JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Wani mugun kallo da takeyi masa yasashi cewa “kinga nifa ba dole zanyi miki ba Amma dai yakamata kisan yancinki a matsayinki na macen da kowa zaiyi burin mallaka…..” Tsaki taja ta nufi wajen park din tana fita ta samu napep ta hau ta fada masa inda zai kaita yaja suka tafi sun rigata zuwa gdan suna kallo harda Rasheed ta shigo da sallamarta su Mom ne kawai da Mai Martaba suka Amsa mata shikam Rasheed wani kallo yakeyi mata na tuhuma inda Kareem yakeyi mata kallon tausayi Muntaz kuwa da shine ya shirya komai miqewa yayi zaibar gurin ya iso gabanta yayi mata murmushi ya fice daga falon Ya’isha da Amrah ma miqewa sukayi Amrah ta riqe hannunta suka juya zasu tafi Rasheed da taka musu wata uwar tsawa da saida fitsari ya kusa qwacewa Juhud ya taso a haukace ya zare belt dinsa batare dasun lura ba ya rufesu da duka bai damu da kowa bama kamar Juhud tafi kowa dakuwa tana ihu tana tambayar meye tayi masa Yana cewa tayi masa shiru Kareem ne ya miqe a guje ganin Yana neman illatata ya angajeshi ya dagata ya nunashi da yatsa yace “kar Kuma ka qara dukanta wlh rama mata zanyi wannan ai zalumci ne duk abinma da Aminah zatayi su waye suka koya mata bagasu ba zaka wani zage qwanjinka akanta ita kadai saboda taqamar kanada iko da ita halittarta kayi?”

Tana kuka ta qwace a hannun Kareem ta rarrafa ta riqe qafafun Rasheed tace “indai dukan nawa zaisa zuciyarka tayi sanyi Baffa’am ka kasheni don Allah……” Daqyar takai qarshen zancen numfashinta ya kama rirriqewa gabadaya falon sukayo kanta kafin su iso gareta ma tuni ta suma, Kareem ya sunkuceta a guje sukayi waje asibitin dake cikin gdan ya nufa da ita suka karbeta suka shigar da ita wani daki gabadaya jikinta ya farfashe da dukan da yayi mata ruwa suka fara daura mata da Allurai.
Mai Martaba ya iso ya tarar da Kareem zaune ya rafsa uban tagumi ya Kira sunansa ya dago idanunsa sun kada sunyi ja Mai Martaba yace “ya jikin nata?” Bai bashi Amsa ba yace “waini meye laifina don nace inason Aminatuh ko Kuma ita meye laifinta da wannan azzalumin zai nemi illatata shiga fah kaga yanda ya farfasa mata jiki Mai Martaba shikenan Kuma don ya kasance uba a gareta saiya takura rayuwarta ya hanata rayuwa da farin ciki ko kuwa laifinta ne qin dawowa da wurin daga mkrnta ita Ina ta sani a garin nan balle ace ita tajasu yawo”……..

Jinjina kai Mai Martaba yayi yace “babu komai qarami Yayanku Ni yakejin haushi saboda nace sai yayi aure Kuma na kawo masa Zulaihat nace ita zai aura bazai iya dukana ba shiyasa yake hucce haushinsa akan Aminah zaici qaniyarsa su gama karatun badai cikin satin nan zasu fara jarabawar ba dukkansu inada yanda zanyi dasu kaikuma kaje ka fara shirye²nka na tafiya Saudi na gama maka komai”
Gumi ne ya keto masa ya dago duk jarumtarsa Saida hawaye ya ciko idanunsa yace “Auren fah Mai Martaba?” Murmushi Mai Martaba yayi yace qarami kenan kaje kayi karatun rabon mutum baya taba wucceshi indai Nike da ikon badawa nabaka Aminatuh Amma suma karatu zan turasu Kano sai sun gama zanyi musu aure kasan wannan tsarin na gdannan ba baqonka bane don ko yayyanku Fadila da Hamida Saida suka gama degree dinsu sannan na auraddasu”
Shigewa yayi ciki yaga yanayin jikin nata ya fito ya nufi motarsa ya shiga ya fice daga gdan. Juhud bata farka ba sai dare sosai Addah Abulle ke jinyarta tayi mata sannu ta daga kai cikin yanayi na jin jiki tace “Addah Ina Baffa’am dina?” Ba Addah ba Ya’isha ma saida ta kalleta taja tsaki tace “uwar me zaiyi miki banza dake kema?”
Sunkuyar dakai tayi tace “hqr zan bashi” tsaki Ya’isha da Amrah sukayi Addah tace “bai jima da barin nan ba” bata Kuma cewa komai ba Addah ta taimaka mata ta miqe ta shiga bathroom tayi brush ta fito dake ba sallah takeyi ba suka bata abinci taci ta kishingida Amrah ce ta matso tace “wato Ya Muntaz ba qaramin dan sharri bane muna dawowa Big Cele yace kina Ina shine ya karkace yace ai dayaje makarantar ma bai samemu acan ba muna Dikko Park da samarinmu muna bikin ranar masoya mu da yayi Mana mgn muka biyosa muka taho kekam cewa kikayi saurayinki zai kawoki qiri² ya kitsa Mana sharri zamuyi mgn Big Cele yace duk wacce tayi masa mgn saiya dagargaza kanta”………….

