DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

ahaka har suka shiga 200level sapna tun tana fushi da rashin son karatun deejah har tazo tahak’ura ta daina, ganin yadda sapna take fushi da ita yasa deejah tad’an rage sha tafara maida hankali tana d’an karatu………
Muje Zuwa
????????
_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_
????????
(BASE ON TRUE LIFE STORY)
Written By ~ Sis Nerja’art
DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND UMMUN MEENAL
INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ?? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ?? CURDLES ?? GIGGLES ?? AND MARRIEGE THINK??
JUST GIVE US FOLLOW….✔
Page 1⃣9⃣➖2⃣0⃣
Ranar da sapna da bazata ta6a mancewa da itaba ranar wata talata bayan sun fito lecture zaune take ita da deejah a bayan wani building kowanensu wayace a hannunsa yana latsawa, mutane d’ai-d’ayane suke giftawa ta wajen, Deejah jakkarta tajawo tabud’e tafitar da robar Coca Cola nan tabud’e tad’ansha sannan takalli sapna da taketa dannar waya tace besty ha wannan kisha, kallon lemun sapna tayi tana murmurshi tace besty yau kuma wannan akesha? Toh ina lacaserar, yamitsa fuska deejah tayi tace wlh wannan naji ina buk’atar sha saboda shi yake d’an ragemin damuwata, kallonta sapna tayi cike da mamaki tace daman akwai lemun da yake rage damuwa? Murmurshi deejah tayi tace amsa kisha anan zaki sami amsar tambayarki, girgiza kai sapna tayi tace a’a ni ba zan shaba, Deejah ta ji haushin hakan da sapna tayi mata cikin 6acin rai tace toh shikenan kin kyauta daman nasan kyamata kike ammah bakomai,
Dasauri sapna tarik’o hannun deejah tare da cewa kiyi hak’uri besty wlh ba haka nake nufiba bari insha Sapna d’aga robar tayi tafara kunkud’a da mamakinta sai taji ba lemun bane ciki, dakyar tajanye kwalbar tare da kallon deejah da itama tazuba mata ido tana kallonta nan Sapna ta fara lumshe ido, dakyar tabud’e baki tace deejah menene kika bani? Murmushi deejah tayi tace karkidamu my besty indai zaki dinga shan wannan babu abinda zai dinga damunki a rayuwa, Sapna sakin kwalbar tayi duk yadda taso tatashi ammah kasawa tayi a k’arshe jikin Deejah tafad’a bacci yayi awon gaba da ita,
Ganin haka yasa Deejah tayi Murmushi tare da cewa my besty ahankali kema zan wayar da ke domin ina buk’atarki acikin rayuwata k’ara gyarama Sapna kwanciyarta tayi sannan tajawo robar tacigaba da shan abunta.
Wacece Deejah?
Khadija Ahmad shine cikakken sunanta, barrister Ahmad babban lawyer ne shine mahaifinta sai doctor zainab itace mahaifiyarta su biyu iyayensu suka haifa ita da yayarta khausar iyayensu basuda buri da yawuce suga ‘ya’yansu sunyi karatu duk wanda zaizo neman auren ‘ya’yansu basu bashi suna iya kashe ko nawane domin ganin ‘ya’yansu sunyi karatu basu damu da yanayin abokansuba da kalar rayuwar da yaran suke,
Saidai abinda basu saniba shine tun yaran nasu suna secondary school suka fara shaye-shaye da lesbian, khausar har tagama karatunta batayi aureba sai yanzu da ake shirin aurar da ita ammah har lokacin tana tare da manyan mata masu aji, deejah ma haka take harka da manyan mata kasancewar iyayen nasu basu cika zama gidaba shiyasa su deejah su ma suke fita sukwana inda sukeso batare da sanin iyayensuba wannan kenan.
Sapna dakyar tabud’e idonta tare da tashi zaune jinta take wata iri kamar ba itaba, kallon deejah tayi da taketa dannar waya hankalinta kwance itama deejah kallonta tayi batare da wata damuwaba tace har kin tashi, hamma Sapna tayi sannan tace deejah menene kika bani nasha? Kar dai kice min giya ce kika bani?
Shuru deejah tayi batace komaiba,
Cikin tsawa sapna tace tambayarki nake deejah kibani amsa,
Batare da damuwaba deejah tace kina tunanin zan cutar dake ne sapna?
