NOVELSSARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL

SARKA COMPLETE HAUSA NOVEL BY ZAINAB IDRIS MAKAWA

SARKA FADI KA RIKICE

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI.
GODIYA YA TABBATA GA ALLAH MAI KOMAI MAI KOWA DAYA BAMU IKON GANIN WANAN LOKACIN MAI DARAJA DA ALFARMA GA MUMINI WANDA YASAN KANSHI DA IMANI DA ALLAH DA ANNABIN RAHAMA S A W. ZAI RIKE ABINDA MUKA KARU DASHI A CIKIN WANAN WATAN NA RAMADAN MAI DARAJA DA DAUKAKA GA MUSULMI
INA MIKA TUNINA GUN YAN UWA MUSULMAI DA MU RIKE IMANI DA TUBANB DA MUKA ROKO GUN ALLAH ALOKACIN IBADUN NA WATAN RAMADAN DA FATAN TSORON ALLAH DA KOYI DA SUNNA ZAI TABBATA A ZUKATAN MU HAR ABADA UBANGIJI KABA MU IKON RIKE IMANI A ZUKATAN DAYI MAKA BAUTA TSARKAKKE A RAYUWAN MU ALLAH KA BAMU CIKAWA DA IMANI.
YAN UWA ALLAH YASA IBADIN MU KARBABBE NE A GARE KA AMIN YA ALLLAHU.

Mama Maimuna wace akafi sani yanzu da suna mamu don canza mata suna da yaran ta sukayi daga maimuna zuwa mamu.
Tana duke tana sharan dakin ta don al,adanta ne tunda safe zata gyara daki da zaran ta gama ibadan ta na safe kafin tayi komai zata gyaro daki har zuwa wajen part din ta.
Duk da masu aiki dake gida bata amince da gyaran su ba kasancewan ta mai kishiyoyin da ba a zaman lafiya a gidan don kishi irin na mata da muke rikewa kamar ba gobe a rayuwan mu.
Sai dai duk aikin nan da take hankalin ta yana gun yar ta dake cikin wani hali a can garin da yanzun zaman shi ya zama mata tari a rayuwanta.
Kasancewa auren ta na farko mijin ya rasu ya barta da yarta a lokacin yar shekara goma a duniya wanan mutuwan ne ya kawo sanadin rabuwan hjy maimuna da yarta tillo da suke so a rayuwan su ita da marigayin mijin nata.
Wanda hakan yayi sanadiyar kara auren ta a yanzun wanda sanadin mutuwan ya jawo mata auren gidan da ta guda tun farko a rayuwan ta.
Sallaman hadiye ne ya katse mata tunane da aikin da takeyi a yanzu, hadiye ita ma kamar yar uwa take a gun maimuna wace itama auren ta ya mutu tana zaune a gidan dan uwan ta a yanzu tare da yaran ta biyu yan mata.
Hadiye ta karaso cikin dakin tana murmushi tare da fadin kai sarkin tsabta gari ya waye ke nan kin shiga hada hadan gyaran guri duk da ba wani dattin a zo a gani a shiyan naki.
Wanan tsabtan naki yake saka a kullun hankalin yayana yana gare ki don tsaban tsabta da iya kwaliyan dake boye maki shekarun ki a kullun kina komawa kamar wata yarinya can.
Murmushi hjy maimuna tayi a lokacin da take aje tsimyan hannun ta tare da zama zaman lazy chair din dake gefen ta a dakin.
Kai Anty hadiye harda ke gurin wanan sherin kuma da ake min a gidan nan ko gaisuwa babu zaki tare da zolaya tunda farar safiyan nan haka ?
To ina kwana ya dare ya kuma yarana suka kwana tana tambayan hadiyen don kawar da wanan maganan a lokacin.
Lafiya kalau muka tashi kin sai dai kin san Allah dama nace wa umma yanzun haka kin tashi kina nan kina wanan aikin naki na gyare gyare tun da safen nan.
Kin san fitina irin na gwagwan ki tun sallamay sallah take fadin wai inzo in dubaki tunda yau ba a turaka kika kwana ba sai kizo ki shafa mata maganin ta.
Murmushi hjy maimuna ta sake a fuskanta tare da fadin ai da kun kirani a waya don tun dazun nake falke ai kin san ban iya komawa barci idan na tashi sai kuma wani daren idan Allah ya kai mu.
