JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Ana azumi ana shirye²n sallah ana na biki gda ya dauki harami sosai komai na bikin Baffan nata ita dasu Ya’isha suke shiryashi Basu Katsina Basu Kano siyayyar ashobin biki da kayan sallarsu kwanaki sunsta tafiya soyayya tsaksninta da Kareem tanata qaruwa dare rana yammaci suna maqale a wayar daya Sanya aka kawo mata sabuwa dal suna tsara yanda bikinsu zai kasance.
A haka aka cinye azumin ana gobe sallah tana falo tana waya Ado drive ya shigo da sallamarsa suka gaisa ya miqa mata wata leda yace “gashi inji wani soja a waje yace akawo miki” Saida gabanta ya Fadi da akace soja Mom ta zubanta ido tace “soja Kuma Amina Ina kika samo soja?” A sanyaye tace “bansani ba Mom” karbar ledar tayi ta bude ta dauko kwalin dake ciki wata rantsattsiyar wayace Sumsum me matuqar kyau da tsadar gaske Mom ta juyata sosai a hannunta ta dubi Juhud data zuba tagumi tana kallon Mom.
Sake zaro kwali na biyu tayi wasu fitinannun turaruka ne masu masifar qamshi a ciki sai tarkacen Sweet da chocolates sai wata takarda qarama dake a ciki miqa mata takardar sukayi taqi karba saima miqewa da tayi Mom tace “ungo ana Kira ki daga kije me zaace miki” noqe kafada tayi tace “Mom…..” Hannun Mom ta Dora a bakinta tace “shitttt Amina banson gardama da fada da Wanda baka sani ba ai gara kayi da wanda ka sani ko banza akwai sanayya”

Hannu tasa ta karba tanabin number da kallo hannunta na rawa ta danna wayar ta Kara a kunnenta yaja ajiyar zuciya daga yanayin saukar numfashin ta gane wayene nan take zuciyarta ta hau kai kawo a qirjinta. Bai bata damar tunanin komai ba yace “baki tausayin me tausayinki ko Meenah?” Shiru ce ta ratsa ta juya ta dubi Mom ta nufi qofar dakinsu yafi minti biyar kafin ya qara qutawa yace “banyi tunanin wannan sakayyar daga gareki ba inaji a Raina a baya idan kowa ya juyamin baya ke zaki kalleni da idanun Rahma ashe ban fahimta daidai ba Meenah meye aibuna da kika kasa maye gurbin rashin cancanta da cancanta a tunanina ko ban cancanta ba ya kamata ki kama hannuna ki dagani matsayin gwaninki…..”
Shiru yayi saboda numfashinsa da yake sarqewa yaja numfashi sosai sannan yaci gaba da cewa shekaruna 37 bantaba ji ko a wasa ina muradin rayuwa da wata mace matsayin mata ba sai a wannan gabar da qaddarar ta hadani dake tabbas da nasan cewa kedin zaki zamo masheqin rayuwata da ban fara jin tausayinki a farko ba” jikinta ne yayi sanyi da kalamansa zuciyarta ta karye bai Bari tace komai ba yace “bansan meye laifina ba don nace inasonki wlh tallahi duk duniya babu namijin da yakeyi miki irin son da nakeyi miki Meenah ba iyakar farin cikina zan fansar gareki ba har rayuwata da mutumcina duk zan iya sallamasu dominki na rantse da Allah idan ban sameki ba matsayin mata to kuwa shima Kareem bazai sameki ba saidai muyi ragas gara ki fita waje ki auri wani Amma a gdanmu ki auri qanina ki rayu dashi gani Ina bulayi Ina bazan iya ganin wannan baqin cikin ba, yess kince yanada nagarta nasan haka Ni banida nagarta Mazinaci ne ni yanzu Kuma soyayyarki ta mayar dani mashayi Kuma a haka zakizo ki rungumeni ki rayu dani dole idan kinqi bani hadin kai don Allah zaki bani don dole Meenah kiji a ranki ni mijin mace daya ne Kuma kece ko babu aure zamu rayu tare”