Oum Hairan
[7/19, 9:05 PM] Oum Hairan: JH013 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki

Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566
Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde

Hadiye wani abu tayi me daci a fili tace “Allah yanaji yana gani” daga haka bata Kuma cewa komai ba ta miqe taje ta kwanta ba bacci takeyi ba tunanin sauyin yanayin Baffa’am din nata ne kawai yake addabarta itakam zataje ta sameshi ya fada mata laifinta don ta kiyaye yimasa irinsa a gaba.
Da wannan tunanin bacci ya dauketa da safe kafin kowa yazo Kareem yazo tanajinsa tayi likimo kamar me bacci ya qaraci mgnrsa ya fita bayan fitarsa kadan Rasheed din ya shigo daga sallama miskilin baice da kowa komai ba ya gama kalle kallenshi ya juya ya fice Ya’isha ta tabe baki tace “miskili kafi mahaukaci ban haushi” dagowa Amrah tayi tace “wato daga jiya zuwa yau gabadaya Big Cele baya cikin nutsuwa na fahimci ba iyakar Juhud yakejin haushi ba kowa ma fushi yakeyi dashi Kuma kinsan dalili?” Girgiza kai Ya’isha tayi tace “akan mgnr auren da Mai Martaba ya matsa masa yayi ne Kuma yace ya zaba masa Zulaihat kinsan tun da can ma Big Cele ya tsani yarinyar nan kamar masifa Ni bansan azal din data haushi ba da Zabin Mai Martaba ya qare akanta”
Tunda suka fara mgnr qirjin Juhud yake dukan tara² aure Baffa’am dinta zaiyi?” Maimakon taji tana farin ciki sai taji ta cika da tausayin kanta a hankali tasa hannu ta share hawayen daya gangaro mata ta yunqura ta tashi zaune cikin dakiya da nuna jarumta tace “a tunanina uba kamar Mai Martaba bazai taba yima dansa Zabin dabai dace dashi ba banga aibin Aunty Zulaihat ba da kuketa mgn akanta ni sainaga ma ta dace da mijin nata zasu dauki kala sosai Ina ganin muyi musu fatan Alkhairi yafi tsayawa wannan surutun da kukeyi Kuma ma Ni banji araina don wannan Baffa’am yake fushinsa ba kawai dai nice na bata masa”

Qwafa Amrah tayi ta fahimci duk yanda zakaso daka ganar da Juhud bata ganewa garama ks qyaleta a cikin duhun da take, Addah ce ta shigo musu da abin karyawa suka karya aka sallamesu suka tafi gda ranar bataje makaranta ba yini tayi a kwance da tsamin jiki bata da aiki sai murdo ruwan zahi a hitter ta gasa jikinta da yayi rudu² abinka da jar fata, abinda yake bata mamaki tun ranar da Rasheed yayi mata duksn mutuwar baya yarda su zauna guri daya da yaga ta fito yake tashi yabar gurin itakuma tsoro ya hanata ta tunkareshi ta fahimci neman abokin mutuwa yake shiko Kareem kullum qara fito mata da salon qaunarsa gareta yake baya boye soyayyarsa a gaban kowa sai gaban Rasheed shima don ya fahimci baya happy da lamarin ne.
Sun shiga jarabawa gadan² kawunansu sun dauki chargi matuqa musamman Juhud data Hana kanta sakewa da farko sunci gaba da zama suna lesson da Kareem tunda ta fahimci duk lkcn da suka zauna Baffa’am din nata zaita zagaye a gurin Yana qwafa yasa dole ta hqr ta janye ta koma yiwa kanta lesson da kanta tanashan wahala Amma saboda baqin nacinta taqi ta hqr hakanan take tursasa kanta, ganin hakan yasa Mai Martaba ya siyo mata tamfatsetsiyar waya Infinix hot 10 yabata tare dayo mata download na manhajoji na bincike da zasu taimakawa brain dinta taji dadi sosai ranar yini tayi da farin ciki a ranta tanajin itama ta faso gari su Ya’isha sa daina daga mata kai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button