JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Juhud is not free read… regular 300 VIP 600 via???????? 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241…

Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241…..

Oum Hairan
[8/2, 6:36 PM] Oum Hairan: 0026 Jinjina kai Juhud takeyi da jin wannan rikitaccen al’amari tabbas duniya ta cika da mutane marasa tsoron Allah saidai kayi fatan Allah ya dada maka Imani kawai, dubanta Mom tayi tace “Kumbo Hami itace ta riqeni tun bayan rasuwar mahaifiyata banida uwar data fita a duniya Meenah” sosai Meenah taji dadi da ganin dangin surukar tata hakanan taji tanayi musu wata qauna me game jini suma sosai suke nuna mata qauna da kulawa sun jima sosai a sashin nata sunata hirarsu gabadaya su anan suka qarashe bikinsu basajin Hausa sosai hatta Rasheed fullanci yakeyi musu wannan tasa Juhud sajewa dasu.
Kwana uku aka dauka ana bikin qofar falo Rasheed hana Juhud zuwa yayi da sunan biki to itama bata matsa ba ganin Mom ta goya masa baya a gdanta tayi nata bikin saidai tasa ta cire kawai idan yaga garara mutane sunwa bangaren sauqi yasata a corner yayita hadanta aiki ta rasa a wanne bigire zata aje Rasheed irin mazan nan ne masu jarabar nacin masifa shi indai zaki dagansa qafa to bakida matsala dashi idan har kaga Yana ciccin mazu to ya nema anyi masa rowa ne.
Tunda ta fahimci haka itakuma taci alwashin kozata wahala indai ya nemi haqqinsa zata bashi domin shima Babu ta inda ya tauyeta ya tsarenta mutumcinta fiye da yanda ma ya tsare nasa, ranar da biki ya watse aka kai amare gdajensu washegari su Kumbo Hami suka shirya tafiya Juhud har tafi Mom shiga damuwa da tafiyar tasu da anyi mata mgn sai hawaye lkcn da taga sun kusan gama shiryawa sulalewa tayi tabar gidan ta koma sashinta tasa Rasheed a gaba da kuka wai ita bataso su tafi.

Murmushi yayi ya shafa kanta yace “ke har yanzu yarinya ce Meenah to yanzu Kuma kawai saboda bakison su tafi sai su zauna? Kiyi hqr idan kika haihu zan dauki dogon hutu zan kaiki garinsu nima rabona da Mali nafi shekara ashirin” da haka ya samu ta sake har sun shiga mota Kumbo Hami ta fito ta kama hannunta hakanan takejin yarinyar a jininta tace “kici gaba da hqr mijinki Yana sonki Ni shaida ce Meenah idan Allah yasa watan hsihuwarki ya kama da rai da rayuwa zan dawo ni zanyi miki biqi kinji jikata” dariya tayi itama tayi dariya suka tafi suna dagawa juna hannu tana kwance bisa kafadar mijinta.
Taso rakasu airport fir yaqi saboda yasan idan taga tashinsu tsaf zata rikice masa, suna komawa kuwa ya fara hadansu kaya ta dubesa tace “yada hada kaya?” Dubanta yayi yaja numfashi yace “tafiya muma zamuyi” komawa tayi ta kwanta yaci gaba da aikinsa bayan ya gama yazo shima ya kwanta sukaci gaba da soyayyarsu sai biyar na yamma sannan sukabar gidan Muntaz ne yakaisu airport suka daga zuwa Enugu.
Sun sauka da dare suka samu motar taxi takaisu masauki suna zuwa ta kwanta zazzabi ya rufeta Saida ta kwana uku tana kwance yana jinyarta har ta samu ta samu sauqi sukaci gaba da rayuwarsu gwanin dadi.

Aikam tana ganin qauna da soyayya ririta cikin nan yakeyi kamar me, lkc ya rinqa turawa cikin nata Yana qara girma komai yanayi mata wuya shine yake yi mata komai kafin ya fita hatta abinci daya barta ta girka gara yaje ya siyo musu, October watan haihuwarta ya kama tsakiyarsa suka dungumo suka dawo Daura kwanansu uku kuwa da dawowa Kumbo Hami ta dira a Daura sunyi murna sosai sunata farin ciki kwanansu uku ya tafi ranar daya tafi kuwa cikin dare ciwon naqudar na gaske ya tashi.
Wayyoh anci wuya matuqa kwana tayi ta wuni tana naquda har Saida suka yanke shawarar ayi mata aiki sun gama komai sun shiga da ita ubangiji ya kawo mata sauqi cikin taimakon Allah ta sunkuto qaton danta namiji wayyoh farin ciki gurin Mom da Mai Martaba da Ya’isha hatta Muntaz yayi murna da wannan haihuwa kwananta daya a asibitin aka sallameta suka dawo gda Kumbo Hami na kulawa da ita shikam gogan saboda farin ciki har kuka yayi gashi bayada damar dawowa bama ya qasar Yana sauka aka turashi Africa ta kudu.

