JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

THIS BOOK IS NOT FREE… REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566

Shares Please

Oum Hairan
[7/12, 9:44 PM] Oum Hairan: JUHUD

(OUM HAIRAN)

( Pure love sex nd romantic)

FP THREE

SUBSCRIBE
DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV

https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

TUNATARWA
Kowa yakanyi maka jaje a lkcn da wani abunqi ya same idan abin farin ciki ya sameka qalilanne sukeyi maka dariya har zuci, kada kasa dariyar mutane a ranka harta rudeka kaji cewa kowa sonka yake masoyin gaskiya shine wanda yake tare dakai a kowanne irin yanayi farin ciki ko akasinsa.????????

CIGABA
Inajin ciwon abinda Gwaggo Lami take fada akanki amma ban isa nayi magana ba abu daya na sani shine inayi miki addu’a ki kasance ya ta gari abar Alfaharin iyaye, kwanci tashi girma ya fara zuwar miki komanki abin mamaki ne gabbanki sunada saurin nuna girma hakan yasa tun kina qarama na sabar miki da saka hijjab irin na kanawa, sosai kike ganin tsangwama qyama cikin Yan’uwanki Hasiya Adama da Baraka Amma baki damuwa kodan kin taso kinganmu a cikin wannan qangin ne oho.
Wata rana Naje tallan Nono birni na dawo na tarar dake kina kuka na shige daki kika biyoni nake tambayarki meye yake faruwa sai kike fadamin Asubi ce ta bugeki saboda kunyi fada da Baraka tace miki kilakin birni kin bugeta hakanan na hqr bance komai ba ashe mgnr nan har gurin iyayenku maza taje da dare Baffanki yazo yake tuhuma ta wai waye yake zuwa yake siyan nono a gurina a sulluwa (mota) daga birni?”

Dagowa nayi na dubesa nace yaron Alh Idi ne da ka hadamu dashi a kasuwa yake zuwa karbar masa nono” numfashi Baffanki ya sauke ya kira sunana na amsa yace “shin Indo kinasa ido akan Aminatu kuwa?” Sake ware injin idona nayi akansa nace “Wai mekake tunanine Haro nikam bangane inda zantukanka suka dosa ba” sake gyara zamansa yayi ya dafe kansa yace “dazu na dawo daga kiwo na Ishe Ribado da Bangel suna tattaunawa naqarasa domin mu gaisa shine suke cemin wai dazun sunga wani me Sulluwa yazo ya dauki Aminatu a mota sunyi hanyar birni” dafe qirji nayi cikin kidima da gigita nace “aa Haro wlh zancene Juhud yau babu inda taje tallanma nice na fita saboda tacemin batajin dadi” jinjina kai yayi yace “shikenan adai qara kulawa” ashe wasan baa fara ba.

Tun daga wannan lkcn suka dora mamu qahon zuqa babu dama mutum yazo siyan nono gurinmu sai suce iskanci yazo ba keba nima a haka nake a gurinsu duk da cewa Baffanki baya bawa abin muhimmanci, tsaka da haka Hammanku Manga ya dawo daga neman kudi yaganki ya nuna yana sonki da murna baffanku yazo min da mgnr domin a lkcn duk anyiwa su baraka aure saura ke kadai kin rasa ko matayi a rugarmu dama maqota saboda sharrin maitar da suka liqa mana.
Duk da zuciyata bataso ba amma banja ba saboda bansan raayinki ba hakanan baffanki ya nemoki ya tambayeki game da Manga domin shi yace ma kun gama daidaitawa nan kikayi tsalle kikace bakiso naso na matsanki ki karbeshi amma sai baffanki yace tunda bakiso babu meyi miki dole ko bayan ransa hakanan naja bakina na tsuke babu kunya yaje yace da yan’uwansa kince bakison Manga nan suka qara sanya masa tsura ashe dama asali ba manga ne yace yanasonki ba sune suka kitsa masa ya aureki sai susan yanda zasuyi su hallaka babanki su kwashe dukiyarki,
Abu kamar wasa gaba me tsanani ta shiga tsakaninsu ko gaisawa basayi watarana da dare har mun kwanta Bangel yazo yayi sallama da Baffanki ya tashi ya fita bansan me suka tattauna ba nidai naga ya dawo yana huci na tambayesa yake cemin Aishatu don Allah ko bayan raina karki yarda ban aminta Aminatu ta auri Manga ba na haramta hakan idan har hakan ta faru bazanyi farin ciki ba” jikina yayi sanyi ya kwanta ranar kwana yayi yana juyi yana hawaye idan na tambayeshi sai yacemin shidai bai aminta Aminatu ta Auri Manga ba a lkcn inata fama da rashin lfy mukaje gun me magani yace cikine dani amma ya kwanta.

