JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Da wannan ya fice Mai Martaba ya dubeta yace “likitana ya tabbatar min da zai samu sauqi fah karki damu” ficewa sukayi suka barta da kallon Kareem dake kwance kamar gawa ta juya itama ta fice kamar mahaukaciya ta nufi block nasu ta fada gado domin tabawa zuciyarta hutu daga sabon tashin hankalin daya tunkarota ga Baffa’am dinta a gabanta Amma yakasa ganeta to waima meye asalin dalilin sukurkucewarsa ne haka Shiba Mai mgn ba Amma surutai rarrara kamar Wanda ya qone a qeya miqewa tayi tare da cewa “tabbas lkc yayi da zan sakawa Mafi cancanta Alkhairinsa…..”
Tunaninta ne ya tsaya cak da tunawa da Kareem shikuma da yake cikin halin ni yasu dora hannu tayi akanta daidai lkcn da wayarta tayi ring ta wawurota Ya’isha tace “na dade inason tsegumta miki watanni biyu baya anga Big Cele a Tanzania to tsoron jagula wannan dofanannen auren naki da Ya Kareem yasa Mom ta Hanani fada miki wai Kuma yau sainaji me kankat ankawo mikishi har qasarku”
Cikin kuka tace “shine me gata ko rashin galihu yasa kukaki fadamin labari mafi soyuwa a duniyata Ya’isha ko ku fada ko karku fada Rana irin wannan zatazo gashi tazo Baffa’am ya dawo zamana da Kareem ya qare…..” Da qaraji Ya’isha ta katseta da cewa bakida hankali ne karki soma wlh Kareem yafi kowa buqatar taimakonki kinaganin fa a halin da yake” jan zuciya tayi tace “meye ribata dama uwarsa ta rantse indai na haihu saiya sakeni to kafin ma na haihu zanbar mata gidan danta nima a dole nake zaune don halacci” magana Ya’isha keson yi mata ta kashe wayarta can Mom ta kirata tace “idan kin kwantar da hankalinki akwai labari me dadin dadi da nakeson baki”

Muryarta harta dashe tace “kun boyemin abinda na cancanci nasani Mom meyesa” murmushi tayi tace “saboda kada muyi mahaukata biyu a dangi shiyasa Meenah kifa nutsu motsi kadan zakiyi ki fada rami mijinki yafi kowa buqatarki to kibi sannu kada santsi ya debeki”haka Mom ta rinqa bata kalamai wai ita a dole saita kwantar mata da hankali batasan qara tashin hankalinta takeyi ba suna kashe wayar Dr Khazeem yazo ta dubeshi yace “ya naki jikin batason hayaniya hakan yasa tace “naji sauqi so ganin yanayinta yasashi ficewa ta koma ta kwanta kamar bazata koma asibitin ba saidai taji zucciyarta taqi natsuwa dole ta shirya ta nufi asibitin ga mamakinta saita isheshi a zaune shida Mai Martaba ta dubesu suka gaisa da Mai Martaba yace “kema kina buqatar hutu ya kamata ki koma gda ki haihu acan” jinjina kai Kareem yayi yace “dama inada burin hakan sai na kwanta jinyar nan” da wannan sukaci gaba da tattaunawarsu hankalin Kareem na kanta Mai Martaba yace “ki koma masaukinku ki huta zan kwana dashi muga abinda hali zaiyi”…….

Yau fah saidai hqr da qarancin page din

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan
[8/12, 8:08 PM] Oum Hairan: Duban juna Juhud da Kareem sukayi yayi mata qaramin murmushi ya shafa sajensa tare da nuna mata hanya yace kije ki huta heart kinyi qoqari fah na gde Allah yabada lada” sunkuyar da kanta tayi tare da daukar wayarta tayi musu Saida safe ta fice ta nufi masaukin nasu zuciyarta na kaikawo tsakanin qirjinta da duniyar Rasheed, tana zuwa wanka kawai tayi tayi sallah ta kwanta itakam wannan dare barawon ma kasa satarta yayi gabadaya ta rasa nutsuwarta batajin daidai saina tunanin Rasheed, da asuba tayi sallah ta zauna tanayima iyayenta da Rasheed addu’a tare da fatan sauqi da sassauci cikin wannan jarabawa da suka tsinci kansu a ciki ciwon tabuwar qwaqwalwa a Rasheed abin Babu kyau.
Data tashi da ciwon mara ta tashi hakan yasa bata koma asibitin da wuri ba Saida Tasha magani ta dan samu relief sannan ta fita ta nufi hospital din a qofar dakin da Kareem yake ta ishe Rasheed Yana tsaye yana danna waya kamar ance ya dago suka hada ido ya lumshe idanunsa qirjinsa Yana bugawa itama haka ta matsa gabansa tace “barka da sfy Baffa’am” ja tayi da baya lkcn daya kece da dariya yace “shegiya ashe kinsan sunana ai Meenah ce take kirana da wannan sunan” lumshe idonta tayi hawaye ya ciko ijiyarta ta bude akansa ta girgiza kai tare da cewa “ka manta kowa da komai ka manta kamannin Meenah a zahiri Amma baka manta sunanta ba Baffa’am ya akayi hakan?”

