JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Ji yayi zuciyarsa ta karye tabbas Dan’adam daraja ce dashi maybe idan ya taimaketa Allah ya qadarta tashinta idan kuma ya tafi yabarta wasu halittun na daji zasu iya zuwa su qarasa ta, da wannan tunanin ya tsugunna ya sanya hannunsa ya dagota cak ya sabata a kafadarsa ya miqe ya nufi Camp dinsu da ita, tafiya ce me tsayi sosai tsakanin gurin daya tsinci Juhud da camp dinsu haka yayita kurdawa cikin wannan duhuwa har ya fito sarari ya fara hango Camp din nasu kuratan sojojin da suke basu fita duty ba suna zazzaune cikin ruwan sunata hirarsu da iface²nsu.
Duk inda ya gifta kallonsa akeyi da fuskar mamaki idan ya wucce su kalli juna su gimtse saboda sanin tsagwaron rashin imaninsa yanzu ne zai sabawa mutum halitta ko yabaka gwale²n da sai kayi sati kana ruwan dumi, kai tsaye clinic din Camp din ya nufa ya wucce kowa ya shiga har dakin duba marasa lfyr ya kwantar da ita saman gado ya juya zai fita Likitan dake kan aiki yayi qundunbalar cewa “Tnks Sir” jinjina masa kai yayi yace “kayi aikinka akan wannan yarinyar banason a samu matsala ka bari ta mutu kaima saika mutu domin alamu sun nuna zamu samu wani haske game da yan ta’addan nan da suka damemu” sake sara masa yayi cikin ladabi ya sanya kai ya fice wani Soldier ya dafashi yace “A tsarin aikinmu babu dauko petiant mu kawoshi garemu domin magani Cornel Rasheed meye yasa kayi hakan shin baka tunanin matsala zata iya afkuwa?”

Fuskarnan kamar hadari yace “nayi ne don inada ra’ayin hakan kuma hakan nakeson yi saboda haka ayi hakan kawai” yana fadin haka ya juya ya sake nufar dajin domin yin abinda ya fitar dashi dazun, bashi ya dawo Camp din ba sai 11:30pm sabe da wata qatuwar gada a kafadarsa yana zuwa ya cillawa kuratan sojojin da ido yabasu umarni suka mike suka fara gyarata tantinsa ya nufa ya cire kayansa gabadaya ya fito dagashi sai gajeran wando ya nufi wani zagayayyen guri ya watso ruwa ya dawo ya shafa mai ya fesa turare yasa wasu kayan shan iska ya kwanta a dan gadonsa ya lumshe idonsa zuciyarsa na kai kawo tsakanin Joss Da Katsina Birnin Daura ya kwana hudu rabonsa da mahaifarsa yanason zuwa amma aiki ya riqeshi.

Taba qofar akayi alamun ana neman sahalewar shiga garesa yayi juyi tare da cewa “a shigo” shigowa likitan yayi ya qame a gabansa yace “Sir wannan Petiant din aikinta yafi qarfinmu saidai akaita Barreck ayi treat nata saboda ciwon nata babbane akwai abubuwan da bamu dasu anan da dole sai dasu zaayi amfani”
Baice masa komi ba ya dauki wayarsa ya kira wata number ba bata lkc aka daga yace “ya nemi izinin gaggawa na komawa barreck cikin yan mintuna aka basa ya miqe suka fita da likitan yana tafe yayiwa drivernsu mgn ya Zama ready ya shiga da kansa ya zare ledar jinin da suka sanya mata ya sabeta ya fita yasa a mota suka dauki hanyar cikin gari barrack dinsu nesa take da gari sosai hakan yasa basu isa ba sai daya saura suna zuwa kai tsaye asibitin ya kaita likitoci sukayi mata cah aka fara jorner mata na’urori saida aka gama saita komi sannan ya juya a gajiye ya nufi gdansa, budewa yayi ya shiga ya bude qofar Falon ya tsaya yana qarewa falon kallo yanajan qwafa.
Wato Christiana bata gyara masa gidan ba tunda ya tafi, iska ya furzar me zafi ya bude dakinsa ya shiga shima kaca² Tsaki yayi ya cire kayansa ya dauki towel ya daura sai yanzu asalin siffarsa ta bayyana dogone kakkaura kirar mazan faman gaske wankan tarwada shiba fari ba shi ba baqi ba, yana da fadin qirjin sosai me cikakkun nonuwa da suke rangaji kamar na mace gargasa ta kewayesu abin gwanin sha’awa gabadaya jikinsa lullube yake da suma fuskarsa me qarancin fara’a faffada me madaidaicin tsayi hancinsa dogone amma ba kamar biro ba lol.