Cikin tsananin fusata da kalamansa tace “ya Isa Baffa’am bantaba ganinka matsayin qasqantacce ko marasshin daraja ba wlh ko lkcn da nasan kana zaman dadiro da arniya mara Imani banji na tsaneka ba Amma yanzu kalamanka suna aika saqo cikin zuciyata duk da kasancewata mara galihu na shaida niba banza bace kamar yanda kakejin izzar sarauta a cikin jininka nima inajin izza a nawa jinin saidai Ni bansan ta meyece ba da wannan nake son sanar dakai na gode da kulawarka gareni Amma bazan taba kwarewa Mai Martaba baya ba saboda jin ya isa dakai yasa yaji a ransa nima ya isa Dani ya zabamin Ya Kareem batare daya nemi shawararmu Ni dakai ba to danme Ni zan nuna masa nidin ba halattaciyar ya bace?
Numfashi taja taci gaba da cewa “bari kaji Baffa’am bazan taba canza zabi ba domin ba zabina bane na ubangiji ne saboda haka bana buqatar kalamanka ka adanasu ka fadawa Aunty Zulaihat ita zataji dadinsu Kuma zasuyi mata amfani Amma Banda Aminatuh”……. Qit ta kashe wayar gabadaya ta cillah a wardrobe tana jan tsaki Baffa’am din nata ya fara kai hqrnta qarshe to waima anayin so dolene da zai takura saita qaunaceshi bayan tariga tayi kyautar zuciyarta ga waninsa?.

Komawa tayi ta zauna a hankali Kuma take auna kalamanta sai takejin babu dadi duk da cewar gsky ta fada masa, turo qofar akayi aka shigo ta dago ganin Muntaz yasata miqewa ya zubawa qirjinta iso yana murmushi wayarsa tayi ring ya miqa mata yace “kin tara kayan dadi baby Amma na hqr na fahimci babu rabona a wannan gurin gonar manya ce” tsaki tayi ta karbi wayar ganin sunan dake kai yasata miqa masa ya matsa da sauri yace “ai baki isaba yarinya dole ki Amsa wayar nan bazaki jamin masifa ba” jifa tayi da wayar ta shige bathroom bugun duniya taqi budewa Saida taji ya cewa “taqi karba fah tama shige bayi tabarni shanye kamar maratayi”

Bata fito daga bathroom dinba Saida taji shigowar su Ya’isha ta fito tana goge idanunta da suka canza kala, da dare ma daya kirata a tata wayar da yasa aka tura masa number tana ganin numbersa ce ta dannata a silent ta koma ta kwanta washegari ta kama idi tun asuba suketa shirye²n tafiya idi sai bakwai suka gama suka fito sunata baza selfie
Suna Shirin fita ya shigo sanye da kakinsa hularsa a hannu ya sauke idanunsa akanta tare da kwantar da kansa a jikin qofar yanajan wata wawuyar ajiyar zuciya me qarfin gaske qwarjini yayi mata ta kasa motsawa daga inda take su Amrah sukayi masa barka da zuwa ya dagansu hannu tare da nuna musu hanya suka fice ta daga qafarta daqyar zata bisu ya cafko hannunta ya janyota ya shigar da ita jikinsa ya matseta sosai yanda bazata iya motsawa ba yace “barka da sallah My wife” qoqarin qwacewa taketayi da hannu daya ya hardeta Amma ta kasa qwaqqwaran motsi ya figi hannunta ya nufi sama da ita ta cake a bakin qofar ta riqe qarfen benen ya juyo ya zuba lumsassun fitinannun idanunsa akanta yace “idan Kuma nayi amfani da qarfina nace saikin shiga cikin fah ya zakiyi?” Qasa tayi da kanta ya dagota yace “banson kuka kawai maimaitamin kalamanki na jiya zakiyi” da sauri ta dago yayi mata murmushi yace “zanyi amfani da duk wani abu daidai ko rashin daidai domin naga na hanaki samun abinda kike tunanin shine ya dace dake badon na cutar dake ba saidon sama miki yanci zaifi miki dadi ki rayu da wanda yasan mutumcinki”
Dagowa tayi ta zuba idanunta cikin nasa tace “kana nufin Ya Kareem baisan mutumcina ba kai kadaine kasani?” Baitaba tunanin abinda zatace kenan ba ya tsaya cak Yana nazarin me zaice mata ta juya zata fice ya sake riqota yace ki shirya zaki rakani unguwa” hannunta ta janye batare da tace masa komai ba ta fice ta nufi masallacin suna idar da sallar ta zille ta nufi wani bangare na gdan ta zauna tana wayarta da Kareem dinta taji an cire wayar a kunnenta ta juya da sauri yayi wanka ya canza kaya cikin wata brown gezna yayi mata kyau sosai taja fasali yace “zaki?” Kallonsa tayi zatayi mgn yace “bama zabi zan baki ba dolene kizo muje” bata kawo komai ba batayi tunanin komi ba tabisa har inda yayi parking motarsa ya bude mata ta shiga ya sake mata murmushi yaja motar a guje suka fice Muntaz ne kawai yaga lkcn daya dauketa suka fice,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button