Harararta Sapna tayi tace ai ga alamun hakan nan nagani wlh deejah kin cutar da rayuwata da har kika sa nasha kayan maye kije ke da Allah, Kuma daga yau inaso kisani babu ni babu ke, wucewa sapna tayi fuu taje tasamu abun hawa takoma gida ko da ta isa gida ta ji dad’in rashin tadda ummah da tayi dan haka saida tayi wanka sannan tayi sallah tare da neman yafiyar ubangijinta bayan ta gama batabi ta kan abinciba takwanta bacci saboda baccin daman bai ishetaba,
Ko da sapna tatafi deejah bata damu da hakan ba saima murmushi da tayi tace lallai Sapna har yanzu bakisan wacece deejah ba kina tunanin zan barki a haka kinyi kuskure muje zuwa.
Sapna ba ita tatashiba sai gab da magrib shima ummah ce tazo tatadata tana ta fad’an baccin la’asar d’in da sapna takeyi.
Tun daga ranar sapna ko ta je school ba ta kallon inda deejah take deejah tun abun baya damunta har yazo yafara damunta domin ta san duk wani karatun da take a school d’in sai da taimakon sapna take samu tana wucewa,
Ranar Monday bayan lecturer ya fita nan mutane suka fara fita daga class d’in sai d’ai-d’aya suke zaune daga cikinsu har da sapna a ciki, deejah ce tataso tanufo inda take tare da zama kusa da ita, ko inda take sapna bata kallaba tacigaba da dannar wayarta, Deejah cikin kwantar da murya tace sapna dan Allah kiyi hak’uri da abinda nayi miki wlh nima ba a son raina hakan take kasancewa da ni ba, harararta Sapna tayi tace wlh bana fatan abinda zai k’ara had’ani da ke,
K’ara marairaicewa deejah tayi tace baidace kice min hakaba sapna wlh ba a son raina hakan takasance ba, nima ina da burin daina wannan rayuwar ammah na kasa dan Allah kar kigujeni sapna ke fa da iliminki kinsan illar yin hakan kuma baki tunanin zaki iya taimakamin wajen ganin na daina wannan mummunar d’abi’ar tawa?
Shuru sapna tayi kamar tana tunani chan sai tace shikenan deejah daman shi zaman tare ya gaji haka idan kaga d’an uwanka ya fad’a wani hali baidace kagujesaba a lokacin ya kamata kataimaka masa wajen ganin ya ku6uta, wlh deejah ni tsakani ga Allah nake zaune da ke domin ina jinki har cikin zuciyata, ammah ke deejah me yajawo miki fad’awa cikin wannan halin alhali da kyaunki da iliminki kuma babu abinda kika rasa a wajen iyayenki meyasa kika 6ata kanki da shaye-shaye?
Murmushi deejah tayi tace nima ba ason raina hakan takasancee da niba dan Allah kar kigujeni kitayani da addu’a idan da rabo zan daina, sapna cike da tausayin deejah tace hakane insha Allahu zaki daina ammah ya kamata kirage sha kinga sai yazamana nan gaba zaki iya dainawa gaba d’aya,
Cikin jin dadi deejah tace nagode sosai sapna da kika fahimceni wlh ke yarinyar kirkice.
Murmushi Sapna tayi tace kar kidamu deejah ammah wlh kika k’ara neman cutar da rayuwata ke da Allah kuma sannan duk wata alak’ar da ke tsakaninmu zata watse, dasauri deejah tace wlh na yarda sapna nagode sosai da kika fahimceni.
Tun daga ranar Deejah tarage sha gaban sapna inma zatasha toh saidai tatashi taje wani wajen tasha sannan tadawo, Sapna abun har mamaki yake bata domin har lokacin bataga alamun chanji daga deejah ba sai ma abinda yacigaba dan agabanta deejah har waya take da mata, saidai ko ya taji zuciyarta tana shirin kawo mata wani zargin game da deejah dasauri take janye tunanin,
Deejah sau Biyu tana zuwa gidansu Sapna ammah ita sapna ko da sau d’aya bata ta6a zuwa gidansu ba, sapna bata ma da lokacin kanta da tadawo Boko tahuta taci abinci saitayi wanka tashirya tatafi islamiyya sai dare takeda lokacin kanta, umman sapna da taga deejah hankalinta bai kwanta da yanayin deejah ba, ko da tatuntu6i d’iyarta da maganar, Sapna cewa tayi ummah wlh deejah d’iyar kirkice kinsan da ace akasin hakane da niba ba zan zauna da itaba, dogon numfashi ummah taja tace hakane sapna domin na yarda da tarbiyar da muka baki dan Allah kar kiwatsa min k’asa a Ido, kar kiban kunya, Murmushi Sapna tayi tare da kwanciya jikin ummah tace insha Allahu ummah ba zan ta6a baki kunyaba saidai kiyi alfahari da ni addu’anki kawai nake buk’ata, ummah shafa kan d’iyar tata tayi tace Allah yayi miki albarka, cikin jin dad’i sapna tace Ameen ummanah,