Tare suka fito zuwa sasshen Amma tshowar gidan wace gwagoce gun hjy maimuna din kuma mahaufiyar mai gidan nasu ke nan.
Kallon saura part din dake rufe Hadiye tayi tare da fadin su wa yan nan basu ma san Allah yai dare gari ya waye ba sai ta hantse masu zasu tashi daga su har yaran nasu ba wanda ke tuna Allah.
Da sauri hjy tace kai tun da safen nan zaki daukarwa kanki nauyi da bai shafe ki ba a cikin su ai babu yaro a yanzu ko ?
Basu da abin yi may zai fitar dasu da wanan sanyin hakan waje , hadiyen tace rashin sanin ciwon kai dai .
Daga hakan ba wanda ya kara tofa wani zance kuma a cikin su don inda sabo sun saba da galin hjy don bata yarda ai maganan kishiryata da ita ko kadan da wuya kaji bakin ta akan abokan zaman ta.
Duk da su a nasu bangaren da zancen ta suke kwana suke tashi a gidan sun kawo karar tsanan duniya sun dora mata akan auren dan uwan nata da tayi.
Wanda ita in har a so ranta ne ba zatayi shi ba sai dai fin karfin ta da iyayye sukayine aka yanke mata wanan hukuncin ba auren shi din.
Har yanzu Allah ya azurta su da yara uku mace daya da tagwaye maza biyu data yaye duk hakan bai sa sun daina kishin ta ba.
Farkon da ta haifi mace dashi tasha gori da zunde a guri kishiiyoyin nata wai an kawo wace zata cika masu gida da diya mata.
Daga baya kuma da Allah ya azurta ta da diya maza biyu lokaci daya sai kishin su ya tsanan ta a kanta wai zata cika masu gida da diyan baya don su sun gama haihuwan su.
Wanan surutan kamar bata san sunayi ba don bata kula zancen su zaman ibadan ta take da mijin ta hankali kwance bata shiga tabgan kowa a gidan sai abinda ya shafe ta.
Basu da suke kishiyoyin ta ba abin ya tsaya har yaran gidan sun kwashi mugun akidan iyayyen nasu suna gwada mata ita ba uwa bace a gare su .
Gwagon ma da suke kiranta dashi yayin zawarcinta a gidan yanzu sun soke sun koma kiran ta da hajiya mamu ko mamu kamar yarda yarta Fatima ke kiranta da tazo masu hutun sati biyu.
Wanda a lokacin wanan hutun daga hajiyan har yar tata sunga tsangwama na wullakanci a gurin mutanen gidan sai agun mai gidan take samun sauki a haka dai tayi hutun ta ta koma gurin kakanta dake rikon ta can Azare.
Tun wanan karon bata sake dawowa kano hutu wurin mahaifiyar tata ba sai dai dan abinda ta samu ta aika mata dashi can.
To gashi yanzu kakan nata dake rikon ta ba lafiya zaman ta ya koma gidan babban danta dake misau da zama wanda tarbiyan gidan bai kwantawa hajiyan a rai ba sam.
Da wanan tunanen take kwana take wuni a ranta tun da labarin hakan yazo mata hankalinta yaki kwanciya da zaman yar tata a can don kada a lalata mata yarinyar.

Amma ce zaune a inda ta gabarta da sallah safe ta mike kafuwan dake mata ciwo tana dan tabasu a hankali don taunar da kafan ke mata suka shigo suka samay ta a hakan.
Sallaman hjy maimu yasa Amma dago kai ta kalli kofa shigowa sashen nata tare da fadin yar albarka yanzu nake zancen ki a raina wallahi.
Na dauka ai wanan maigardaman kamar mutanen farko bata je kiran ki ba in dogara in samay ki da kaina.
Hjy tana murmushi tace haba gwago hadiyen ce kamar mutanen farko aiko hadiye bata da gardama ko mussu ta tafi mun dai tsaya gaisawa ne da ita.
Yo na sani tunda ciwon ba a jikin ta yake ba suna gani kamar wasa ne kece kadai a gidan nan kike tausaya min kan kafan nan nawa.
Shiyasa ban yarda kowa ya taba min kafan idan bake ba don har da gayya suke min tausa kinga jiya da kikai min da dare da maganin nan da kika dafa min na samu barci sosai.
