JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Murmushi tayi tace “to Kuma meye na kukan aini Inasonka da qawancen….” Ihu yayi yace “don Allah da gaske?” Daga masa kai tayi yace “wayyoh dadi zan baki alawar madarar dana siyawa Meenah zankai mata lahira idan munje gda” murmushi tayi me hade da hawaye tace “Baffa’am ai wanda ya mutu baici baisha baya mgn fah” hannunsa yayi a baki yace “dallah ware sunguma malohuwa ita Meenah an fada miki irin mutuwar kowa tayi ne ai ita kullum tare muke kwana da asuba saita bace bana qara ganinta sai wani daren Kuma in fada miki kullum cemin takeyi Inasonka Baffa’am dina bazan taba rayuwar farin ciki ba tare dakai ba kaji a ranka ko bana duniyarka to Ina fadar zuciyarka daka bani nini kadai…..”ba itaba dukkansu Saida suka kalleshi sak muryar Juhud yayi amfani da ita wajen furucin tayi dariya sosai tace “Kana bani nishadi…..”
Wata tsawa Kareem ya daka mata yace “yaci gaba da baki nishadi zan datse duk wata alaqa dake tsakaninku kuwa muga qaryar baki nishadi” dama a qufule take dashi da Mai Martaba ta kuwa hayayyaqo masa tace “zaka iya Kuma? Kanajin kanada qumaji da qwarin gwiwar raba hanta da jini ne? To karka soma shidin bangare ne na rayuwata da bashida tamka wlh a duniyata yafi iyayena domin na rasasu tun bansan dadinsu ba shine ya mayemin gurbinsu ya zamemin uwa uba Yaya qani aboki qawa sannan ya……..” Dauketa da mari taji anyi ta dafe gurin da sauri kafin ta kanta ya gama juyawa taji qarar wani Marin ta bude idanunta da sauri taga Kareem dafe da kunci Mai Martaba a tsakiyarsu Rasheed sai huci yakeyi yana hanqoro so yake ya samu dama ya damqi Kareem Mai Martaba ya hanashi yace “kasheka zanyi in kashe banza wlh don akan qawata Babu ruwana dakai qanina ne inma yayana ne saina aikaka inda na aika Wanda ya kashemin Meenah”

Zama Kareem yayi Yana huci Yana cije lebe shima Rasheed ya zauna yace “saqagon banza dashi dabai iya komai ba sai cin zali” shidai bai kulashi ba don ya fahimci idan yaci gaba da kulashi mahaukata biyu zaayi Amma yaci alwashin ta qarfin tsiya saiya raba Meenah dashi suna sauka a Kano Lado driver yazo ya daukesu suka nufi Katsina Mai Martaba motarsa daban shida Rasheed shikuma shida Meenah ko a tafiyar babu me cewa wani qala har suka isa Katsinan a yanda Mai Martaba ya tsara dole haka sukabi gdan sarautar suka nufa anan yace su zauna harta haihu.
Yana qunci da cin magani suka shiga cikin gdan kai tsaye ya figi hannunta suka shige part din nasa ya kulle qofar ya saki hannunta Yana huci ta juya ta nufi kujera ta zauna ko kallonsa batayi ba ya gama kumburinsa ya nufi dakin baccinsa ta tabe baki a ranta tace “ka kuwa hadu da aiki” batabi ta kansa ba itama ta shige dayan bangaren tayi wanka ta bude Jakarta ta dauki doguwar riga ta sanya tasa mayafinta ta sulale tabar part din ta nufi cikin gdan ta matsu taga Mom tana shiga falon Mom ta taso da gudu ta tareta da cewa “oyoyo oyoyo Aminah ta” dariya tayi suka zube a kujera tace “ashe kema kinyi kewata Mom Ina Sarki” juyawa tayi inda suke zaune shida babansa tace “au shine bazaka kulani ba” dariya yayi ya taso ya fado jikinta yace “kin tafi kin barni inata kewanki Dad dina ya dawo inaso kizo ki ganshi kullum na saci wayan Mom na kiraki sai najita a kashe”

Murmushi tayi me hade da hawaye tace “Allah Sarki My Son kana Raina ya kakeji game da dawowar Dad dinka?” Kwantar dakai yayi jikinta yace “happy Mom kinsan me Dad dina fah bashida lfy baya gane kowa harni” share masa hawayensa tayi tace “ka daina damuwa zai ganeka zansa ya ganeka kaji” daganta kai yayi Rasheed dake zaune yace “kuma itace qawata da nake baki lbr Mom Kinga ashema tasanku tasan wannan yaron da yaketa cemin Dad” tare suka share hawaye da Mom Mom tace “hakanma mun gode Allah Meenah wai a hakan fah an samu sauqi farkon lkcn da aka tsintoshi abin baa cewa komai sai gdyr Allah Amma yanzu yaji dama”
Jinjina kai tayi ya taso ya dawo kusa da ita tayi saurin sanya Sarki a tsakiyarsu yace “dariya ma kike bani” dukkansu sukayi dariya Daidai lkcn da Addah Abulle ta fito daga sashin Mai Martaba idanunta akan Meenah sukayi kallon kallo taja baya da sauri tace “na shiga uku ni Zainabu wato shegen yaron nan da yace sun zubar da cikinga ashe qarya yakeyi” murmushi Meenah tayi zuwa yanzu zuciyarta ta fara tsikewa tace “sannu fah Addah ya gda mun sameku lfy?” Wata uwar qwafa tayi ta nufi dakinta fuuuuu Meenah ta tabe baki ta mayar da hankalinta ga Mom sukaci gaba da hirarsu tanata dariya abinta shirmen da Rasheed yake buga musu ko Sarki bazaiyi ba suna haka Fadila ta fito ta debesu ta watsar Meenah tayi murmushi tace “Allah Sarki wannan fah Mom?” Girgiza kai tayi tace “au Fadila auren ne yaqi dadi mijin neman mata har ksn gadonsu na sunnah shine tayo yaji ya aiko mata da takarda saki daya” dafe qirji tayi tace “ya salam Abin tausayi Allah ya daidaitasu” murmushi Mom tayi tace “kayyah dai itama Amrah jiya ta koma aure mijin ya qara shine zatayi masa haukanta ya korota uwar mijin tace ita dama batason wannan auren daidai ya nace ne daqyar dai aka sasanta ta koma kayy Meenah munga jarabawa dan ritsin nan ” jinjina kai tayi tace Allah yasa ta zamo kaffara amsawa tayi da Amin sunata hirarsu ta yaushe gamo Kareem ya shigo suka gaisa da Mom ya dubi Juhud yace “bansan kin fito ba fah Saida na leqa dakinki naga bakinan” murmushi tayi tace “nazo mu gaisa dasu Mom ne”

