JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Miqewa yayi ya dauki Mahfuz daya farka a bacci yake neman uwarsa ya fita ya nufi dakinta ya bude ya shiga ga mamakinsa ya isketa zaune can qarshen gadon ta zuba uban tagumi ya zubanta ido tausayinta da qaunarsa na qara nunkuwa a zuciyarsa ya haura gadon ya kwantar da Mahfuz ya sanya hannunsa ya janye mata tagumin ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sunsunar sumarta yanajin wata natsuwa na kwararo masa yace “idan na rasa gatan kowa a duniya baikamata na rasa naki ba Meenah bai kamata na zamo mara galihun nunawa duniya a gurinki ba bayan kin kasance mace daya tal dake mulkin zuciyata please na roqeki ki daina jin a ranki akwai abinda zai rabamu qaddarar mutum Babu me tayashi dakonta ni kece qaddarata nima nine qaddararki bazan hanaki kuka ba akan abubuwan da suke faruwa Amma dai ki rinqaji a ranki iyakar rintsin rayuwar duniya ni nakine ke kadai Babu wani tsanani da zaisa na rabu dake saidai qaddarar mutuwa idan ta gifta saboda haka banson sakejin wadannan kalaman naki don Allah kinji?” Zamewa tayi a jikinsa ta miqa hannu ta dauki Mahfuz tayi Bismillah ta Sanya masa nonon ya kama yanasha shikuma yana aikin kallonsu.

Kwanciya tayi badon tayi bacci ba saidon tabawa zuciyarta hutu shima kwanciya yayi a bayanta ya maqaleta da haka sukayi bacci washegari da wuri ya fice daga gdan duk cika ta gidan sarautar idan ka shiga barayin Rasheed bazaka taba cewa sabuwar haihuwa akayi ba saboda yanda gdan yake a yashe daga ita sai Kumbo Hami suketa harkokinsu Rasheed bai dawo ba sai bayan Isha lkcn har sun kwanta ya shigo ya kirata ta miqe ta nufi dakin nasa yana safa da marwa ta samu guri ta zauna shima ya zauna a gabanta ya dubeta sosai yace “nasa anzo an kama Hajiya Bilki da Dada Hanne…..” Dafe qirji tayi da sauri tace “na shiga uku Baffa’am me sukayi maka?” Share zufa yayi ya miqe yace “saboda a koya musu hankali su fita daga harkata da iyalina” yana mgnr yana hada kayansa ta miqe ta Isa gabansa jikinta na rawa ta durqushe tace “wlh wannan abin baikai ka dauki wannan matakin ba Abban Sarki ana barin halal ko don kunya please kada kayimin haka wani bala’in zaka qara jefani a ciki kasa a sakosu wlh ni na yafe musu….”
Rufe mata baki yayi yace “ke zaki iya yafewa saboda bakisan ciwon kanki ba nikam ban yafe ba Yana fadin haka ya shige bathroom yabarta sake da baki wannan mutumin kwai dan neman jarfa anason kashe wata yana neman zunguro sama da kara

Tananan zaune ya fito daga wankan Yana tsane ruwa ta sake dubansa zatayi mgn ya nuna mata hanya yace “jeki ma hadu da safe inason zanyi yan nazarce nazarce” miqewa tayi jikinta a mace ta koma dakinta ta ishe Kumbo Hami tana sallar Isha ta zauna bayan ta idar ne take tambayarta meye yake faruwa ta kuwa zayyane mata komai tayi shiru na dan lkc sanna ta dago tace “banji dadin kaisu qara da yayi ba shima hakan qarin wata fitinar ce daya qyalesu watarana sai lbr”
Miqewa tayi ta Sanya Sarki junior a gadonsa tana cewa “nima abinda naso ya fahimta kenan yaqi bani hadin kai koroni ma yayi Kuma tunda yayi niyya Babu me hanashi” da wannan tayi addu’a ta kwanta sukayi baccinsu itadai da zullimi ta kwana aikam abinda take gudun ne ya faru da safe Yana fita Hidaya da Khadija sukayiwa gdan tsinke suka rinqa zaginta sunacin mutumcinta Meenah babu baki sai hawaye kawai da takeyi suna tsaka da wannan tujarar ne Kareem yazo musu barka don shi sai ranar ma yakejin lbrn haihuwar gurin Fadila aikuwa ranar Khadija da Hidaya sunji a jikinsu domin dukan mutuwa yayi musu kamar shine sojan daqyar Mai Martaba ya qwacesu barkar da baiyi ba kenan ya fice daga gdan rashin mutuncin gdan ya fara girmewa tunaninsa ace Babu Wanda ya isa ya fada aji anbi an tsangwami yarinya akan abinda bashida tushe balle makama aikam ranar hatta Addah Abulle Saida taji kunyar irin rashin albarkar da Kareem yazo ya zazzage mata a gdan akan rashin zuwa taga Dan da aka haifawa Rasheed yan uwansa kuwa gda gda ya rinqa binsu yana ci musu mutumci Yana fada musu ai ba Meenah suke qi ba Rasheed suke qi tunda shine ya dauko Meenah Kuma yakeson kayarsa sannan ba Meenah kadai ta haifi Mahfuz ba Rasheed shine silar zuwansa duniya saboda haka shine basaso”

