JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Zubanta ido yayi Yana kallon yanda duk ta tsorata yaji dadin hakan ya shafa kansa yace “da nayi niyyar fadawa Baffa’am dinki Amma idan kikayi alqawarin bazaki qara zuwa ba to zan rufa miki asiri ke qilama ya sani fah don duk motsin da zakiyi abune me sauqi su sani din” batasan sanda tace “insha Allahu baima sani ba bakuma zai sani ba bazan qara zuwa ba”
Yaji dadin hakan yace “ok meye kukaje yi a dakin Muntaz?” Nan taji wani dukan saukar aradu ta dago suka hada ido mugum kwarjini ne dashi shima kamar Baffa’am dinta duk iyakar zille zillensu idan aka hadasu dashi basa iyayi masa qarya, cikin in…Ina tace “ha….hqr mukaje mubashi yaci gaba dayi Mana lesson shine yace wai saidai na rinqa biyansa Wai banida kudin biyansa Amma inada kadarar da tafi kudi ni na kasa gane me yake nufi Ya Kareem ko kai ka gane?……”
“Wht?” Ya furta da qaraji ta dago da sauri ga mamakinta sai taga gabadaya ya hargitse jikinsa har wata rawa yakeyi idanunsa sun kada sunyi jawur ya dafe kansa yace “innanillahi wa innah ilaihir raji’un”
Daidai lkcn Muntaz ya fito cikin shirinsa na tafiya qwallo hangosu tsaye yasashi daure fuska ya nufi motarsa ya bude zai shiga Kareem ya daga murya ya kirasa ya tsaya batare daya juyo ba, matsawa yayi bayansa yace “bantaba tunanin akuyancinka yakai ka rinqa farautar lalata rayuwar Aminatuh ba sai yau so inason kasani wlh tallahi idan naji ko naga wani abu akasin daidai ya faru da Juhud billahil lazi saina tona maka asiri dan iskan banza dan iskan wofi duk kuyangin gdannan da bayi Basu isheka ba saika tsallaka kan yar Amana…….” Dakatar dashi yayi yace “dakata Mal kaima fah abinda nakewa shine kakeyiwa duka dodo daya mukewa tsafi aikin banza kaine kake tunanin ci da addini ni tun tuni na dade da fahimtar ka dade da lalube…….” Wani gigitaccen mari ya sauke masa ya shaqesa suka kama kokawa ya rinqa gwara masa kai a jikin bishiya Mai Martaba dake tahowa ya hangosu ya iso da sauri shida dogaransa daqyar ya bambare hannun Kareem daga wuyan Muntaz, duk da haka Muntaz bai rusuna ba cewa yake wlh ko kanaso ko bakaso tunda nayi niyya saina aikata qarshen kishi kasa a daura maka aure da ita yau dinnan ko a gdanka take saina mayar da yawuna saidai idan mutuwa nayi”…………

THIS BOOK IS NOT FREE… REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566

DON ALLAH IDAN KIN/KA TURA KUDINKA BANA BUQATAR DOGUWAR GAISUWA KAWAI EVIDENCE OF PAYMENT DA SUNAN LITTAFIN DA KIKESO NAKE BUQATAR GANI KO BANA ONLINE KIBARMIN IN NA HAU ZAN GANI KUMA ZANYI ADD NAKI A GROUP DINA COURSE MUTANEN DA YAWA.

Oum Hairan
[7/18, 6:49 PM] Oum Hairan: JH011

(Pure love sex nd romantic story)

Free page ya qare idan kinsan baki biya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki

Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566

Cikin fusata Kareem yake qoqarin qwacewa yana huci Yana cewa “an fada maka kowa ma irinka ne mara Imani mara tsoron Allah Wanda zina tayiwa kanta cikin rayuwarsa” rirriqeshi suka sakeyi Dogari Ado ya kama Muntaz yasa a mota suka fice asibiti yakaishi akayi masa dressing din wajen da Kareem ya faffasa masa kai suka juyo sai huci yakeyi Yana furzar da iska baqin ciki ya hanashi furta ko kalma daya, Wai akan wannan tsintacciyar yarinyar Kareem ya fitar masa da jini wani huci ya furzar ya dunqule hannunsa ya daki dayan dashi yace “wlh saina wargaza wannan yarinyar tunda abin ya zama rashin mutunci ni zaaciwa mutumci akan wata banzar bafulatana mara galihu”
Shidai Ado bai kulasa ba har sukaje gda fada suka wucce domin amsa Kiran Mai Martaba acan suka tarar da Kareem suka watsawa juna wani mugun kallo na kiyayi kanka, Mai Martaba ne ya nunawa Muntaz guri ya titsiyesu akan su fada masa meye ya hadasu har suke neman illata junansu?” Kareem irin mutanen nan ne masu baqar zuciya idan ransa ya baci baya mgn shikuma Muntaz ko hauka yake bazaice don yayiwa Juhud tayin shaidana bane yasa aka illatashi, tsawa Mai Martaba ya daka musu yace “ku tashi ku bani guri tunda bazakuyi mgn ba sakarkaru kawai” miqewa sukayi kamar zasu bangaji juna suka fita a daidai inda zasu rabu kowa ya shiga bangarensa Muntaz ya dafa Kareem yace “mu hadu a filin qwallo sabon wasa zan take leda ko ta tsiya kota tsiya tsiya”