Yarfa hannu yayi yace “nima to nasani kawai dai kema kinsan idan na kama Wanda ya kashemin Meenah a gabana saina dirmeshi da alburushi ke barima kiji fah koda yake na daina kulaki Meenah kishine gareta batason a hadata da wata a mafarki Ina ganinta kullum Kuma fah tana dan kama dake kadan Amma bakikai kyaunta ba” Mai Martaba ne yajiyo mgnr ta Rasheed tayi yawa ya leqo yaga ashe shida Meenah ne tasashi a gaba sai hawaye takeyi ya qwala mata Kira tayi saurin goge hawayen tace “ok ganinan” ta juya zata tafi ya riqota yace “shifa Wannan mutumin dan raini ne ya rainani yama zaayi Ina mgn da mutum ka kirashi to kaima ka kiyayeni kafin na qundumeka” zaro ido sukayi dukkansu ya dora hannunsa a bakinsa yace “lalalah ashe fah sabo nakeyi kayyy ke haihuwa zakiyi me zaki Haifa?”
Ganin batada niyyar tahowa ne Mai Martaba ya fito yaja hannunta yace “idan kika biyewa wannan saiku raba Rana da dare yanayi miki soki burutsunsa” sosai sautin kukanta yake fita batare da tasan kalmar ta subuce ba tace “ta Ina zan fara taimakonsa?”
Dubanta Kareem yayi ya kawar dakai yanajin wani abu nayi masa yawo a qirji da sauri ta share zancen da cewa “Mai Martaba ya jikin nasa?” A gajarce yace da sauqi sosai dama lkcn hutunsa yayi zamu tafi gabadaya daku saboda dukkanku kuna buqatar kulawa” jinjina kai tayi tabbas tana buqatar kulawa sosai Kuma taji dadin hakan domin itace damarta ta fuzgo yancinta zuciyarta na raya mata dolene Kuma wajibi akanta ta qwaci kanta domin Baffa’am dinta.

Kwanaki biyu suka qara a asibitin aka sallamesu cikin kwanakin ta fahimci abubuwa da yawa game da Baffa’am dinta hakanan wani lkcn sai yayi shiru yaqi yima kowa mgn ya rinqa kallon kowa daidai idan Mai Martaba ya cika damunsa saiya tashi kawai yakoma jikin tagar dakin yana hango waje yana cewa “kawai don anga Aminatuh batada gata sai a takurawa mijinta nifa idan kunsan takurawa na Meenah nazakuyi to kubarni ko da qafa zan koma Tanzania harda Sudan naje naci gaba da gadin kabarin Meenah ta”
Zantukan nasa a sukurkutacce suke ba kowa ke fahimtarsa ba Amma ita tana gane wani abu cikin maganganunsa ta fahimci kamar akwai hoton abinda yake masa yawo a kwanya da yake bashi gizon mutuwarta tunda dukkan wata kalma tasa mutuwa yake cewa Meenansa tayi to ya akayi haka?” Abin da yafi komai bata al’ajabi ita daya yafi yiwa wannan soki burutsun zantukan nasa marasa kan gado inda ta fahimci Kareem ko kadan bayason yaga Rasheed ya fiye mata mgn shi kansa Mai martaba yana nuna alamun hakan wannan take sanyata cikin jimami domin da tazo asibitin kafin sallamarsu zai tareta da cewa yawwa qawata zo na baki lbrn Meenah a duk sanda ya fadi haka sai takanga fuskar Kareem tayi duhu inda ita Kuma takan shiga tunani da zullumin wannan lamari.
Kwana uku suka qara komansu ya kammala suka dauki hanyar 9ja ko a cikin jirgin da Rasheed ya fara mata mgn sai Mai Martaba ya katseshi da cewa kai wai meye yake damunka ne Rasheed shikuma gashi ko yayi shiru baa minti biyar zai sake zungurota yace mata “yawwa qawata akai kaza akai kaza” haka Mai martaba zai sake mata tsawa itadai ta kasa jurewa ganinta wannan ai takura dan adam ne Kuma ma meye don ya zabeta matsayin abokiyar hirarsa aikuwa tayi kicin kicin da fuska ta juya gabadaya gareshi ta kamo hannunsa tace “labarin me kakeso ka bani Baffa’am?” Dago kansa yayi da yasa cikin cinyarsa ya dubi Mai Martaba da Kareem yace “ai dama batun yanzu ba na fahimci wadannan Gayun basasona da qawance dake Kuma na daina kulasu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button