BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Page 1⃣5⃣➖1⃣6⃣

Dafasa yaji anyi ta baya dasauri yagoge hawayen fuskarsa, muryar mummynsa yaji tana cewa haba my son bai daceba aga hawayen gwarzon namiji kamarka ya kamata kadaina sanya damuwa a ranka be a man mana,

Murmushi yayi tare da k’ok’arin 6oye damuwarsa yace kiyi hak’uri mummyna insha Allahu na daina,

Cikin jin dad’i tace yauwa my son kataso kazo muje kaci abinci dan yau ban tunanin ka ci wani abu kuma sister d’inka tana nan ta zo tun d’azun take cigiyarka, tashi yayi yabi bayanta domin saida tayi maganar yatuno maltina ce kawai yasha yau.

A parlour yatadda Hafsat, ganinsa yasa tataso tarungume d’an uwan nata tilo Cikin jin dad’i tace oyoyoo my yaya, Murmushi shima yayi tare da d’agota daga jikinsa yace my sis saukar yaushe.

Cikin shagwa6a tace tun d’azun ina gidan nan fa tun 3 o’clock nake sa ran dawowarka ammah shuru shine nayi tunanin ko ka biya wajen new Auntynmu, dariya yayi yarik’o hannunta yace my sis har yanzu kina nan da shagwa6arki ina my daughter baki zo da itaba?

Murmushi tayi ganin yadda yayan nata yabasar da maganar domin ta san halinsa a yanzu ba ya son ayi mashi maganar mace, jawosa tayi suka nufi dining tace Afnan tana wajen nanny d’inta suna chan d’ayan d’akin, jawo masa kujera tayi yazauna sannan tayi serving d’insa.

Bayan ya gama cin abincin yazauna suka sha hira da ‘yar k’anwarsa da yake ji da ita,

Sai bayan sallar isha sannan yad’auketa a motarsa zai maidata gidanta, tafiya suke tad’ago kai takalli yayan nata cike da so da k’auna tace yayana.
‘Dago kai yayi yakalleta batare da ya ce komai ba dan Haidar ba mutum bane mai yawan son magana ba ,
Marairaicewa tayi tace dan Allah kamance abinda yafaru tsakaninka da Aunty khadija kasake yin aure kaga zamanka haka ba mata baida dad’i wlh inaso inga matarka ko dan insamu ‘yar uwa kuma ka ga mummy ma ba ta jin dad’in zamanka haka.

Murmushi Haidar yayi bai tanka ba yacigaba da tuk’insa, hafsat kasancewar ta san halin yayan nata bata damu da shurun da yayi ba, shagwa6e fuska tayi kamar zatayi kuka tace yayana dan Allah kataimaka kasamo min ‘yar uwa.

Yanayin yadda tayi maganar ta so tabashi dariya daidai lokacin mai gadi ya hangame mashi gate d’in gidan yashiga saida yayi parking d’in motar sannan yajuyo yakalleta yasakar mata murmushi yace kar kidamu my sweetheart insha Allahu ina nan ina duba matar da zata dace da ni wadda ku ma zakuji dad’in zama da ita ba kamar khadija ba,

Cikin jin dad’i hafsat tarungumesa tace gaskiya na ji dad’i yayana Allah yaza6a mafi alkhairi,
Ameen my dear,
Bankwana sukayi tafita daga motar saida tabud’e gidanta tashiga sannan yajuyar da kan motar yatafi gida cike da kewar k’anwar tasa.


Sapna kwance take tana ta chart d’inta gefenta kwalbar coke ce tana yi tana korawa ammah ba ainahin coke d’in bane giya ce take sha nan da nan idanuwanta suka rine tafara sakin layi????.

Ummah ce tashigo d’akin tace sapna kitaso kid’auko Abincinki dakyar ta iya bud’e baki tace ummah sai zuwa anjima zan ci.

Kallonta ummah take cikin mamaki tace ya akayi naga kin canza haka?

Murmushi sapna tayi tace wlh ummah kaina ne yake ciwo,

Ummah dogon numfashi taja tace haba har kin d’aga min hankali kedai wata ragguwace ciwon kai kawai ammah har kin canza maganarki ma sai kace ta ‘yan maye toh wlh kigyara aure fa zakiyi nan gaba kuma haihuwa zakiyi ragwancinki ya yi yawa.

Murmushi kawai sapna tayi tana lumshe ido, ummah tace Allah yasauk’e bari inje insamo miki magani, ficcewa ummah tayi dakyar sapna takulle marfin robar tana jin dad’in yadda ummah bata gane ta ba daman yawanci idan tana gida duk wani abu da zata sha saidai tazuba cikin kwalbar lemu dan gudun 6acin rana.

