JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Kada masa kai tayi ya zaro kudi a aljihunsa ya ajiye mata yace “is ok akwai ma’aikata a gidannan idan na fita zanyi musu mgn zasuzo kowa zai gabatar miki da aikinsa idan kina buqatar wani abu ko baby akwai dan aike saiki bashi” jinjina kai tayi ya sake sunkuyawa yayi kissing Muneefah ya fice tana binsa da kallo ita mamakin sanyinsa takeyi cikin kwanakin nan ta lura ya sauko sosai don ita kanta tasan da Rasheed din dane rainin hankalin da takeyi masa da tuni ya ladabtar da ita Amma yanzun ta fahimci kamar bama abun na damunsa.
Da wannan tunanin ta miqe ta shige bayi tayi wanka ta gyara jikinta ta fito tasa kayanta ta sanya dankunne ta nufi kitchen ga mamakinta a dinning ta tarar da kayan Karin kumallo ta fara budewa ko baa fada mata ba tasan aikinsa ne doya ce da taji qwai sai miyar albasa da attaruhu sai ruwan tea a flast da kayan hadi a gefe taja fasali ta zauna ta fara bawa cikinta haqqinsa taji dadin break din sosai tana Shirin tashi ma’aikatan suka shigo mace daya maza biyu suka gaisheta ta amsa musu macen tace “ranki ya dade ni sunana Jummai daga Daura Yallabai ya kawoni nan aikina shine shara da mopping da wanke² sai kula da Muneefah yace tsarin gdansa baa masa girki shine yakeyi ko Kuma ke kiyi” jinjina kai tayi dayan yace “nikuma sunana Hadi duk abinda ya shafi fita unguwa da aike zuwa waje alhakinane” juyawa tayi da dayan yace “nikuma dan ruwa ne aikina shine kula da fulawa da wanki da guga ranki ya dade sunana Badaru” yanda yayi mgnr yabata dariya tayi murmushi tace “yayi kowa yaje yayi aikinsa”

Godiya sukayi suka fita kowa ya kama aikinsa Jummai ma ta fara gyaran falon ita Kuma ta shiga dakinsa ta gyaro ta kunna masa turaruka ta fesa na fesawa ta wanke toilet ta fito ta shiga nata shima ta gyara biyun da suke rufe ne kawai bata shiga ba ta koma tayi kwanciyarta ta rashin aikinyi har daya sannan ta fito ta dora girki Jummai nayi mata hira har suka gama suka Muneefah nata wasanta tayi wanka ta shirya cikin wata atampa blue tayi mata kyau dinkin doguwar riga me aljihu tayi sallar la’asar ta kunna kallo tana kallo tana chat har biyar sannan taji tsayawar motarsa ya shigo da kaya niqi² a hannunsa Jummai ta miqe tana masa sannu da zuwa itakuwa hakimar kawar dakai ma tayi yasan tayi ne don yaji haushi yayi murmushi ya aje kayan yace “barka da gida ranki ya dade Allah ja kwana ya qara lafiya fulanin gobe” duk yanda taso da shareshi dole Saida yasa tayi murmushi tace “sannu da shigowa” cire rigarsa ta sama yayi ya rage dagashi sai singlet ya qarawa A.C gudu yace “nasha wahala yau inata qoqarin naga tafiyar nan bata ritsa dani ba Amma Saida ta fado kaina Meenah banson tafiya nabarki wlh…..” Ai tuni ta fara hada gumi ta juyo da sauri tana cizge dankwali tace “tafiya Kuma Baffa’am tab wlh aa bazaa Kuma sakani a tara ba nikam qafata qafarka”

Murmushi yayi Yana kallonta a zucci yace yar iskar qarya zanyi maganinki ta ruwan sanyi ni zakiyiwa hauka! Amma a fili sai yace “to ya zanyi Meenah Babu damar tafiya da iyali Australia sunada mugun sanyi dole sai kaje kaga yanayin gurin tukunna ko zaka dauki iyalinka Kuma ma Banda abinki mu ai zaman gaba mukeyi Inna tafi dake amfanin me zakiyimin abinda bakaso ai nesa kakeyi dashi ko?” Girgiza kai tayi ta zame qasan kujerar tace “nikam mubar batun wasa wlh nasha wahala a wancan karon har zaucewa Saida nayi Saida Mom da Mai Martaba suka rinqa sawa ana yimin addu’a sannan na dawo hankalina ya Rasheed don Allah ki million nawa ne kabasu subarmin kai a gida ni idan bamaka dashi zansai da shanuna da Kaka ya karbarmin gurin dangin mahaifi na nabaka kabasu subarmin kai kaji?” Tana mgnr muryarta na rawa.
Shima zamowa yayi ya zauna a gabanta ya riqo hannunta yanajin wani spark na jijiyoyinsa saboda rabonsa da riqe hannun mace haka shekara an tafi takwas kenan, jan wani numfashi yayi yace “kinaso na ne?” Tambayar ta daketa ta dago da sauri idanunta ya kawo ruwa yayi saurin dora hannunsa a bakinsa yace “aa ba kuka ba tambaya ce my Meenah kinasona?” Daga masa kai tayi ta fada jikinsa ta rushe da kuka tana cewa “don Allah don Allah Ya Rasheed please kada ka sake tafiya kabarni wlh zaucewa zanyi…..” Hade bakinsu yayi ya lumshe idonsa yanajin wata natsuwa na shigarsa shaidan na qoqarin tuno masa da abubuwa Yana yaqarsa daqyar yayi galaba akansa ya koreshi ta hanyar zarmewa wa tabe²nsa itakam lumshe idonta tayi banda hawaye Babu abinda takeyi ganin Yana qoqarin zaqewa Kuma tasan kowanne lkc Muneefah ko Jummai in sunji shiru zasu iya fitowa yasata janyewa.