Murmushi Kareem yayi sai yanzu zuciyarsa ta fara sauka yace “bazan hanaka mummunan tunaninka ba saidai inaso kasani ita zina yado takeyi idan kayi da yar wani zaayi da taka idan kayi da matar wani zaayi da taka kazalika idan kayi da qanwar wani zaayi da taka wannan kadai ya ishi me hankali nutsuwa Aminatuh ba kowa bace marainiya ce me rangwamen gata idan da Allah yaso ta lalace saiya barta tayita galantoyi a duniya har ta samu abokin lalacewarta so baiso hakan ba saiya jefata hannun Big Cele duk da gurbatar yanayinsa ya kawar dakai gareta domin riqe amanar Allah kullum abinda yake fada a kula da ita itadin tanada qarancin hangen nesa kaico abin tur wai ace a gdannan zata lalace……”
Dakatar dashi yayi da cewa “Dama kaje ka dauki speaker ka fara tafsir a masallacin fada qila da ka samu sadaka Dan m qauye kawai da ya kasa fahimtar rayuwa” shigewa yayi part dinsa ya banko qofar yabar Kareem tsaye cikin tsananin mamakin wannan qazamar rayuwar ta yan’uwansa qwafa yayi ya shige dakinsa ya fada gado Yana juyi tabbas akwai aiki a gaban maza shikam da Abba zai barshi daya nemi auren Juhud cikin lkc qanqani kodon ya tseratar da ita daga sharrin Muntaz Amma yasan abune ma bame yuwuwa ba tunda bai gama karatunsa ba a burin irin na Mai Martaba ba mazaba yaransa mata na bayayi musu aure sai sun hada degree certificate maza kuwa sai sunyi Masters degree ya samawa kowa gwaggwaban aikin yi.

Lumshe idonsa yayi cikin yanayina tausayin kai da Kuma abar qaunar tasa shikam zaiyi qundunbalar furta mata koda bazaa Basu damar soyayya ba Allah ya jarabceshi da muguwar qaunarta baiji a ransa zai iya sakacin Bari ta kubce masa ba, da wannan tunanin yaji ana Kiran sallar magrib ya tashi ya fita domin zuwa masallaci ya jima a masallacin sannan ya tashi ya nufi cikin gdan a falo ya tarar dasu dukkansu suna kallon wani Indian series gabadaya hankalinsu ya bayu ga kallon da sukeyi duk cikinsu babu me motsin kirki.
Ya jima tsaye akansu bai gano Juhud ba can ya hangeta kwance a kujera da littafi a hannunta da alamun nazari takeyi, zuciya yaja ya nufeta inda Momy tabisa da kallo ya tsaya akanta ya sanya hannu ya zare littafin ta dago idanunta ta saukesu akansa ta kawar dakai, sake jan numfashi yayi ya zauna a gefenta yace “Ina Ya’isha da Amrah?” Miqewa tayi zaune ta duba bata gansu ba ta dawo da dubanta gareshi tace “bansan sanda suka fita ba” jinjina kai yayi yace “wato Addah kun qyale yarannan suna abinda sukeso babu me iya tsawatar musu basuda aiki saidai suyi wanka su fice su kwaso wannan su kwaso wancan samari saikace budurwar karya idan anyi mgn Momy tace farin jini ne don Allah wannan wacce rayuwa kuka zaba musu a matsayinsu na mata da zasu tafi gdan wasu?”
Dubansa Addah tayi tace “nikam bansan da wanne yare zan ganar dakai ka gane ba Abdulkareem wlh nafika jin ciwon wannan abin da yarannan sukeyi to baka isa kayi mgn bane kawai sun samu daurin gindi daga Mai Martaba abinda sukaga dama shi sukeyi kayi mgn suje su fadaka dashi yazo yayita fada shiyasa na tattara na zubansu ido kaima yanzu nemanka yakeyi sunje sunce masa kaine ka hana Aminatu zuwa chilling”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button