JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL

JUHUD COMPLETE HAUSA NOVEL BY OUM HAIRAN

Jinjina kai yayi ya bude littafin ya fara dubawa ya dubeta yace “ni ba turanci na karanta ba Amma zanyi bakin qoqarina wajen ganar dake abinda Allah yasa na fahimta ki tsara lkcnki da safe zanke miki darasin addini da dare Kuma na boko hakan yayi miki?” Rufe fuskarta tayi tana dariyar jin dadi tace “wlh yayi Ya Kareem na gde Allah yabarmana kai” murmushi yayi yace “dole saiya kasheni tashi muje ki nunamin assignment dinku na qarshe da Muntaz nagani saina samu gabar dora miki”

Miqewa tayi tayi tsalle ta rungume Addah Abulle tace “idan na zama gwamna Ya Kareem zan fara kaiws makka” dariya sukayi Momy tace “baki rabo da shirme me sunan yaya to Ina kika baro Baffa’am din naki ni kwana biyu ma banjinsa ko yanayin aikin ne?” Cokalo baki tayi tace “bayan ya daina sona ko waya ya Kira baya cewa abani” murmushi Mom tayi tace “ai kedin ce da hayyata kimbi kin damesa yaushe zai dawo naji yace saura wata biyu ya samu hutu ya dawo gida” tsallen murna ta kamayi tace “na kusa na kwanta a jikin Baffa’am dina me dadi Allah duk duniya banga Wanda yafi Baffa’am dina iya rarrashina ba sai Ya Kareem da yake kwatantawa……”
Fuzgarta yayi yace “kin cika surutun banza Amina to shidin muharraminki ne da zakike kwanciya a jikinsa dan wauta idan kinyi a baya yanzu shima yasan kin wucce wannan shirmen dubeki fah mace daya da rabi haba wannan ai shirme ne” murguda masa baki tayi tace “eh dai dan baqin…..” Bugu yakai mata suka zuba a guje yana cewa sai kin fadamin waye dan baqin ciki yarinya itakuma tanayi masa gwalo da haka har bangaren Mai Martaba tana shiga ta shige bayan Mai Martaba tana dariya shima dariyar yayi ya janyota ta lafe a jikinsa yace “ya akayi ne Aminatu sarkin wasa kekam kamar ba yar soja ba” tana haki tace “ba Ya Kareem ne yakemin baqin cikin hawa cinyar Baffa’am dina ba don Mom tace saura wata biyu ya dawo” murmushi Mai Martaba yayi yace “aifa kaima ka taro March inakai Ina shiga tsakanin ya da ubanta wannan ai sai Allah” gwalo ta qarayi masa yace “to kagani fah Mai Martaba gwalo takemin” daquwa ya watsa mata yace “tayi din kaine babban kwabo ai” zama yayi shima suka fara karatun anan inda batayi daidai ba ya ranqwasheta kafin su gama duk ya tara mata gajiya ta narke tace ita bacci takeji dakansa ya rakata har qofar falon Muntaz na tsaye a harabar gdan fuska duk tayi dameji yayi qwafa ya shige dakinsa shikuma ya qarasa rakata ta shiga dakin nasu sukayi sallama.

Goma da rabi Amma babu kowa a dakin daga Amrah har Ya’isha kayanta ta cire ta daura towel ta fada wanka tayi wankanta cikin nutsuwa ta bude qofar zata fito taga duhu dakin tace “subhanallah An dauke wuta Bari na jira a kunna inj…..” Mgnr qin qarasa fitowa tayi qirjinta ya doka da qarfi jin motsi a dakin cikin rawar murya tace “Am…rah…. Ya’isha yaushe kuka daw…..” Nan ma kasa qarasawa tayi jin an rungumeta ta baya a razane tace “please Amrah nace miki banson wannan wasan ki daina Allah zan fadaki……” Wutar jikinta ce ta dauke jin an Sanya hannu an janye mata towel din jikinta an dora hannu saman qirjinta ta bude baki tasa ihu nandanan taji an saketa daidai lkcn da su Ya’isha suka banko qofar da sauri Amrah a lkcn ne Kuma wutar ta dawo tayi tsaye sangalgal babu komi a jikinta sai rawar baki data jiki takeyi da sauri Ya’isha ta matsa ta dauki hijjab ta zura mata suka dubeta sukace “yadai Baby meye ya faru?” Sai lkcn kuzarinta ya dawo ta fara dube² a dakin cikin firgici suma dube²n suka fara suna tayata ta fara bankada labule itane har qarqashin gado Amma bataga kowa ba suka dubi juna Ya’isha tace “wai meye kike nema?”

A wahalce tace “mutum” kallon juna sukayi sukace “mutum Kuma?” Jinjina kai tayi sai lkcn taji hawaye ya qwace mata tace “wanka na fito kawai naga wuta ta dauke Ina tunanin kune naji an rungumeni ta baya kafin na gama saita natsuwata aka yagemin towel shine inayin ihu naji kamar an fita da gudu Kuma sai gaku kun shigo don Allah ko kune kuka tsorata Ni?”
Numfashi suka sauke a tare Amrah tace “wlh bamu bane muma da muka shigo ihunki ne yasamu takowa da gudu wannan gdan wani banzan gdane kowa Yana bangarensa sai a saceka ma baa sani ba”
Zama tayi cikin mugun tashin hankali suma suka zauna Amrah na binta da kallo tace “kece da shekiyar gardamarki da kin bimu Aida bakiyi gamo ba Kuma ko banza kyaga gari” numfashi ta sauke tace “to waiko inada Aljanu ne?” Dariya abin yabasu Ya’isha tace “to waye ya sani ni Amrah fito Mana da qwalam dinmu mu dan lasa Amma wlh yau Shafiq ya wahalar dani shege inaga magani yaje yasha ya gaji da miyar da nakeyi masa baya qosar dani” Amrah ce ta cafe da cewa “ke yau ni kinsan sabon kamu nayi wani alhajin birni infada miki quarter million yasamin a account yace next week zai dawo” tafawa sukayi itadai tana zaune tana kallonsu suka dauko ledojin da suka shigo dasu suka baje Ya’isha tace “sauko kici rabonki” girgiza kai tayi suka miqe sukace “aikuwa baki isaba yarinya dole kici” danna mata tsiren sukayi a baki ta lumshe idonta tana taunawa suka sata a gaba suna dariya saukowa tayi tasa hannu sukaci sukayi hani’an.