Kafin ta gama daidaita natsuwarta ya sunkuceta sai dakinsa ya azata a gadonsa ya turmusheta tana tureshi tana komai yaqi barinta sai rawar jiki yakeyi da ta murya Yana cewa “Mee…. Meenah…. please….. Long time banci ba wlh tunda nabarki banqaraci ba banqara sha’awar ciba sai da kika dawo rayuwata kibarni naci naji da…din…ki….”
Batada mafitar data wucce qyaleshin duk da tanajin fargaba koda yake tasan duk masifar Rasheed baikai Kareem ba saidai shi dabanne Yana bata nutsuwar da takeji a ranta Babu me bata kamarta sambatunsa kadai ya isa gamsar da mace me gajeran zango, Rasheed ya mayar da qwalamarsa a wannan yammaci anci amarcin gaske taji a jikinta koda komai ya kammala gumi ta rinqa hadawa ga ciwon jiki tare sukayi wanka yanata narke mata kunyarsa ma ta kamaji saboda ta fahimci shi baya da kunya ko kadan akan wannan abun.
Bayan sunyi wanka sukayi sallar magrib da ake binsu sukayi Isha sannan suka nufi dinning sukaci abinci yanata zubanta shagwaba itakam duk jikinta yayi sanyi ta dago idonta tace “amma Ya Rasheed ka fasa tafiyar ko?” Murmushinsa na Izza yayi mata yace “sai yanda ta yuwu”

Miqewa tayi ta shige dakinta ta haye gado ta zauna ta zuba uban tagumi itakam ta tsorata da wannan al’amari batajin zata iya yarda ya tafi ya barta idan ta tuna da hakanma hawayenta nunkuwa sukeyi ita da kanta takeji ashe zuciyarta tashice har yanzu ashe Baffa’am dinta bashida na biyu har gobe a duniyarta to meye yasa da ta farajin haushinsa?”
Jinjina kai tayi tana qissima ta yanda zata fara rayuwa cikin zulumi sai ta dauki wayarta kamar ta kira Kumbo Hami ta fada mata sai Kuma taga kamar bai dace ba haka ta rinqa saqawa da warwarewa har dare ya fara nisa ta shiga tayi wanka ta dawo ta kwanta abinka da farar fata idanunta har sun kumbura koda Jummai ta kawo mata Muneefah cewa tayi taje su kwanta tare ganin kwanciyar bazata kaita bane tasata tashi ta sake alwala ta dauki qur’ani tana karantawa tana hawaye.
Shigowa yayi dakin mamaki ya cikashi jin shassheqarta ya kunna globe din da sauri yaganta rungume da qur’ani tana rera kukanta ya qarasa gareta ya zare qur’anin ya aje ya dagota ya mannata da jikinsa yace “meye kikewa kuka Meenah kinsani ko a baya bana qaunar kuka ko?” Maqalqaleshi tayi tana qarawa kukanta gunji tace “ni don Allah kace ka fasa tafiya kabarni wlh zanyi maka duk abinda kakeso” dariya tabashi sosai ya shafa kanta yace “to na fasa saime Kuma?” Rungumeshi tayi tana ajiyar zuciya tace “shikenan idan sun matsa ka bar musu aikin kawai kaji?”

Daganta kai yayi ta shafa sumarsa tace “na gode Baffa’am….” Janta yayi suka zube a gado ya fara luguiguiceta ta saki masa jiki kuwa suka raya Daren da wata irin azababbiyar qauna me narkar da zuciya sun gurji juna sosai tanajin sabuwar qaunarsa na ratsata, tun daga wannan dare komansu ya fara saituwa cikin ruwan sanyi da dabara ya shawo kanta riritashi takeyi kamar qwai bata yarda ta tabashi saboda karma yaji yanason tafiya yabarta shima mugun tattalinta yakeyi Abu daya yaso Basu damuwa tanason zuwa Daura watanni sun fara nisa tanason taje taga Mom Amma fir yaqi tun tana lallabashi har Saida suka daina mgn ta daina kulashi da ya matsa mata sai ta kama kuka tace don yaga batada galibi ne batada uwa bata da uba shiyasa yakeson ya nuna mata Mom ba ita ta haifeta ba.
Sosai ya fahimci Meenah yar sharri ce ta qaro wulaqanci dole ya shiryanta tafiya Katsina aikuwa tayita murna shikuma yayita kumburi zuciyarsa na basa kawai so take taje taga uwar mijinta ta tuno da ubar yarta Kareem idan zuciya ta raya masa haka sai kawai yaji koma me zatayi tayi bazai barta ba ranar data shirya tafi tun asuba take shiri yayi kwanciyarsa yaqi fitowa harta shirya ta shirya Muneefah ta shiga dakin nasa da sallama ya Amsa mata a ciki ta zauna tace “Baby na shirya banga kana shiri ba Kuma kace kaine zaka kaimu airport” iska ya furzar yayi miqa yace “ina zakije ne?” Da sauri ta dubesa tace “Ban fahimta ba Daura Mana” hade rai yayi yace ba yau ba…” Ai baigama rufe bakinsa ba ta miqe tana cewa “haba don Allah Ya Rasheed kada kayimin haka wlh na fadawa su Mom dasu Ya’isha yau zanzo har Sarki junior fah na fadawa yanata murna hatta Amrah da Addah Abulle sunata murna zasuga Muneefah…..” A fusace yace “shut-up Meenah nace bazakije ba yau ki fita ki bani guri dama nasan dokinki kije kiyi hirar tsohon mijinki kiji dadi ko? To bazaki ba idan kika matsamin ma wlh zan iya cewa keda Daura har abada muga ta tsiya”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button