JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Hakanan suka nufi unguwar da gidan nasa yake Mai gadi ya bude musu suka shiga sukayi parking Aunty Hamida ce take riqe da hannunta har cikin gdan suka haura da ita saman itama kamar dayan sashin dakuna biyu ne sai wani qarami da alamun local kitchen ne wanda koda zaka buqaci wani abu da dare basai ka sauka ba, daya cikin dakunan suka bude suka shigar da ita sosai Hajiya Kulsum aminiyar Mom ta qara yimata nasiha akan biyayya ga mijinta itadai Babu abinda da takeyi sai kuka da rawar sanyi zazzabi ne yake neman rufeta Ya’isha ta matso jikinta ta sunkuya tace “ke banza ce wlh Ni banga abin kuka ba to kukan mafita ya zame miki kome?” Dagowa tayi ta sauke idanunta sa suka jima da komawa jajaye saboda kuka tace “shi….shikenan da gaske na rasa Baffa’am dina Ya’isha Kuma akeso nayi rayuwar farin ciki…..” Muryarta ne ya kama rawa Ya’isha tace “mun shigai Aunty Hamida ku Kira mijinta zata tayar mana da aljanu” yanda jikinta ke tsuma ne yasa Hamida yarda ta Kira wayar Rasheed ya daga muryarsa can qasa shima rawar tasa muryar takeyi yace “ya aunty Hamida ya akayi?” Cikin zaquwa tace “Meenah ke neman rikice Mana mun kasa gane kanta don Allah kazo idan kana kusa” kashe wayar yayi dake dama Yana gdan duk motsinsu yanaji ya dauki doguwar riga ya saka ya bude qofar ya fito idanunsa kamar garwashi saboda ja dake duk yafisu Rasheed haske shi fari ne sosai daka kalleshi zaka gane kukan shima yakeyi.
Kuka Fadila ta saka da ganin yanda yayan nata ya zama wani kalar tausayi tace “tunda yarinyar nan ta shigo zuri’armu muka daina cikakken farin ciki Ya Kareem kaima duk ta susutaka yanzu kukannan don ita kakeyinsa…..”
Hanya ya saita mata cikin zafin zuciya yace “kowa yaje na gde” binsa sukayi da kallo ya dubi Hajiya Kulsum yace “Mama wlh idan akaci gaba da hayaniya a gdannan tsaf zan haukace brain dina tana neman daina aiki” sumsum suka rinqa ficewa daga gdan saida suka fice gabadaya ya tsaya yana jin tashin motocinsu gabansa faduwa yake daqyar ya tura qofar da sallama ya shiga dakin ya tsaya tsakiyarsa Yana qarenta kallo tana zaune ta dora kanta jikin gado sai tsumar jiki takeyi a sanyaye ya isa gareta ya tsugunna gabanta yakai hannunsa zai dago kanta gabansa ya fadi ya janye ya sake saita idanunsa akanta yace “meye yake damunki?” Kamar me jiran yayi mgn ta dago kumburarrun idanunta suka shiga cikin nasa ya kawar da kansa ya dake zuciyarsa yakai hannunsa jikinta yajishi zafi zau yaja numfashi ya miqe ya dauki wayarsa Yana zagaya dakin can yace “Inada petiant a gdana kazo da wuri don Allah” da haka ya kashe wayar yaci gaba da zagaya dakin can yaji ana qwanqwasa qofar ya sauka ya bude suka shigo tare Dr Razaq ya fara tambayarta yanayin da takeji tayi masa shiru shikam Kareem ido ya kafeta dashi can da tambayar ta isheta tace “Kaje Dr Razaq bakada maganin matsalata Allah ne kawai zaimin magani” wata iska Kareem ya furzar ya juya ya fice Dr Razaq ya biyosa yaganshi tsaye ya hade kai da garu ya dafashi yace “ka daina Sanya wannan damuwar a ranka Ranka shi dade kanada heart problem idan komai zaike damunka to rayuwarka tana cikin kwale²”
Juyowa yayi ya dubi Dr Razaq yace “kana nufin Meenah zata soni nima?” Dariya tambayar tabawa Razaq yace “kama qaddara a ranka tasoka fiye da kowa ta gama karfa ka manta kaine ta fara so a rayuwarta ko ka manta Karin mgnr hausawa da suke cewa so baya tsufa saidai masoyan su tsufa bature kuma yace true love never end” wani murmushi yayi yace “na gde Dr Razaq zan jira lkcn da zan gasqata hakan”………….