Bayan sun nutsa ne Ya’isha tace “nayiwa Saleem alqawarin gobe zan taho dake yace dubu dari zaibani tukuici idan Kuma kin amince yazo gda” dagowa tayi tace “aa nidai kar yazo banason zuwansa wancan zuwan da yayi Ya Kareem kamar zai cinyeni saboda masifa har cewa yayi zai fadawa Baffa’am”
Tsaki sukaja a tare Amrah tace “ke muguwar bahuwa ce waike meye yasa bazaki waye ba koda yake dama ance sai mutum ya shekara arba’in yake wayewa badon hakaba kawai kita nuqu² da kayan dadi a jikinki saidai ki wanke kisa masa pant yayi gashi ki aske babu me mora” watsa mata harara tayi tace “ai cikar mutuncina kenan” wata dariya suka kwashe da ita sukace “sakarya ita ajiya yanzu haka mijin da kike adanawa ma yana kwance da wata zaa daura masa aure dake Kinga ta banza kikayi, tabe baki tayi tace “eh shida ubangijinsa nidai nafiso na hadu da nawa salin alin murmushi sukayi sukace ai saikitayi aikine be isheki ba duk gindin da baayi masa susa ya zama sorry rayuwar ga ta hutawa daga duniya sai Habuja aljanna tamai rabo”

Da wannan tasa rigar baccinta ta juyansu baya tayi kwanciyarta tanajin kowacce na waya da saurayinta itakam ko a jikinta washegari da wuri ta tashi tayi wanka tayi sallah ta fito ilai kuwa ta iske malamin nata a falo yana duba wani littafin addini ta isa gabansa ta zauna suka gaisa cikin larabci kamar yanda ya sabar mata ya zuba idanunsa akanta yanajin saqon daya dade yanayi masa yawo a zucci na tasowa hadda take kawo masa shikuma hankalinsa nakanta Saida ta gama ta dago taga yanda ya kafeta da ido taja numfashi tare dakai hannunta idonsa ya qifta da sakin wata babbar ajiyar zuciya ya fara Bismillah sannan ya fara yimata qari bayan ya gama biya mata suka koma Hadith suka sake gangarawa tajweed haka ya rinqa karbar haddarta mataki mataki yana sake ware injin idonsa akanta gabadaya yau kallon da yakeyi mata yasa ta kasa sakewa dashi suna gamawa ta miqe ya riqo hannunta yace “na takura miki ko?”
Qasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta yaja numfashi ya qara rage sautin muryarsa yace “wasu fararen kyawawan furanni ne suke sauka saman shararriyar hanyar da babu komai a samanta sai wasu korayen bishiyu da suka kewayeta gefenta Kuma ruwa ne yake kwaranya ta saman wani farin dutse a gefen dutsen wata yar bukka ce irin taku ta fulanin asali tsuntsaye nata shawagi dangin su Kanari Dawisu Jimina Alhuda’huda dadai sauransu”
Gabadaya ya dauke mata hankali da lbrn nasa jin yayi shiru ne yasata dagowa ilai kuwa idanunta ya fada cikin nasa kwarjini yayi mata irin zaman da yayi saman kilishin dole ne ka kiyayeshi yayi murmushi yace “ina tafe cikin nutsuwa Amma zuciyata matse take data isa inda wannan bukkar take wacce ta gefenta ruwa yake gudana take, Ina isa naja na tsaya saboda wata busar sarewa me kashe jijiyoyin jiki dake tashi ta cikin wannan bukka tare da wata zazzaqar murya tana rera waqe cikin harshen fullanci” sake tsagaitawa yayi ya hadiyi yawu can yaci gaba da cewa “bansan wace a ciki ba Amma zuciyata ta kwadaitu dason ganin mamallakiyar wannan murya me saukar da kasala Kuma me irin suffar matan aljanna, Aminah ba fadamin akayi ba a Raina naji koma wacece zata kasance haskenta kamar na hurul’ayn, Ina shiga kinsan wa idona ya ganemin?” Girgiza kai tayi cikin matsuwa dajin qarshen labarin ya daga hannunsa ya nunata da yatsa yace “kece Aminatuh….” Zaro ido tayi ta dafe qirji tace “ni Kuma Ya Kareem?” Matsowa yayi numfashinsu na gwamuwa yace “na’am Juhud kene na gani a dakin Kuma aka mallakamin ke matsayin matata ta sunnah tunda nake bantaba mafarkin da naji dama ban farka ba kamar wannan naso naga irin rayuwar da zamuyi da rayuwata a wannan kyakkyawan muhalli Aminatuh Wlh tallahi billahil lazi la’ilaha illahuwa Inasonki sonda bantaba yiwa kaina ba soyayya ta aure”……………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button