BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

MUJE ZUWA
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Page 1⃣7⃣➖1⃣8⃣

Ranar wata juma’a ranar da ba zata ta6a mancewa ba a rayuwarta abbah ne yatashi da matsanancin ciwon ciki duk sun tsorata da ciwon nasa dan ko abinci kasa ci yayi da ka gansa ka san yana jin jiki sosai, sapna da sauri ta d’auko hijab inta tasaka tanufi gidan baba sani k’anen mahaifinta da yake bayan layinsu domin takirasa, ganin yanayin yadda tashigo saida yatada hankalin baba sani da matarsa, nan suka shiga tambayarta me ke faruwa?

Dakyar tabud’e baki hawaye suna zuba daga idonta tace wlh Abbah ne baida lafiya dan Allah katafo muje akaishi asibiti nan hankalin baba sani yatashi dasauri yajawo key d’in mota suka fito suka nufi gidan,

Tun fitar Sapna, Abbah yakalli ummah da ta buga tagumi tana kallonsa murmushin k’arfin hali yayi dakyar yabud’e baki yace Bilkisu Allah yayi miki albarka aduniyar nan banda kowa daga ke sai sapna sai k’anena sani, ku kula da kanku kuji tsoron Allah aduk yanayin da kuka samu kanku kumaida lamurranku ga Allah kukular min da d’iyata.

Ummah hawaye suna Zuba daga idonta tace toh Alhaji insha Allahu zamuyi duk abinda kace mun gode da shawararka, murmushi yayi yace Allah yayi muku albarka baki d’ayanku, Ameen tace,
Waiga wa yayi yaga ba sapna, ganin haka yasa ummah tagane sapna ce yake nema, ahankali tace Alhaji ta je takira sani domin muje asibiti,

Dakyar yabud’e baki yace ya za ayi akai gawa asibiti kawai akaita makwancinta, kallonsa ummah tayi tana so tafahimci abinda yake nufi, ganin haka yasa abbah yayi d’an guntun murmushi dakyar yabud’e baki yace d’ebo min ruwa insha,

dasauri ummah tatashi domin takawo mashi ruwa dan duk wunin yau ba abinda yaci, tana tafiya nan yafara kalmatush-shahada, koda tadawo ta taddasa idanuwansa a rufe tace Alhaji katashi kasha ruwan, shuru taji ya yi, rik’o hannunsa tayi tace ko baka iya tashi intaimaka maka? Kawai sai ganin hannuntayi ya koma, k’ara d’aga hannuntayi nan ma taga haka, fashewa tayi da kuka tace nashiga ukku kai dai ace ka mutu Alhaji,

Daidai lokacin su sapna suka shigo d’akin sapna takalli ummanta tace ummah muzo mukaisa asibiti yanzu, shuru ummah tayi.

Babah sani da tunda yaga yayan nasa saida jikinsa yayi sanyi domin ba ya tunanin da sauran rai atare da shi, dakyar yaja k’afarsa ya isa inda yake yakai kunnansa saitin hancinsa yaji ba ya numfashi, hannunsa ya d’aura saman k’irjinsa nan ma baida alamun rai ba atare da shi, innalillahi wa inna’ilaihiraji’un yashiga nanatawa, dasauri sapna ta iso inda yake cikin tashin hankali tace baba sani ya akayi abbah bacci yake ko?

Kallonta yayi cikin tausayi idanuwansa sunyi jawur yace eh sapna Abbanki ya yi baccin da ba a farkawa daga garesa saidai muyi hak’uri dasauri sapna taja baya tace me kake nufi da haka? Kana nufin abbanah ya rasu?

Ummah k’ara fashewa da kuka tayi tace ina zansa kaina shikenan Alhaji ya tafi ya barmu, dasauri sapna tayo wajenta tare da fad’awa jikin ummah, itama fashewa tayi da kuka tace ummah kidaina cewa haka abbanah ba mutuwa yayiba, cikin kuka ummah tace sapna saidai muyi hak’uri wanda yabamu shi ya kar6i abunsa.

Kuka sukeyi kamar ransu zai fita, Babah sani ma ne mai juriya cikinsu nan yashiga basu hak’uri tare da yi masu nasiha akan kukan mutuwar da sukayi, nan duk suka nutsu suka daina kukan suka shiga yi masa addu’a, ganin sun sami natsuwa yasa baba sami yafita domin yakira mutane azo a kimtsasa akaisa gidansa na gaskiya.

