau my son dafatan ka tashi lafiya, d’aura kansa yayi saman cinyarta yace lafiya lau mummyna.
Shafa kansa tayi tace my son kai dai baka girma har da iyalinka ammah baka daina hawana ba, d’ago kai yayi yakalleta yace mummy kidaina cewa ina da iyali ni banda kowa dan Allah kibar maganar,
Murmushi tayi tace my son aidai tunda ka ta6a aure ai ka girma, cikin shagwa6a yace toh mummy ai yanzu banda auren kuma banda d’a.
Murmushi tak’ara yi tace babana saisa nakeson kak’ara yin auren domin inga jikana dan Allah kasamo mana mata kazo kakoma gidan ka,
tashi yayi yace mummy zan tafi aiki,
Kallonsa mummy tayi tace dan na yi maganar aure ko? Wlh idan baka maida hankaliba kasamo mata mu zamu za6a maka wadda tayi mana,
wucewa yayi ko breakfast bai tsaya yi ba ransa a 6ace, motarsa yashiga direct Aminu Kano Teaching Hospital yanufa.
Ko da ya isa asibitin patients yatadda jibgi guda zaune a saman kujerun da suke a kusa da office d’insa suna jiransa ganinsa yasa suka fara mik’o gaisuwa attender ne yazo yabud’e masa k’ofar bayan ya zauna nan yafara duba patients d’in nasa.
Wajen k’arfe ukku yagama aikinsa cikin tafiyarsa ta k’asaita yafito dan yau ko Dr Ahmad bai tsaya jiraba, Sister Aisha ce tahangosa dasauri tanufo inda yake fuskarta d’auke da murmushi motarsa yanufa ganin yana shirin shiga yasa ta kira sunansa, ba tare da ya juyo ba yatsaya, dasauri ta iso inda yake, cikin fara’a tace doctor ba dai tafiya zakayi?
Kallonta yayi a wulak’ance yace yadda idanuwanki suka gane miki,
Haushi sister Aysha taji tace wai kai dr haydar meyasa kake son wulak’antani ko da ka ga na damu da kai?
Tsanarta ce tabayyana a fuskarsa yace wai ke wace kalar macece marar zuciya? Ina so kifita harkata domin bakiga ina kula mata ba a hospital d’in nan dan haka ba zan fara a kanki ba, baijira jin abunda zata ce ba yabud’e motarsa yashiga yatada nan yabad’a mata k’ura, ita dai tsaye tayi inda yabarta tana bin motar da kallo har ya 6ace mata tadaina ganinsa sannan tawuce takaici duk ya cikata domin ita dai tana son guy d’in.
Gudu yake da mota har ya isa wata anguwa, bakin titi yafaka motarsa ganin ukku da rabi ta yi ‘yan isilamiyya ne suke wucewa jefi-jefi yana binsu da kallo har Kusan 4:30pm, ganin yau ma baiyi nasaraba yasa yakoma cikin motar yakife kansa da sitiyarin saida yayi kusan 5 minutes sannan yatada motarsa cikin takaici yanufi gida.
Ko da yakoma gida direct d’akinsa yanufa, wanka yashiga bayan ya shirya yagabatar da sallar la’asar addu’a yatsinci kansa da yi akan Allah yacika masa burinsa,
Haushin kansa yaji da yatuno akan abinda yake addu’ar, hawayen takaicine suka zubo masa tunowa da yayi da abunda yake burin yamance a rayuwarsa…………
Please kudinga yi min uzuri nima ba a son raina bane yasa kuke ganin bana dogon typing kuyi la’akkari da novel biyu nakeyi a lokaci guda, ina ganin messages d’inku nagode sosai masoya????
Muje Zuwa
????????????????
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
????????????????
(TRUE LIFE STORY)
Written By ~ Sis Nerja’art