Ummah bata dad’e da fitaba datawo hannunta d’auke da goran ruwa da magani, mik’ama sapna tayi tace tashi kisha dakyar sapna tatashi takar6i paracetamol d’in, ummah tana fita tabud’e bed side tasaka maganin sannan takoma ta kwanta tausayin ummanta ne yakamata tana tuno rayuwar da tajefa kanta a ciki hawaye nan suka fara zuba daga idonta nan hankalinta yak’ara tashi dakyar tabud’e baki tace deejah kece silar fad’awata wannan mummunar rayuwar, ganin damuwa tana neman tayi mata yawa yasa tajawo kwalbar coke d’in tabud’e takunkud’e giyar da take ciki nan da nan tasaki robar takoma takwanta bacci yayi awon gaba da ita.

WACECE SAPNA


Alhaji Aliyu da Bilkisu sunyi auren soyayya,

Alhaji Aliyu yana koyawa a makarantar mata ta gwamnati da take a jihar kano sannan yana kasuwancinsa yana siyar da labulaye kala-kala ana yo masa order d’in yadunan shikuma sai yad’inka da kansa ya d’aura k’anansa sani a bisa kasuwancinsa shi yake kular masa da shagon Allah ya sanya albarka a cikin sana’ar dan kud’i suke shigo masa ba ‘yan kad’an ba,

kasancewar su biyu Allah yaba iyayensu, bilkisu kuma ta kasance d’iyar k’anwar mahaifiyarsu Alh Aliyu bayan rasuwar iyayenta rik’onta yadawo hannun mamarsu Aliyu, mahaifinsu Alh tukur manomine yana da rufin asiri bakin gwalgwado ya sa ‘ya’yansa sunyi karatun boko bayan Aliyu ya gama karatunsa da taimakon Allah yasamu aikin koyarwa iyayensu sunyi murna sosai lokacin bilkisu ta gama secondary school aka had’asu aure suna zaman su lafiya hankalinsu kwance saidai hankalin bilkisu ya tashi saboda kusan shekara d’aya da aurensu ammah ko 6atan wata bata ta6a yi ba Alh Aliyune yake kwantar mata da hankali ranar wata talata da ba za su ta6a mancewa da itaba aranar akasha akayi ruwa mai k’arfi wanda yayi sanadiyar fad’uwar gidaje ciki ko harda gidan iyayen Alh Aliyu nan bango yadannesu duk suka mutu a ranar anyi sa’a k’anensa yana gidansa da yaje ruwa yataresa sai yakwana chan, Alh Aliyu sunga tashin hankali haka suka hak’ura suka mik’a lamurransu ga Allah,

saida sukayi zaman aure na tsawon shekara hud’u sannan Allah yabasu haihuwa tunda bilkisu tasamu ciki murnar wajensu ba a magana,

Bayan wata tara tahaifi shantaleliyar d’iyarta kyakkyawa mai kama da ita kasancewarta fulani ta usuli saidai d’iyar ta fi uwar fari, ranar suna jaririya taci sunan mahaifiyar Alh Aliyu wato Fatima ammah suna ce mata Sapna.

Tun daga kanta bilkisu bata k’ara ko 6atan wataba ahaka yarinya tataso tana samun kulawa sosai wajen iyayen nata ta taso cikin gata ga wayau ammah kuma hakan bai hana su tarbiyantar da itaba,

Tana da shekara hud’u mahaifinta yasa ta islamiyya da boko kasancewar kafin akai inda yake teaching akwai primary school kullum idan zai wuce aiki sai ya biya ya safketa idan yataso yabiya yad’auketa ahaka har tagama primary d’inta, makarantar da yake koyawa yasamo mata tayi joining d’in karatunta.

Tana taimaka ma mahaifiyarta wajen ayyukan gida, ba ta wasa da islamiyyarta ko kad’an kasancewarta ta tasowa mai son karatu.

Tana da shekara sha shidda tayi candy har tagama makarantarta ba ta da k’awa wacce zata ce Aminiyarta ce saidai gaisawa sama-sama kasancewarta bata da son yin abokai, ko da exams d’insu tafito murna wajen iyayenta da ita kanta ba a magana, mahaifinta kasancewar mai son karatune nan yashiga nema mata admission domin yana burin yaga d’iyarsa ta yi ilimi bakin gwalgwado, ahaka yasamo mata admission a B.U.K inda tayi choosing d’in Computer Biology domin shine best subject d’inta. Ana saura sati ukku tafara zuwa makaranta ranar wata juma’a ranar da bazata ta6a mancewaba a rayuwarta……….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button