Bayan wata d’aya ummah ta matsa ma sapna kan dole tafara zuwa school ko da taje lokacin har anfara lecture fara kalle-kalle tayi tana neman wajen zama a matsayinta na new students, ajin cike yake da mata da maza, wani wajen zaman mutum d’aya tahango wadda take zaune ta yafucota da hannu tana murmushi dasauri sapna ta isa wajen tazauna suka kalli juna sukayi murmushi batare da sunyi magana ba suka maida hankalinsu ga lecture d’in da akeyi.

Lecturer d’in yana gamawa yatattara kayansa yafita, wadda take zaune kusa da sapna takalleta tayi murmushi a karo na biyu tace sannu da zuwa ammah ke yau kika fara zuwa ko?, itama sapna ta maida mata murmushin tace eh wlh,
Ayyah am Khadija Nasir by name ammah nickname d’ina deejah dafatan zan zama friend d’inki,
Murmushi sapna tayi tace Hafsat Aliyu ix ma name, babu damuwa deejah na kar6eki a matsayin friend d’ita.

Deejah ita taraka sapna tayo clearance d’in course foam d’inta saboda ita tazo late dan tun last week new comers suka fara zuwa.

tun daga ranar sapna da deejah suka k’ulla abota, ko da deejah za ta girme mata da kadan ahaka suke k’awancensu, deejah ta lik’ema sapna ne ganin yadda brain d’inta take ja, dan duk wani karatun deejah sapna ce take taimaka mata,

yau ma dai bayan lecturer ya fita daga class d’insu, sapna tace wash na gaji gaskiya wannan guy din yana wahalar da mu dayawa, dariya deejah tayi tace wlh dan saboda ke da kike matsamin ai da ban zama lecture d’insa, harararta sapna tayi cikin wasa tace ke ai in za a biye miki babu lecture d’in da zaki zauna, deejah tace wlh kau babu, Jakarta tajawo tabud’e tad’auko robar lemun lacasera ammah ga wanda yasan lemun in ya gani zai gane bashi bane a ciki, bud’ewa tayi tafara sha.

kallonta sapna tayi tace wai ke baki da aiki kullum sai kinsha wannan lemun? dariya deejah tayi tace wlh ina jin dad’insa bana iya zama ban sha Shiba, kid’and’ana kiji akwai dad’i, sapna tace no ni bana sha,
sapna kenan kadai har yanzu baki wayeba
eh na ji bakomai kibarni a matsayin difficult villager ta nan suka sa dariya sapna tace ke nifa yunwa nakeji, kallonta deejah tayi tace kije kisamo mana abinda zamuci domin ni kin san da na sha wannan lemun babu inda nake iya zuwa,

kallonta sapna tayi tace ni tunda nake ban ta6a jin wanda yasha lemun nan yace ba ya iya tashiba sai ke, ni ai lacasera ne kawai bana sha ban saniba ko shine yake sanyaki haka ba.

kife kanta deejah tayi ba tare da ta bata amsa ba, ganin haka yasa sapna tatashi tafita waje domin tasamo musu abinda zasu ci, takeaway tayo musu tasiyo maltina sannan tadawo class d’in yadda tatafi tabar deejah haka tadawo ta same ta, aje mata nata tayi gabanta ita kuma ta bud’e nata tafara ci tace idan kin tashi kin ci, idan da sabo daman sapna ta saba ganin deejah a wannan halin.

sai da lecturer yashigo sannan sapna ta tada deejah dakyar tabud’e idonta da sukayi jawur.

kallonta sapna tayi tace bakida lafiya ne deejah?
maida idanuwanta tayi tarufe dakyar tabud’e baki cikin muryar masu jin bacci tace kai na yake min ciwo, sannan Takoma ta kwanta.

ita dai sapna kallon deejah take cikin mamaki tunani take wane irin ciwon kai ne dan kullum deejah saidai tace kanta yake ciwo, kuma sai tayi ta abubuwa irin na masu shaye-shaye, maida hankalinta tayi wajan lecture d’in da ake masu a haka har lecturer d’in yagama abinda yake yafita daga class d’in.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button