Ba Shiba ita kanta taso ace yana kusa yaga dansa yasa masa albarka hakanan dai akaci gaba da hidindumun haihuwar wani abin mamaki babu wani daga bangaren Addah Abulle daya leqo barkar wannan haihuwa lamarin ya bawa kowa mamaki itako Meenah batasa a ranta ba balle abin ya dameta domin ba iyakar su kadai bane duk Wanda ke gdan sarautar Babu Wanda ya leqo musu barka tasan saboda itane Kuma tariga tayi forget na komai dazai sanyata damuwa dane dai ta haifi abinta Kuma ubansa da shaqiqan danginsa suna murna da zuwansa duniya.
Duk wani gata da maijego yar gata take samu Meenah ta samu samansa Babu abinda zatacewa surukarta da Mai Martaba sai gdy domin shima ya taka rawar gani gaya a wannan haihuwa, duk abinda uba yakeyi shine ya dauki nauyi donma komai na buqata Rasheed ya tanadi abinsa sai dan abinda baa rasa ba Kuma ya zuba mata kudi masu kauri a account dinta ko zata buqaci wani abu.
Ranar kwanaki uku ne suna zaune da Mom da Ya’isha da Aunty Hamida a falo Juhud na feeding din babynta ya kafeta da ido qurr yana qare mata kallo suna dariya Kumbo Hami tana cewa “wannan ja’irin yaron quiya zaiyi tun yanzun Yana qarewa uwarshi kallo da shegen wayonsa aka haifesa” itadai saidai tayi dariya kawai.
Sallama akayi a bakin qofar suka daga kai suka kalli me shigowar Hajiya Bilki ce ta shigo ita da Dada Hanne babbar yayarsu Mai Martaba Mom ta taresu fuska a washe tana musu sannu da zuwa ta basu gurin zama Dada Hanne ta tabe baki tace “ashe an haihu?” Da yanayin rashin jin dadin tambayar Mom tace “eh wlh yau kwana uku” tabe baki sukayi Dada Hanne tace “eh tun ranar aka fadamin shine dai yau na daure nace Bari nazo Ke Bilki bani ruwan qanzon nan” dukkansu kallonta sukayi ta miqa hannu ta dauki yaron a cinyar Juhud tana harararta kawai ta bude bakin yaron ta dauki ruwan zata dura masa Meenah ta miqe da sauri tayi kukan kura ta warce danta Dada Hanne ta kuwa dauketa da mari tace “kutmar ubancen ke dan uwarki ni zaki qwacewa yaro a hannu koda yake ba banza ba dama anfada ance indai da abar a jikinki bazaki Bari a karyawa danki ba gashi kuwa munga alama to wlh baki Isa ki bata Mana zuri’a ba dolene abawa yaron nan ruwan qanzon nan Kuma daga yau an daina bashi wannan baqin nonon na tsiya a nema masa Madara ko abawa Fadila ta shayar dashi shidai Rasheedun da kwadayin farar fata da kyauwun banza yakaishi ya dauko to ta qare masa akansa….”

Tana qoqarin fusgar jaririn Juhud ta qara qanqame abinta ta saki wani kuka me sauti tace “wlh bazaku kashemin daba duk abinda zakuyi saidai kuyi…..” Mom ce ta karbe da cewa “Dada Ina ganin mutumcinki ki fita daga lamarin halwata kafin na hada dake na tsince muku zarafi yaran nan daga ita har mijinta basu damu da lamarin kowa ba ku kun damu dasu to waima Ina ruwanku da abinda ta Haifa ne ince dai nasu ne su suka Samar da abinsu ke yanzu bakiji kunya ba gotai gotai dake kizo kina yada girma gaban jikarki”
Hayayyaqo mata Dada Hanne tayi tana cewa eh dama Mana dole kice haka Aisha ai kinci kin qoshi mun kaiki matsayin da baki takaba a baya to dake da Mahfuz da Rasheedu da duk wani Wanda yake yaruwa a gidannan a qarqashin darajata yake balle wannan yar galaulawar da kuka kwaso kuka manna Mana saboda haka wlh muddin Ina raye Kuma Rasheedu daga tsatson sarki Waziri ya fito to dole ne a bani dannan mu karya masa maita takanas nayi tattaki har Kankia na karbo wannan maganin don tseratar da ahllinmu daga gurbacewa irin maita ai bala’i ne bazamu sake a lalata Mana halwa da son zuciya ba” Hajiya Bilki ce ta cafe da cewa “yo Dada Hanne da kike wannan mgnr jinki zasuyi ne ko zaa barsu su gane me kike nufi da gatan da kikeson yi musu ne ai anriga an lashe kurwas basuda katabus hatta Mai Martaban bashi da fuss indai akan wannan tsintacciyar magen ala qaqai dince kina gani fah saboda a samu a ceto yaron nan nabawa Alh Aminu shawarar yafadawa Mai Martaba tunda yaqi Hidaya ga Dijenan babu makusa in batafi ba bazaa fita ba ya aurawa Rasheed Amma yaron nan ya debemin albarka ta sama data qasa har Yana cewa indai halwata ce to har abada bayaso……”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button