Miqewa yayi ya nufi part din uwarsa yace “ok ku gaisa sosai Amma ki nemamin abinci yau girkinki nakeson ci…..” Rasheed dake tura motar wasan yara shida Sarki ya dago yace “lahhh zaka sammin?” Tsayawa Kareem yayi ya juyo ya dubeshi da tausayawa yace “in kanaso ma kullum ka rinqa zuwa kana karba Aminah ta iya girki sosai” tsalle yayi ya dafesa yace “itama sunanta Meenah nima tawa Meenan ta iya girki nifa tunda Meenah ta mutu ban qara cin abinci me dadin nata ba”
Tsayawa yayi kamar zai juyo sai Kuma yasakai ya shige ciki sama² suka rinqa jiyo hargowar Addah Abulle basajin dai abinda suke cewa Meenah ta miqe tace “bari na koma Mom duhun magrib ya fara shiga saida safe” ta juya ga Rasheed daya zuba mata ido tace “Baffa’am Saida safe” daga mata hannu yayi yace “zanzo na karbi abincin naki ai” murmushi tayi ta juya ta fice ta nufi sashinta taji an bangajeta taja baya da sauri tare da cewa A’uzubillahi…..” Tana duban Wanda ya bangajeta din Fadila ce qanwar mijinta tayi murmushi kawai ta juya taci gaba da tafiyarta a bayanta taji tana cewa “gayyar na ayyah gayyar tsiya an dawo zaaci gaba da dorawa uwarmu ciwon zuciya jarababbiya qalatacciya da wani shegen cikinki a gaba irin masifa irin maita……”
Kalamin sun daketa ta cije lebe tare da tsayawa batare data juyo ba tace “hakane saidai kin manta abu daya bani na liqe mawa dan’uwanku ma shine qalatacce jarababben daya liqemin wlh da zaku bashi shawarar ya rabu dani ma ya dauka da dadi nikaji domin zan yar da qwallon mangwaro na huta da qudaje”

Tana fadin haka ta shige tabar Fadila sake da baki lallai yarinyar ta riqa wato sune qudaje Kareem ne mangwaro tab yau da tashin hankali a gdannan, fuuuu ta shige ciki ta nufi sashin uwar tasu tana shiga ta fara karanta mata qarya da gaskiya aikuwa ta hau ta zauna ta dauki waya ta Kira Dada Hanne ta zayyane mata abinda ke faruwa Dada Hanne tace “ai Ni wannan jaraba na rasa dame tayi kama yarinya ta zamewa mutane qarfen qafa an kasa kwanceta a yar shima Mahfuz din kwanaki kamar abin arziqi aikin da mukayi ya fara cinsa yanzu Kuma yaqi kullum abubuwa lalacewa sukeyi”
Takaici ya cika zuciyar Addah Abulle tace “ni takaicina ma cikin nan da yake jikinta ashe bai fadaman lissafin daidai ba boyemin yayi yanzu kawai Ina ganinta naganta da tsohon ciki haihuwa kusa” wata uwar ashar Dada Hanne ta qunduma tace “au ke yanzu kina zaune sakarai kika bari tayi ciki kema zaa jorner miki tsiyar?” Da muryar takaici tace “to ya zanyi kefa kika sani na rinqa rabar da kudi tsakanin gurin malamanki dana Hajiya Bilki nidai banga wata nasara ba saita dawowa ta gdannan”
Qwafa Dada Hanne tayi tace “ai shegiyar gantalalliyar yarinyar ce masifar taurin kaine da ita bansan wanne irin shiri ne a jikinta ba Amma bari intasan wata batasan wata ba” sun jima suna saqarsu a mugun zare sannan sukayi sallama da shirinsu na cimma matsaya.
Meenah kam tana shiga part dinta idanunta ya sauka qasan tiles din taga wani garin magani duk an barbadar dashi kiyayewar Allah ce kawai tasa taga maganin saboda shima arsh ne kalar tiles din, taja baya da sauri tana a’uziyya a fili ta fara dube dube bataga Wanda zata Kira ba ta koma gefe ta tsaya tsam jikinta na tsuma tsoro ya cikata tana nan tsaye Allah ya jefo mata Kareem taja ajiyar zuciya, qarasowa yayi da sauri yace “meye kikeyi anan Kuma?” Dubansa tayi jikinta na tsuma tace “naje zan shiga naga wannan abun” idanunsa ya zuba a tiles din ya na kallon abin ya girgiza kai yace “ki shigo da Bismillah babu abinda zai sameki sai abinda Allah ya hukunta kiji haka aranki”……….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button