Kasa hajiya maimu takai ta fara gaida gwagon nata tare da tambayan lafiyan kafan nata tana kokarin kai hannun ta saman kafan da tsohuwar ta mike tare da fadin .
Gwago sai nake ganin kamar hauwan da kafan yayi ne yake sauka a hankali , sai da ta sake ajiyan zuciya tace nima hakan nake gani yar nan.
Don yau da kaina na je ban daki ba tare da na rike komai ba kin ga ke nan sauki na samuwa gare ni ai.
Allah yasa saukin yafi haka gwago hjy tace tana zama a kasan tare da mayar da hankalin ta kan kafan tsohuwar tana bi da kallo a hankali.
Hadiye ce tace tunda ga maimu tazo barin tafi in watsa ruwa in dawo tana fadin haka ta fice dakin ta barsu su biyu.
Addu,a take ma kafar kamar yadda ta sabayi duk safe hakama da dare kafin su kwanta take bin kafar tsohuwar da addu,a wanda hakan ke ma tsohuwar dadi sosai don sanin addini irin na yar dan uwan nata tilo da ke a hannun ta tun bayan rabuwa da mahaifiyar da mahaifinta yayi.
A wana lokaci ne ya dauko ta ya danka hanun yar uwanshi wace yake ganin zata rike mashi ita amana wanda har gimanta zuwa yanzu take a karkashin gwagon nata.
Wanda gwagon nata take ji da ita a matsayinta na yar dan uwanta a firin ta tun farko bata so auren ta da mijin ta na farko ba taso cikin yaranta maza uku da take dasu ta sai hakan bai faru ba don fitowan wani can dake son yar tun bata karasa mallakan hankalinta ba .
Dole ba don taso ba ta yarda da auren ta a wani ashe zaman ba nai dorewa bane Allah yayi ikon shi a kansu.
Suma a can azare sun so rike maimuna kada ta fita gidan don kyawawan halin ta sai dai hakan bai samu ba don gwagon nata da ta sa yar nata a gaba tazo da ita kano ta karasa rakanan ta a gabanta don hankalin ta yafi kwanciya.
Bayan gama wankan hjy maimuna ne taje karo ilimi a makarantan FCE don ta kawar da kadaicin dake damun ta inda wanan lokacin ne gwagon nata ta fitar da kudirin ta nason hada yar tata da wani daga cikin diyan ta.
Inda karamin nasu ya nuna shi matar shi ta ishe shi tun a wurin sai shi Alhaji sani ne ya nuna sha,awan hakan a kanta ya kawar wa yan uwan nasa da gardama ya nuna shi zai aure ta tun farko yaso hakan Allah ne bainufa ba.
Amma taji dadi wanan zancen sosai don abinda takewa yar tata kwadayin samu ta samu do yafi sauran kwaciy hankali da samu sosai.
Tasan wahalan yar tata ya yanke do haka zata kwantarwa yar tata da hankali don su zauna lafiya duk da tasan akwai badakala a tsakanin zama da abokan zaman don gidan nasa ba kwanciyan hankali kowa jin kanta takeyi.
Wanan ne ma yasa yake so ya kara aure sai ga wanan zancen yazo mai a saukake ya yayi saurin yin na,am da zancen mahaifiyar su ya karbi auren yar uwar ta shi don maimuna mace ce da kowani namiji zaiso zama da ita.
Duk da yasan akwai aiki a gidan shi don rashin hadin kan matan shi da babu shi a lokacin bai hana shi kwadayin saka yar uwan nasa cikin iyalin nasa ba duk da yasan akwai matsala a yin hakan.
Daga hjy maimuna har Alhaji Sani sun fuskanci matsaloli da dama a wurin iyalin shi farkon auren su sai da ya jajirce masu suka samu lafiya ta hanyan tura kowace gidan su ta kwana biyu a can aka zauna lafiya.
Wanan zuwan gidan da sukayi yasa kowace ta shiga hankalinta don sun san komai zai iya faruwa idan sun matsa fitina akan kishin yar uwan tasa.
Ba shi da hajiya maimuna suka fuskanci wanan matsalan ba har Amma da take tsohuwar gidan ta fuskanci matsaloli da dama a wurin sarakkan nata wanda dama tasan da hakan.
Ada can baya Amma a gidan ta wanda mijin ta ya bar mata take zaune sai daga baya da jikin tsufa ya fara tsanan ta mata Alhaji Sani ya dawo da ita a cikin iyalin shi.