Basu wani dauki mgnr da muhimmaci ba ba Kuma su risuna ba sukaci gaba da dabdalarsu rikici yaqi qarewa cikin wannan family har ranar suna akayi sunan babu wani armashi kamar abin arziqi dangi suka hadu ranar Meenah Saida ta gwammace ita dama mutuwa tayi da wannan baqin cikin data riska wannan Rana a qarshe baa gama sunan da ita lfy ba sai a gadon asibiti ta qarashe sunan jininta yayi mugun hawa hawan da Rasheed bai taba tsammani ba ya shiga tashin hankali matuqa da yanayin da yaga matar tasa a ciki, da dare aka sallamesu suka dawo gda kanta na ciwo sosai da Rasheed da Mom da Kumbo Hami sunata rarrashinta da kalami na kwantar da hankali bacci ya dauketa washegari badon yaso ba ya shirya yabar garin ya koma wajen aiki yabarsu cike da kewar juna…………….

Kuyi hqr da wannan

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan
[8/4, 8:56 PM] Oum Hairan: 0028 Kwananta sittin da haihuwa Kumbo Hami ta koma Mali inda ita Kuma taci gaba da rainon danta cikin kulawa da tattali a hankali lkc yaketa tafiya qaunarta da Rasheed tanata qara gaba inda aiki ya riqeshi kusan watanni biyar sannan ya waiwayosu ranar anyi qara’in rayuwa kamar bazaakai gobe ba yayi musu sati biyu ya shirya domin tafiya wani aikin hadin gwiwar qasa da qasa zuwa Togo yaso tafiya da ita Mom tace gara yaje yaga yanayin gurin tukunna inyaso sai yazo ko ya aiko tabisa.
Hakanan suka rabu bason ransu ba wani abin almara tunda ya tafi wayarsa bata shiga da farko sun dauka yanayin aiki ne tafi tafi da tafiyarsa ya dauki wata biyu babu waya babu aike, sosai hankalin Juhud yaqi kwanciya hakanan wata faduwar gaba ta aureta Mom ma tana cikin damuwar rashin jin labarin dannata hakanan take daurewa tana kwantarwa da Meenah hankali, tafiya na qara tsayi har aka tafi wata shidda Babu waya Babu amo Babu labari. Qa’idar aikin nasu yace watanni shiddan ne gashi sun wucce nan fa Mai Martaba ya tashi takanas yaje barikinsu inda ya dawo cikin matsanancin tashin hankali suna ganinshi Meenah dake zaune ta dora kanta saman cinyar Mom tana aikin kuka ta miqe tana cewa “Mai Martaba kaganoshi Yana cikin qoshin lfy?”

Sunkuyar dakai Mai Martaba yayi yana kwance rawaninsa yace “lamarin akwai daure kai fah naje barikinsu duk sojojin da aka tura Togo sun dawo tsiraru ne suka mutu Amma shi bai dawo ba dana matsa da bincike ma a data na aikinsa tun sunada wata biyu da tafiya wani mugun ciwon kai ya sarqeshi shine dalilin da yasa aka bashi hutu da zummar zai dawo gda tsayin watannin nan bai dawo ba…..” Yanke jiki Meenah tayi ta fadi qasa sumammiya gabadaya sukayi kanta Mom ta dauko ruwa ta fara yayyafa mata daqyar ta dawo hayyacinta ta miqe zaune ta dubi Mai Martaba cikin gushewar hayyaci tace.
“Me kakeso kacemin Mai Martaba mijina ya taho gda daga filin daga Kuma baizo gidaba to Ina ya tsaya Kuma wayoyinsa basa shiga tun satin daya tafi?” Gumi Mai Martaba ya sharce yace “shine abinda nima nake tambaya kada ki tashi hankalinki na sanar da duk Wanda ya kamata na sanarwa wannan isue din Kuma sun fara bincike daga yau insha Allahu komai zaizo da sauqi….” Cikin kuka tace “ta yaya zan kwantar da hankalina bayan rayuwata tana cikin garari nikam don Allah ku fitomin da mijina wlh inason kayana” daqyar suka samu suka lallasheta shima ba shiru tayi da kukan ba kawai surutan ta daina hakanan aka duqufa babu ji Babu gani nemansa ta kafofin sadarwa na Internet da duk wasu hanyoyi da zaa samu bayaninsa Amma shiru Babu amo Babu labarinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button