Yayi daidai da dan qaramin bakinsa me dauke da siririyar wushirya a tsakiyar shiryayyun haqoransa sajensa baqi sidik daya hade da gajeran gemunsa sumarsa baqa kwantacciya ta fulanin asali ta qara armasa sirrin boyayyen kuma bayyanannen kyansa.
Cornel Rasheed Mahfuz kenan haifaffen garin Port-Harcourt da asalin Jahar Katsina cikin Daura L.g.a Wanda aikin soldiar yakai General Mahfuz wato mahaifinsa da mahaifiyarsa Salma Part-Harcourt ta haifesu su shidda acan, Captain Salman shine Babba Sai Dr Arman da yake bi masa sai Hamida Sannan Raseed sai Muntaz sannan auta Ya’isha,
Zainab matar babansu ce wacce suke kira Adda Abulle tana da yara hudu Kareem Shine Babba baikai Rasheed ba ya girmin Muntaz sai Fadila da Urwat sannan Auta Amrah, shekaru sunata turawa har zuwa lkcn ritayar Gen Mahfuz ritayar tasa tazo daidai da lkcn da Wansa da yake mulkar masarautar Daura ya rasu hakan tasa aka nadashi matsayin sarkin daura, dole ya dungumo ya dawo gida domin gudanar da mulkinsa.

Babbar matsala da take damun wannan Fam shine rashin qwaba asalin wata rayuwa akeyi da ake cewa uwa ba kwaba uba ba harara duk abinda da yaran sukaga dama shi sukeyi Qa’idar Gen Mahfuz ce ko hararar dansa mace tayi saita fuskanci fushinsa to itama Momy Salma kusan tafiyarsu daya Adda Abulle ce kawai me iya tsawatar to itan bata samu goyan baya daga gurin mai gidan da kuma abokiyar zamanta ba hakan yasa ta dauki mataki mafi rauni shine qin abun a zuciyarta.
Gen Mahfuz mutum ne na mutane me taimakon talakawansa babbar matsalarsa da kowa ya sani itace ta gidansa ya kasance kowa abinda yakeso yakeyi babu me cewa wani gyara domin kowa abinda zuciyarsa ta saqa masa yake aikatawa daga mazan har matan da kayi musu mgn zasuce maka Life is Freedom…….

THIS BOOK IS NOT FREE… REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566

Shares Please

Oum Hairan
[7/13, 9:13 PM] Oum Hairan: JUHUD

(OUM HAIRAN)

( Pure love sex nd romantic)

FREE PAGE FIVE 5

SANARWA
Wannan littafin na kudine idan kina buƙatar ci gaba da samunsa bayan gama free page kiyi ƙasa a ƙarshe an faɗi hanyoyin da zakubi don biya da karatu cikin Aminci.

SUBSCRIBE
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

TUNATARWA
Idan kayi hƙr a yau ɗinka, to zaka tsinci ribarsa a gobenka kada mu gajiya da juriya da hƙr da dukkan halin da muka tsinci kanmu a ciki komai na duniya me wuccewa ne kada tsanani yasa ka rinqa jin kamar ubangiji ya manta dakai ne aa Allah baya mantawa da bayinsa, yabarka ne domin auna nauyin imaninka.????????

CIGABA
A tsakaninsu ma suna ji da ganin abin matsayin wani abin alfahari adda Abulle tana bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta nusar dasu illar rayuwar da suka zaɓawa kansu musamman ma mazan amma ta kasa samun nasara har takai sunayi mata kallon wata barazana ga jin dadinsu wannan ta sanya dole ta zubansu ido take binsu da addu’a, duk cikin gidan nan ɗa ɗaya ne tsarkakke wato Kareem.
Shi ɗaya ne nasihar mahaifiyarsa take tasiri a kansa har ya tattara ɗabi’ar gdansu ya zuba a kwandon shara tasowarsa da kasancewarsa mutum da bayason raini yasa ƙannensa mata suka ɗan nutsu duk wata sheɗanarsu da iskancinsu basuyi idan yana kusa,
Hajiya Salma kullum mitar da takeyi wai ya hana mata yaranta mata sakewa idan tana wannan mitar yakanyi murmushi yace “Momy wannan takurar da kike cewa anyima Amrah da Ya’isha itane gatansu saboda haka bazan fasa ba duk yarinyar da naga xata sake layi zan hukuntata daidai da laifinta” da taji haka saita haɗashi da Raseed to shima bai bawa mgnr muhimmaci ba abu ɗaya ya sanar da ita ai shiɗin samansu yake yasan daidai yasan akasinta.
Daga momy yarsu Ya’isha babu wanda yaji daɗin abinda Rasheed yace dole suka ja bakinsu sukayi shiru don har gara kowa ma dashi domin shi idan aka ɓata masa horon gidan soja yakeyiwa mutum wannan tasa duk gidan babu wanda baya tsoronsa hatta da Muntaz da yafi kowa lalacewa yana boye laifinsa garesa duk da ba ko yaushe yake kulawa ba to idan ya tashi kulawar akansha wahala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button