Farkon dawowan ta gidan sun nuna rashin amincewan haka don a ganin su Amma tana nuna masu wariyan akan yar tata .
Wanda sune suka ja hakan don haketan da sukayi a cewan su itace ummul,abasin kulla auren mijin su da yar uwan tashi.
Inda ita kuma hajiya maimuna ke nuna mata kulawan zumunci da nuna halin tarbiya a gareta wanda hakan yana kara tunzura zukantan yan uwan zaman nata.
Don yadda take matukar kulawa da tsohuwan yana ma mijin nasu dadi sosai har bai iya boye hakan ko a gaban kowa wanda hakan ya kara ma hjy maimunan daraja a idon kowa.
Amma dake kallon ta na dan lokaci ta nisa tare da fadin wai may kike tunane haka ne yar nan tun dazun nake magana dake kinyi nisa ga tunane.
Kkari kakaro murmushi hjy tayi a fuskanta tana gyara zaman ta tare da fadi babu komai gwago tana so kawar da tambayan da tsohuwar tai mata.
A, a kinga yar nan tun jiya nake ganin ki a wani hali kina kokarin boye min babu komai idan baki fada min abinda ke damun ki ba wazaki fadawa.
In dai halin abokan zaman nan naki ne ai yaci ace yanzu kin saba da halin su dai ko ko kuma shi sanin ne yake maki wanin abin ban sani ba ?
Saurin girgiza kai hjy tayi tare da fadin a, a gwago halin su ai inda sabo yanzu na saba da shi a gidan nan shi kuma yaya tsakanin mu dashi sai godiya da sam barka don bai rage mu da komai na rayuwaba a gidan nan.
Cikin jin dadi Amma tace to ai shi na gani yo Allah na tuba kishiya idan ba taga ka fadi ka mutu ba ai kiyayya ba zai kare ba a tsakanin ku.
Gama ke da suke ganin ki shigo daga baya ciki su kin na kokarin fin su da komai a gidan nan ai dole su sakaki a gaba haka.
Gwago ba komai wallahi dama zancen yarinyar nan dai ne ya tsaya min a raina hankalina yaki kwanciya da zaman ta a gidan yaya da sukeyi a misau yanzu.
Don babu tarbiya sam a gidan nan ko wani yaro gaban kan shi yake babu mai kwaba mashi ki ga dole hankalina ya tashi don yanzun ne lokacin da ya dace ta samu tarbiyan kwarai a rayuwan ta.
Zancen dai A ruwa ne ke ban kikaki sake ranki dashi yar nan ina zaune take da kakanta a gidan kina ganin zata saka mata ido tayi halin yaran gidan ke nan.
Gwago ba zaku gane abinda nake nufi bane yarsu ce ai komai zasuyi mata daidai ne a gurin su to amma ni abinda zaije ya dawo nakewa gudu ba wani abu ba can.
Haba yar nan ana baki kina roko addua ya dace mu bita dashi a duk inda take mutuwa ce mai yake kauna ta raba ku da ita.
Da mahaifinta yana raye ai da duk wanan bai taso ba yanzu to rabo yana kashewa yana rayawa rabon yaran nan ne ya kashe mata nata uban.
Sallaman Alh sani da ya shigo dakin gaida mahaifiyar shi da kwana ya samay su a hakan kallo daya yai masu ya gane suna wani magana ne mai muhinmanci a tsakanin su.
Sai da ya zauna ya fara gaida mahaifitar tasa tare da tambayan lafiyan jikin ta yana mai mayar da hankakin shi a kafanta dake mike.
Muryan hjy maimu ne ke gaida dashi da kwana inda ya dago yana amsa mata a cikin kulawa tare da tambayan lafiyan yaran shi.
Ta amsa da Alhamdullahi lafiya muka kwana suna barci kodana fito yace dama ai ke ke nan kullun kiwa mutane wayau ki kwashe ladan farko a wurin hajiya.
Murmusawa tayi don jin abinda ya fada mata din kafin tai magana Amma ta karbe da fadin yar albarka tafiku kaunane shiyasa.
A cikin raha da jin dadi yace to yau dai gaskiya tayi halin ta tunda hajiya ta fadi gaskiya dama mun sani kin karbe muna ita ai.