Ban wani damu ba duk da cewa Baffanki kullum cikin kawomin magani yake hakan baisa cikin nan ya tashi ba wata biyu tsakani sukayi wani gagarumin rikici daya sanya suka qara kullatar juna ashe a wannan dare sukayi taro suka yanke shawarar tunda yaqi basu hadin kai kawai su kasheshi su huta mana inyaso sai manga ya kada shanun yayi kudu dasu kinga zaace barayin shanh ne suka kasheshi.
Maddibo Buba ne yaji wannan shirin nasu a daren kuwa ya kira Haro ya sanar dashi abinda yan’uwansa suke shiryawa yaja fasali tare da murmushi yace “babu komai Allah yafi kowa sanin abindake qarqashin qasa dana ban qasa yafi kowa sanin daidai” daya dawo bai sanar dani ba nidai naga ya tashi cikin dare ya dauko wata qaramar adaka ya bude ya zaro wasu abubuwa masu walwali yabani yacemin Aishatu wannan abin da kike gani ba komai bane face dutsen Lu’ulu’u wanda yan birni suke cewa diamond wannan kuma gwal ne nasan kinsanshi don Allah ki nemi guri kiyi musu mugun boyo asalinsu na Mahaifiyata ne Aminatu naketa ajiyarsu domin Aminatu kada kibari wani yasan dasu a hannunki sunfi shanun can da kike gani garke guda daraja domin kuwa yanzu a duniyar mutanenmu wane da wane ma ba kowane yake iya mallakar diamond ba koda bayan raina zasu qwace komai ya kasance Aminatu ta tsira da wadannan abubuwan”

Na dade ina tunani kafin na tashi na haqa rami a qarqashin gadona na zubasu a ciki insha Allahu a yau zan baki abinki ki daura a qugunki su zame miki jigida iya wuya kada ki bari su kubce miki kinji” jinjina kai tayi Innatu taci gaba da cewa “washegari da safe na damawa Baffanki fura yasha ya kada shanu ya tafi kiwo nikuma na dauki nono na shiga gari acan suka cim masa da rana lkcn kin tafi kaimasa hura suka sareshi akansa da qirjinsa ya fadi jini nata malala kince kinga shanunsa lkcn da aka kadasu akayi hayi dasu amma bakiga wanda ya kada dinba kina binsu har kika ishe inda Gawar mahaifinki take yashe a qasa kece kika dawo kika fadawa Maddibo cewa an sari Baffanki kuka dunguma kuka koma nidai bayan na dawo na ishe wannan mugun labari shine tunda na yanke jiki na fadi bantashi ba nake zaune a wannan halin tsayin shekara biyu kwatsam sai cikina ya fara motsi nasa kika kiramin Jumme na sanar da ita dake tasan da batun kwanciyar cikin ta sanarwa da Maddibo Shi kadai yayi murna ya rinqa karbomin magani ashe a gefe Bangel da Rubado zargina sukeyi da Buba wai yana shigowa dakina ya dade hakanan sukaje suka kitsawa Jumme tazo har dakin nan tayimin tatas ina zaune babu halin magana a cewarsu ma wai wannan cikin na jikina ba na Haro bane na Buba ne Juhud Allah daya tsakanina da buba daga sannu sai idan ya kawomin magani ko nonon da zaki fita dashi talle.

A haka muke rayuwa har kawo yanzu da komai ya qara lalacewa Juhud kullum mutanen nan basu fadin alkhairi garemu kullum cikin yi mana kalen sharri suke yanzu haka kwanaki uku da suka wucce Jafaru makiyayi ya dawo daga kudu ya kawo shanaye guda dari da ashirin yace na Baffanki ne to tun jiya sukebin kaina akan na yarda a daura aurenki da Manga nikuma gashi Baffanki yabarmin wasicin ko bayan ransa bai aminta a hadaki aure da Manga ba a yau bayan kin fita diban ruwa har barazana sukayi min da rayuwata Juhud bandamu ba indai akan burin Haro ne su kashenin ma kansu sukayiwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button