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan
[8/8, 9:07 PM] Oum Hairan: 0032 Sallama sukayi ya rakashi ya hau motarsa tare da karbar magunguna bai koma gdan ba shima ya shiga tasa motar Yana duba agogo 8:30pm ya jinjina kai ya fice a gdan kai tsaye wani restaurant ya nufa yayi musu siyayyar abinda zasuci ya juya ya koma gdan ya kulle ko Ina ya nufi saman Saida ya shiga dakinsa yayi wanka ya sanya kayan baccinsa ya fito ya bude nata dakin tana zaune inda ya barta har yanzu kukan takeyi gabadaya lamarinta ya tsinka masa lakar jiki da gaske take jin damuwar a cikin ruhinta.
Aje ledar dake hannunsa yayi ya tsugunna a gabanta ya kamo hannunta ta fuzge ya zauna sosai a gabanta ya dafe kuncinsa da hannayensa biyu ya zuba mata manyan idanunsa da a baya suke firgitata da sanyata shiga taitayinta baiji a ransa ko yace ta tashi suyi nafila zatayi ba shiyasa ya janyo ledar yace “Ya’isha tace tun shekaran jiya bakici abinci ba ko meye dalili?” Shiru tayi masa yaja fasali ya furzar da iska ya bude ledar ya fara yaga mata Naman yanda zataji dadin ci ya dauko yakai mata bakinta ta kawar dakai yayi murmushi yace.
“Lamarinki abun mamaki ne Meenah sai naga kamar kina jayayya da hukuncin ubangiji ne ya kamata ace rayuwarki kadai ta ishenki darasin da duk wani abu da Allah yayi zaki tarbeshi hannu biyu wlh duk da nakasance me qulafuci da addu’ar idan kedin Alkhairi ce gareni ki zama gatana ki zama mallakina bantaba furtawa wani burina a kanki ba na fawwalawa ubangiji na yarda duk abinda yayi daidai ne so Kuma sama taka cikin lkcn da ban tsammata ba kiran Mai Martaba ya shigomin yana fadamin na tanadi sadaki a hannuna daga dubu hamsin zuwa abinda Allah ya horemin nazo masallacin Fada yana nemana bansan meye zai faru ba hakanan na tafi Ina zuwa naga dogare sun budamin na shiga kamar yanda baa nemi izininki ba nima baa nemi nawa ba wlh kudin aljihuna kawai Mai Martaba ya karba dubu tamanin yabada umarnin a daura nidai na nemi guri na zauna Ina jiran naji auren waye zaa daura kawai naji ance yace shi a matsayin waliyinki ya bada aurenki gareni akan sadaki naira dubu tamanin bisa sharadin zanyi miki lefe kamar yanda al’ada ta tsara”

Shiru yayi yana mayar da numfashi sannan yaci gaba da cewa to meye laifina cikin lamarin nan Meenah?” A qufule ta dago tace “meyesa bakace bakaso ba?” Murmushi yayi yace “ko bake bace zan karba balle Kuma ya kasance dadaddiyar addu’ata ce ubangiji ya amsamin tare da tabbatarmin da ita kamar mafarki so ni a tsarina bana jayayya da duk abinda nasan ba ikona bane, Meenah a baya kema haka kike saboda kedin dalubata ce bansan meye ya sauyaki ba kinga inada maganganu da yawa da nakeso mu tattauna da zasu zame mana mafita Amma farko don girman Allah badon halin Abdulkareem kici abinci muyi sallah wlh ko Isha banyi ba saimu zauna”
Yanayin magiyar tasa tasata dole ta dauki Naman takai bakinta yaji dadin hakan sosai ya miqe ya shiga bathroom ya dauro alwala lkcn daya fito ta gama ya tattare ya fita da kayan ya dawo ya isheta a bayi tana brush da alwala, abin sallar ya shimfida yajasu sukayi Isha sukayi nafila raka’a biyu ya sanya hannunsa ya dafa kanta ta zame zata miqe ya miqe ya riqeta tare da matseta a jikin bango ya fara karanto addu’o’insa cikin larabcinsa me Sanyaya jiki sunkai 10 minutes a haka sannan ya saketa yana binta da kallo har zuwa lkcn bata daina dauke hawaye a idonta ba miqewa yayi ya dagata ya zare mata alqyabbar jikinta ya sake ware lafayar jikinta tana tureshi tana komai ta durqushe da sauri yayi dariya wai kunyarsa takeji Meenah da lkcn data fara period shine mutum na farko daya fara sani shima a lambu ya isheta tanata kuka wai taji ciwo daqyar ta fada masa yayi mata bayani.
Sautin dariyarsa ce tasata dagowa ya zauna tare da daganta gira yace “ashe kinajin kunyata Meenah yaushe kika farajin kunyana?” Harara ta galla masa yace “ko a jikina ki kwana kinayi yanzun dai Bari na barki ki kwanta ki huta abinki Saida safe” ficewa yayi yaja mata qofa tabisa da kallo tare da miqewa tayiwa dakin key ta haye gadon tayi kwanciyarta badon tayi bacci ba saidon tabawa zuciyarta damar tunanin abinda yake damunta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button