Suka sa dariya ga baki dayab su a dakin inda yace da alama dai wani magana mai muhinmanci kuke tunda safen na haka dai ?
Baki Amma ta tabe tare da fadi ba wani magana bane sai zancen yar nan dai A ruwa da taki kwantar da hankalin ta akan shi tu lokacin da taji suna Misau ita da kakarta taki kwantar da hankalin ta kan zama su can din.
Sai da ya mayar da kallon shi gun hjy a cikin kulawa yace da ita,
Why maimu, ina gun iyayye ta take a can din may zai sa ki tayar da hankali ki kuma ina mun gama wanan maganan dake tun ranan ?
Kanta dake kasa ta dago tana kokarin mayar da hawayen dake barazanan fitowa daga idanuwan ta tana fadin ba hakana bane yaya.
Kwata kwata hankaliba bai kwanta da zaman yarinyar a gidan bane amma ni ba naki bane da zaman nata a gurin su ai su din iyayyen tane na jini.
To kin san da hakan may zai tayar maki da hankali kuma yanzun kan wanan maganan sai dai idan kina boye muna wani abinda bamu sani bane a can.
Da sauri hjy maimu tace cikin girgiza kanta a, a yaya wallahi ko daya don kawai tarbiyan da yarinyar zata taso a cikin sane nake jawa nan gaba.
Dan murmushi ya sauke a fuskan shi irin ta manyan da suka gama sanin duniya tare da fadin yanzun dai na fahinci yar ki hajiya.
Ta fi bukatan rikon yarta ya dawo hannun ta ke nan hakan zaifi kwantar mata da hankali nake gani.
A sanyaye ta amsa da fadin hakan nake nufi sai dai kuma ina tunanen inda zata zauna isan na dauko tane don nasan ba zasu hani ita ba idan har na bukaci hakan din,
Wanan wani irin magana ne kikeyi ke a ina kike zaune yanzu koda baki gidan nan ai Fatima mai zama a gidana ne balle gaki a gidan baki daya.
Amma ta karbe da fadin yar nan tana da gaskiyar ta ubana hutu kawai yarinyar nan tazo ba a kwshe lafiya da matan ka ba ina ga tazo da zama baki daya a gidan yanzu ?
Haba hajiya yaya kuke wanan magana haka ne kamar ba gidana ba yata ce fa ta cikina Fatima ko ban hada alaka ta jini da uwarta ba ai na hada na aurataya da uwar ta yanzun ko ?
Kafi wani yai magana a dakin sallama hajiya Jumai uwar gidan Alh sani ne ta shigo dakin gaida Amma da kwana.
Wanda hakan doka ne daga maigidan da ya kafa wa kowa a gidan babba da yaro duk safe dole kowa yazo dakin mahaifiyar tashi ya gaida ita da kwana kamar yadda ya tsara masu a gidan.
Amsa mata sallaman sukayi lokaci guda inda ta karaso tana watsawa mijin nata da hjy maimu data samu suna wani maganan wanda bata san ko na may ye ba a dakin.
Ciki kishi daya motsa mata irin na mata ta gaida mahaifiyar tashi da kwana babu tambayan komai ta juya zata bar dakin sai Amma ce ke tambayanta kwanan yaran ta don ta gama fahintar halin da ta shiga lokacin.
A dakile ta amsa da suna lafiya har ta juya hjy maimu ta fara gaida ita da fadin yaya ina kwana kamar ba zata amsa ba ta dai amsa a cikin saurewa da lafiya kawai ta juya ta fita.
Kai Alh sani ya girgiza bayan fitan ta tare da mikewa do barin dakin yana fadin ni zan fita hajiya ina mu kare wanan maganan ke nan ko ?
Kallon hjy maimu Amma tayi tare da fadin ai ga tanan idan ta gamsu da maganan ka sai a saka lokacin da za a dauko yarinyar ko ?
Sai lokacin ta dan murmusa tun fara maganan yarinyar da sukayi tare da fadin a,a magana yana hannu uban yar dai gwago ni na isa in saka rana da kai inyi rashin kunya kuma ?
Ko ya manta a gaban mahaifiyar shi yake ya dan kalle ta cikin kulawa tare da fadi see you kamar ba ita bace ta burkicewa mutane yanzu kan yar tata.
Ranshin kunya ai kin riga da kin gama ko tunda kin nuna muna kin fimu son yar har hakan yana dariya ya fice daga dakin.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button